Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat. / Hoto: Reuters

Turkiyya a ranar Asabar ta taya Kungiyar Tarayyar Afirka murnar cika shekaru 61. Ranar Afirka, rana ce wadda ake murnar zagayowarta a kowace 25 ga Mayu, domin tunawa da ranar da ƙasashen Afirka suka haɗu domin haɗa ƙungiyar haɗin kan Afirka ta OAU a ranar 25 ga watan Mayun 1963.

"Muna matukar taya dukkan abokanmu na Afirka murnar zagayowar ranar Afirka ta 25 ga Mayu, wadda ke bikin cika shekaru 61 da kafuwar Tarayyar Afirka, wanda hakan ke nuni da manufar dunkulewar nahiyar Afirka da kuma burin zama tare cikin hakuri," kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana a wata sanarwa.

“Dangantakarmu da nahiyar Afirka mai matukar muhimmanci da kuma al'ummominta ana gudanar da ita ne a cikin cikakken tsari kuma a hukumance, bisa ka'idojin mutunta juna da daidaito," kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

“Babban makasudin hadin gwiwarmu da kasashen Afirka shi ne tabbatar da zaman lafiya, da kwanciyar hankali da ci gaba a duk fadin Afirka.”

Ankara za ta bayar da goyon baya ga ƙasashen Afirka “domin a ji muryarsu da ƙarfi a duniya,” in ji sanarwar.

Ma'aikatar ta ce, a wani bangare na manufar Ankara game da Afirka, za a gudanar da taron bitar ministocin Turkiyya da Afirka karo na uku a cikin wannan kaka.

TRT Afrika