Shugaban 'yan adawar Sanagal Ousmane Sonko na gaiswa da magoya baya tare da dan takarar shugaban kasar da yake goyawa baya a zaben 24 ga Maris Bassirou Diomaye Faye a wajen gangamin zabe na farko kwana guda bayan sakin su daga kurkuku a Dakar, Senegal March 15, 2024. / Hoto: Reuters

'Yan kasar Senegal sun shirya fita jefa kuri'a a ranar Lahadi, a yayin da ake cikin halin rashin tabbas din siyasa bayan dage zaben na watan Fabrairu.

Bayan dage zaben, Shugaba Macky Sall ya sanar da sabon lokacin gudanar da zabe- a ranar da Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta sanar da cewa matukar aka wuce ranar 2 ga Afrilu ba a gudanar da zabe ba to an saba wa kundin tsarin mulki a wannan rana ce wa'adin shugaba mai ci zai zo karshe.

Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ta bayyana bukatar a gudanar da zabe cikin gaggawa, inda ta saba matakin da kwamitin nsulhun kasa ya dauka na mayar da zaben suw a watan Yuni.

Akwai 'yan takara 17 da suke nman zaman shugaban kasa

A watan da ya gabata, Sall, wanda yake kan mulki sama da shakara goma, ya ce zai sauka daga kan kan mulki a ranar 2 ga Afrilu da wa'adinsa ya zo karshe.

A ranar 3 ga Fabrairu, Sall ya sanar da dakatar da zaben da aka shirya yi a ranar 25 ga Fabrairu.

Jagoran Sanagal tun 2012, Sall ya kalubalanci jerin sunayen 'yan takara kuma ya zargi alkalan kundin tsarin mulki da aikata cin hanci da rashawa.

Duk da kasancewar Senegal daya daga kasashen Afirka da ba su fuskanci juyin mulkin soji ba tun bayan samun 'yancin kai a 1960, amma yanayin dambarwar siyasar da aka shiga a kasar ya yi ajalin mutane uku.

Bayan an kafa majalisar dokokin Senegal, ta samar da dokar da ta ce a dinga gudanar da zabe har zuwa 15 ga Disamba, inda kuma jami'an tsaro suka je suka fitar da wasu 'yan majalisar adawa.

Mai goyon bayan shugaban 'yan adawar Sanagal Ousmane Sonko da dan takarar shugaban kasar bassirou Diomaye Faye, wadanda aka saki daga fursuna, na duke da tutatr Sanagal bayan taron manema labarai da suka yi a Dakar.

Sai dai kuma, Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ta bayyana cewa dage zaben da aka yi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar.

Takarar mata

Anta Babacar Ngom ce mace ta farko da ta cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a Sanagal, inda take kamfe da sunan kawo cigaba da daidaita mata da maza.

Diyar shugaban asusun Sedima ce, gidan da ke da karfin siyasa a yankin Yammaci da Tsakiyar Senegal.

Kafin ta fada siyasa, ita ce daraktan zartarwa na kamfanin kiwon kaji.

Tare da kwarewar da take da ita a bangare mai zaman kansa, tana gwagwarmayar kasuwanci ya zama gada tsakanin gwamnati da jama'a

Daga alkawururrukan da ta yi, Ngom na son kafa bankin mata na kasa don tallafawa tattalin arzikin mata don su digara da kai, tare da kalubalantar abubuwan da ke hana mata bunkasa da ma shiga siyasa har su zama shugaban kasa.

Tana kuma fatan ciyar da kasar gaba ta hanyar kafa masana'antu, kasar da ke da mutane miliyan 17.

An fitar da sunayen mata shida daga cikin 93 da suke saka rai d atsayawa takara, kuma 20 ne kawai suka kai ga matakin fitar da sunaye na karshe, wanda Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta amince da sunaye biyu kawai - Ngom da Rose Wardin. Rahotanni sun ce batutuwa game da zama Wardin 'yar kasar faransa na nufin Ngom ce kadai 'yar takarar shugaban kasa

Senegal March 15, 2024Magoya baya na murna bayan sakin Sonko da Diamaye faye daga gidan kurkuku a Sanagal.

TRT Afirka ta bayyana Ngom a matsayin mace jajirtacciya mai yakin neman zabe, a lokacin da Shugaba Sall ya yi rashin nasarar dage lokacin zaben.

Wannan ya janyi hatsaniya inda 'yan sanda suke kame mutane nan a watan Fabrairu masu zanga-zangar suka ce zai kara musu kwarin gwiwa a gangami da take yi.

A watan Agustan 2023, matar mai shekaru 39 ta kafa jam'iyyar siyasa mai suna 'Next geration for Citizens" (ARC).

Dan takarar jam'iyya mai mulko

Amadou Ba. Tsohon Firaminista Amadou Ba ne dan takarar jam'iyya mai mulki.`

Tsohon mai karbar haraji ya rike mukamin Firaminista tun 2022, kuma ya taba rike mukamin ministan harkokin waje da na kudi a Sanagal.

A watan da ya gabata, ya yi ritaya don mayar da hankali ga gangamin zabe, mai shekara 63 na iya zama dan takarar da aka fi so, kuma zai iya yin nasara, duk da yana fuskantar hamayya sosai.

Ba ya yi bayani game da wasu muhimman batutuwa: gudun hijira ba bisa ka'ida ba da ayyukan yi ga matasa.

Masu nazari sun bayyana shi a matsayin dan takarar gwamnati kuma mai kwarjini, amma suna fadin Ba na fuskantar kalubalen jan ra'ayin talakawan Sanagal kan su zabe shi.

Dan takarar shugaban kasa na Sanagal Amadou Ba ya yi jawabi a yayin gangamin da ya yi a Guediawaye a wajen birnin Dakar, Senegal March 10, 2024

'Yan adawa

Madugun 'yan adawa na SenegalOusmane Sonko ya fito daga kurkuku kwanaki 10 kafin ranar zabe, wanda hakan ya sanya ka yi ta murna a fadin kasar.

Sonko ne ya zo na uku a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2019, amma an haramta masa tsayawa takara wannan shekarar. Abokinsa Bassirou Diomaye Faye ne aka sanar a matsayin dan takarar 'yan adawa.

TRT Afrika ta bayyana cewa Senegal ba ta gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a game da zabe. Sai di kuma, ana kallon Faye dan takarar hadin gwiwa a matsayin babban dan takara a zaben.

Tare da goyon baya sosai, Sonko ya yi kira ga dukkan magoya bayansa da su marawa Faye baya a yayin da kasar ke fuskantar matsalar tattalin arziki da rashi ayyukan yi.

Idan Faye ya yi nasara, kawancen zai yi abubuwa d ayawa ga kungiyar yankin mai kasashe takwas, da kuma yunkurin kasar na tono albarkatun man fetur.

Faye ya rubuta ce wa "Na gamsu da ba za a iya samun cikakken 'yancin kai ba tare da samun ikon juya tattalin arzikin kasarka ba, kula da kiwon dabbobi, kamun kifi da ayyukan noma, shirya sosai don samun 'yanci a fanninsamar da abini,kasafin kudi, makamashi da kimiyya."

Kawancen sun bayyana cewa suna son kawar da rashin adalci, samar da ayyukan yi, inda suke son samar da ofishin mataimakin shugaban kasa tare da rushe na firaminista.

Tunanin samar da sabon kudi ma na kan gaba wajen manufofinsu. Wasu na neman a daina amfani da kudin Faransa na CFA Franc, wanda aka samar don maye gurbin Dalar Amurka, suna cewa kudi ne da aka gada daga Faransa kuma kasashen Afirka 14 suka amince suna amfani da shi.

An ga yadda 'yan adawar suke da karsashi sosai wajen son farfado da tattalin arziki da sake dawo da yarjejeniyar fitar da albarktun mai.

Ana sa ran hakar ma'adanai ma zai zama wani babban jigon farfado da tattalin arziki da yalwar jama'a.

A yayin da ake gaf da samar da mai a tsandauri a Senegal a tsakiyar 2024, kasar na neman fada kudaden shigar da take samu ta bangaren fitar da albarkatun mai.

Sonko ya yi bayani game da bukatar yaki da cin hanci da rashawa a cikin gwamnati, tare da kare tattalin arzikin kasar daga katsalandan din kasashen waje.

Ousmane Sonko na murmushi a yayin da yake sauraren dan takarar shugaban kasar da yake marawa baya a zaben 14 ga Maris,

Sonko mai shekara 49 ya fuskanci matsaloli sosai da gwamnati. An tuhume shi da manyan laifuka da suka hada da shiga kungiyar bata-gari, hada kai da 'yan ta'adda da dakile ayyukan jami'an tsaro saboda wani al'amari da ya faru a 2021.

A kan wani laifin na daban, an yanke masa hukuncin daurin shekara biyu a kurkuku saboda "lalata rayuwar mace matashiya" wand ahakan ya sanya shi gaza tsayawa takara a zabe.

Tun watan Yulin 2023 yake kurkuku, ya kuma dinga yin yajin cin abinci kafin a kai shi dakin gaggawa na asibi. An rawaito ya dakatar da yajin cin abincin bayan da malaman Musulunci a Senegal suka shiga tsakanin rikicin siyasar.

An sake shi bayan wata doka da shugaba Sall ya yi ta yin afuwa da laifukan da suka shafi zanga-zanga a 2021.

Tun bayan sakin sa, ya dinga kira da a hada kai a tsakanin mutane, yana mai nacewa da cewar an mayar da hankali ga zabuka ne, yana kuma kira ga matasa da su fita jefa kuri'a.

"Wannan ba lokacin daukar fansa ba ne. Ba za a dauki fansa ba, amma za a yi adalci. Muna da babban aiki a gaban mu. Ba mu da lokacin farautar abokan hamayya. Amma a sani karara cewa: Ba sani ba sabo," in ji Sonko a wajen taron manema labarai a babban birnin Dakar.

Rahotanni sun ce Sonko ya yi hasashen Faye, daya daga cikin manyan 'yan takara na iya samun kaso 60 a zagayen farko na zaben.

Magoya bayan 'yan adawa yayin gangami a babban birnin Dakar.

TRT World