Nijeriya na samar da megawatt 4,500 ne kawai na lantarki / Hoto: AFP

Nijeriya tana bukatar zuba jarin dala biliyan 34.5 don samar da isassehn lantarki a kasar nan da shekarar 2030, a cewar wani sabon rahoto na Kungiyar Kawance Kan Makamashi da ake Sabuntawa da kuma samar da makamashi, (REEEA-A).

Jaridar Kasuwanci ta intanet ta Businessday Nigeria wacce ta ruwaito labarin a ranar Litinin, ta bayyana cewa rahoton ya ce Nijeriya na bukatar zuba jarin dala biliyan 4.93 a duk shekara har nan da shekara bakwai don iya cimma samar da megawat 20,000 ga al’ummar kasar da yawansu ya haura miliyan 200.

A cewar wasu bayanai na samar da wutar lantarki a Nijeriya, a yanzu haka kasar na samar da megawatt 4,500 ne kawai na lantarki, duk da cewa tana da karfin samar da megawatt 13,000.

Rahoton ya fayyace cewa matsalolin rashin iskar gas da lalacewar injina da janyewar ruwa a loutan rani na daga cikin abubuwa da suka sa lamarin ke ta’azzara.

TRT Afrika da abokan hulda