Mutum daya ne ke jagorantar gungu biyu na masu aikata laifin. Hoto/ActuNiger

Rundunar ‘yan sandan Jamhuriyyar Nijar ta yi nasarar kama gungun masu aikata laifi har biyu a gundumar Sautou da ke Jihar Yamai.

Rundunar ‘yan sandan reshen Koubia ta bayyana cewa mutum tara ne suka shiga hannunta daga cikin gungu biyu na wadanda ake zargin masu aikata laifi ne tare da wata mace daya.

Jaridar ActuNiger ta ruwaito cewa rundunar ta kai samame wani kango bayan ta samu bayanai kan cewa akwai wasu masu aikata laifuka da ke zaune a wurin.

Haka kuma a cikin rukuni na farko da aka cafe, bincike ya nuna cewa kusan duka mutanen da aka kama an taba yanke musu hukunci kan laifuka da suka shafi ko dai sata ko kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi.

‘Yan sandan sun kuma tabbatar da cewa jagoran gungun ya amsa laifin cewa suna kwacen waya da kuma afkawa gidajen jama’a a cikin dare domin sata.

Kamar yadda ya bayyana, mutum shida a cikin gungun barayi ne, daya kuma wanda ake kiransa da Tupac ya shahara wurin dillancin miyagun kwayoyi.

Ita kuma macen da aka kama, budurwar daya daga cikinsu ce wadda ake amfani da ita a matsayin tarko domin jawo hankalin maza.

‘Yan sandan kuma sun bayyana cewa wannan gungun na kai hare-hare a yankunan da suka hada da Koubia da Sonuci da Banikoubay da Centre aere.

Wadanda ake zargin sun kuma bayyana cewa idan sun yi sata suna sayar da kayayyakin da suka hada da wayoyi a farashi mara daraja ga wani mai sana’ar walda a gundumar Bani koubeye wanda ake wa lakabi da “the Boss” wanda shi ne oga a gare su.

Gungu na biyu na masu laifin kuwa ya kunshi mutum uku.

Shi wannan gungun na biyun ya shahara ne wurin fashi da makami a wurin taro ta hanyar amfani da wuka kuma shi ma gungun ‘’the Boss’’ shi ne ke jagorantar shi.

Sukan yi zagaye ne da dare a birnin Yamai kan babur inda suke amfani da wuka domin kwace baburan mutane.

Bayan sun kwace sukan kai babur din zuwa wurin daya daga cikinsu domin yi masa kwaskwarima kafin su sayar da shi.

‘Yan sandan sun bayyana cewa sun gudanar da bincike matuka bayan kamen gungun kuma sun gano abubuwa a tattare da su da suka hada da babur kirar Kasea da wuka da hular kwano ta sojoji uku da belt da tabar wiwi da kuma wayoyi.

Rundunar ta kuma tabbatar da cewa mutum daya ne ke jagorantar gungun masu laifin biyu wadanda ke aikata laifuka a wurare daban-daban.

TRT Afrika da abokan hulda