Zimbabwe ta ce za ta ci tarar duk wani kasuwanci da ke amfani da hauhawar farashin canji a kasar.
Matakin hakan na zuwa ne a yayin da gwamnati kasar ke ƙoƙarin ɗaga darajar sabon kudin da ta ƙaddamar mai suna Zimbabwe Gold (ZiG).
Duk wani kasuwanci da ke amfani da farashin canji da ya zarce na hukuma kan kashi 13.5 na kudin ZiG a kowace dalar Amurka, za a ci shi tarar kudin ZiG 200,000 kwatankwacin dalar Amurka 14,815, a cewar wata sanarwar gwamnati da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Duk wanda ke gudanar da harkokin kasuwanci na ''siyar da kayayyaki ko ayyuka a farashin musayar canji da ya zarce farashin da bankuna ke sayarwa a hukumance,'' ya tafka laifin keta hakkin harar hula, in ji sanarwar da aka fitar a ƙarshen ranar Alhamis.
Tun bayan ƙaddamar da sabon kudin ZiG a farkon watan Afrilu, gwamnati Zimbabwe ke ci gaba da kokarin ganin ta ɗaga darajar kudin tare da ganin ya zaga ko ina a fadin kasar, inda hukumomi suka soma dirar mikiya kan 'yan kasuwar canjin kudi na bayan fage a watan da ya gabata.
Kudin musayar kasuwanci a hukumance
Wasu kasuwancin, kamar a manyan kantuna ana karɓar kuɗi sama da ƙimar farashin kasuwa daga hannun kwastamomin da ke biya da sabon kuɗin ƙasar, yayin da sauran 'yan kasuwa kuma suke ƙin karbar kudin ZiG din.
A ranar Talata ne sashen hada-hadar kudin Zimbabwe ya dauki matakin tilasta amfani da kudin ZiG a matsayin kudin musayar kasuwanci a hukumance.
Wannan shi ne karo na hudu cikin shekaru 10 da Zimbabwe wadda ke yankin kudancin Afirka ke kokarin samun kudinta, hakan na zuwa ne a matsayin wani mataki na ƙoƙarin shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma daidaita tattalin arzikin ƙasar da ya daɗe yana fama da tarin ƙalubale.