Hadiza Gabon

Daga Halima Umar Saleh

Fitacciyar ƴar fim ɗin Hausa ta Kannywood a Nijeriya Hadiza Aliyu Gabon ta ce ta shigar da ƙarar mutumin da “ya ɓata mata suna” ne domin hakan ya zama izina da darasi ga ƴan baya.

Gabon, wacce ta shigar da ƙarar a wata Kotun Majistare da ke Kaduna a ranar Laraba, ta shaida wa TRT Afrika cewa rikicin da aka shafe fiye da shekara ɗaya da rabi ana yi tsakaninta da mutumin da take ƙarar ta jawo mata naƙasu sosai a harkokin rayuwarta, saboda “ɓata min sunan da ya yi tun da farko.”

Hadiza Gabon ta shigar da wannan ƙara ce bayan da kotun da mutumin ya fara kai ƙararta ta wanke ta daga zargin zamba.

Za a fara sauraron sabuwar ƙarar a ranar 15 ga watan Nuwamban 2023 a kotun, da ke kan Titin Daura a cikin birnin Kaduna.

Me ya faru tun farko?

A watan Maris ɗin 2022 ne wani mutum mai suna Bala Musa daga Jihar Zamfara ya shigar da ƙarar Gabon a kotu, bisa zarginta da karɓar kudinsa har 396,000 da nufin za ta aure shi, amma bai samu cikar buri ba.

Bala ya ce sun yi musayar saƙonnin ne da Gabon ta shafukan sada zumunta, inda har ya gabatar wa Kotun Shari’ar Musuluncin da ya shigar da ƙarar shaidar rasitin banki na kuɗin da ya aika ɗin.

Ban san abin da ya shiga kansa ba da har zai dinga tunanin ni ce wacce ta aika masa saƙon cewa ya ban N,396,000 da alkawarin zan aure shi.

Hadiza Gabon, Tauraruwa a Kannywood

Sai dai Hadiza Gabon ta musanta zargin inda ta ce ba ta taɓa sani ko ganin Bala ba a rayuwarta.

“Daga labarin har sammacin kotun a shafukan sada zumunta na tsince su, abin ya ba ni mamaki matuƙa saboda bi ban ma taɓa sanin mai irin sunansa ba balle na yi wata hulɗa shi.

“Ta yaya ma za a ce na tallata wa wani kaina da nufin ya ba ni kuɗi don ya aure ni?” kamar yadda Gabon ta gaya wa TRT Afrika a wata hira ta wayar tarho.

Bala ya nemi kotu ta sa Hadiza ta biya shi naira miliyan ɗaya “na ƙin aurensa”, da kuma N396,000 ɗinsa na farko.

Sai dai bayan lokacin da aka ɗauka ana shari’ar, daga baya an gano mutanen da kuɗin da Bala ya tura suka shiga hannunsu, waɗanda sun san shi sosai.

Sun amsa laifin cewa sun yi sojan-gona da sunan Hadiza Gabon ne don karbar kudi a hannun Bala, tare da neman kotu ta yafe musu.

Abin da ya biyo baya

Bayan tabbatar da cewa Hadiza Gabon ba ta da hannu a cikin zargin da Bala ya yi mata ne, sai kotun a ranar 31 ga watan Oktoban da ya wuce ta wanke ta daga zargin.

“Kotu ta umarce shi ya biya ni diyyar Naira 300,000 na ɓata min suna shi kuma lauyansa ya biya N200,000 na ɓata min lokaci, amma har yau ba su biya ba,” in ji Gabon.

Gabon ta ce wannan lamari ya yi matuƙar ɓata mata rai da janyo mata ɓacin suna a idon al’umma saboda mutane da yawa sun yarda da zargin mutumin.

“Wannan batun baya ga ɓacin suna da ya jawo min ya kuma sa na yi asarar wasu ayyuka na miliyoyin naira, saboda kamfanonin da za su ba ni kwangila sun fasa don ganin akwai shari’ar da muke yi a kotu,” ta gaya wa TRT Afrika Hausa cikin yanayi na takaici.

Dalilin shigar da shi ƙara

Hadiza ta ce abin da ya fi ɓata mata rai shi ne yadda Bala Musa ya dinga yin hira da ƴan jarida yana sake ɓata mata suna cewa ta ci kuɗinsa ta ƙi ta aure shi.

“Ban san abin da ya shiga kansa ba da har zai dinga tunanin ni ce wacce ta aika masa saƙon cewa ya ba ni N,396,000 da alkawarin zan aure shi.

“Shi ya sa na ga gara na shigar da ƙara kan wannan cin mutunci da ɓata suna da ya yi min don ya zama izina da darasi ga ƴan baya.”

Ta jaddada cewa ba za ta janye ƙarar ba har sai ta samu adalci daga kotu kan wannan abu da Bala ya yi mata.

Zambar intanet ta zama ruwan dare

Irin wannan lamari da ya samu Bala Musa abu ne da ya zama ruwan dare ba a Nijeriya ba har a duniya baki ɗaya, inda wasu ɓata-gari ke amfani da sunan fitattun mutane suna damfarar jama’a.

A wasu lokutan kuma har mutanen da ba su shahara ba ma kan fuskanci damfarar ta shafin Whatsapp ko sauran shafukan sada zumunta.

Ba ɗaiɗaikun mutane kawai ake yi wa irin wannan zamba ba, a wasu lokutan har manyan kamfanoni da hukumomin gwamnati ma ba su tsira ba.

A misali duk shekara a Nijeriya bankunan ‘yan kasuwa na tafka asarar dala miliyan 30 a sakamakon laifukan intanet.

TRT Afrika