Na bai wa lauyoyina umarni su daukaka kara kan hukuncin kotu: Abba Kabir Yusuf

Na bai wa lauyoyina umarni su daukaka kara kan hukuncin kotu: Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce hukuncin kotun cike yake da kura-kurai da rashin adalci.
Gwamna Abba ya bukaci al'ummar Kano kada su karaya domin kuwa shi ne ya ci zabe da kuri'a  1,019,602./Hoto: Abba Kabir Yusuf/Facebook

Gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Nijeriya Abba Kabir Yusuf ya ce ya bai wa lauyoyinsa umarni su daukaka bayan bayan kotu ta ce ba shi ne halastaccen gwamnan jihar ba.

Gwamna Abba Gida-Gida, kamar yadda ake yi masa lakabi, ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa 'yan jihar ta Kano ranar Laraba da daddare.

Ya yi jawabin ne bayan kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben jihar na 2023.

"Akwai kura-kura da rashin sanya doka a gurbinta kamar yadda tawagar lauyoyinmu ta bayyana. Shi ya sa kundin tsarin mulkinmu ya ba mu damar bin matakai daban-daban kamar zuwa Kotun Daukaka Kara da Kotun Koli," in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ya kara da cewa: "Don haka a wannan gaɓa, tuni mun umarci tawagar lauyoyinmu ta daukaka kara game da wannan hukunci nan ba da jimawa ba domin tabbatar da adalci."

Gwamna Abba ya bukaci al'ummar Kano kada su karaya domin kuwa ya tabbatar shi ne ya ci zaben gwamnan jihar da aka gudanar a watan Maris na 2023 da kuri'a 1,019,602, inda ya bai wa dan takarar APC tazarar kuri'a 128,897.

"Muna so mu tabbatar muku cewa wannan hukunci ba zai sa mu karaya ba, kuma ba zai kashe mana gwiwa ba, domin kuwa wani koma-baya ne ga jiharmu da ba zai dore ba wanda za mu shawo kansa da yarda Allah (SWT)," in ji Gwamna Abba Kabir Yusuf.

TRT Afrika