Sama da mutum 2,000 ne suka mutu sakamakon zaftarewar ƙasa a Papua New Guinea  Hoto: AFP

Ƙasar Papua New Guinea ta sanar da Majalisar Ɗinkin Duniya MDD a ranar Litinin cewa sama da mutane 2,000 ne suka mutu sakamokon zaftarewar ƙasa ɗaya rutsa da su, a cewar wata wasiƙa da kamfanin dillacin labarai na AFP ya samo.

"Zaftarwar ƙasar ta binne fiye da mutane 2,000 da ransu tare da tafka mummunar ɓarna," kamar yadda cibiyar taƙaita aukuwar bala'o'i ta ƙasar ta shaida wa ofishin MDD da ke Port Moresby babban birnin ƙasar.

Iftila'in ya shafe wani ƙauye da ke cike da mutane a gefen tsaunin lardin Enga bayan da wani babban dutse na Mungalo ya tarwatse da safiyar ranar Juma'a, inda ya binne gidaje da dama da kuma mutanen da ke kwana a ciki.

Sama da gidaje 150 ne iftila'in zaftarewa ƙasar ta binne a ƙauyen Yambali kaɗai, a cewar wani jami’in hukumar 'yan gudan hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya a ƙasar Papua New Guinea.

Kazalika lamarin ya haifar da gagarumar asara inda ''gine-gine suka rushe yayin da gonaki suka shafe, sannan tasirin hakan zai matuƙar shafar tattalin arzikin ƙasar,'' in ji jami'in hukumar.

Girman iftila'in na buƙatar "haɗin gwiwa da ayyukan gaggawa daga dukkan masu ruwa da tsaki", in ji jami'in. / Hoto: AFP 

''Babbar hanyar zuwa wurin hako ma'adinai na ''Porgera Mine a rufe take baki ɗaya,'' a cewar wasiƙar wadda ta isa hannu jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya a safiyar ranar Litinin.

''Har yanzu babu tabbas a yanayin tsaro wajen, domin ƙasar na ci gaba da zaftarewa ƙaɗan-ƙadan, lamarin da ke haifar da haɗari ga ana ci gaba da da ake ciki Yanayin da ke barazana ga ƙungiyoyin ceto da sauran mutanen da suka tsira.''

Girman iftila'in na buƙatar "haɗin gwiwa da ayyukan gaggawa daga dukkan masu ruwa da tsaki", in ji jami'in.

Wasiƙar ta yi kira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta sanar da abokan hulɗar Papua New Guinea ta fannin samar da ci gaba "da sauran ƙasashen duniya" halin da ake ciki na baya-bayan nan.

Akwai buƙatar a samar da haɗin-kai ta cibiyar takaita aukuwar bala'o'i, in ji wasikar.

AFP