A watan Zul Hijjah ne ake gudanar da aikin Hajji, wato daya daga cikin shika-shikan Musulunci biyar – inda miliyoyin Musulmai suke sauke farali a Saudiyya a kowace shekara, kuma shi ne wata na 12 (na karshe) a kalandar Musulunci.
Zul Hijjah wata ne mai matukar muhimmanci ga mabiya addinin Musulunci ko da yake wannan makala za ta mayar da hankali ne a kan ranakun 10 farko na wannan ne.
Sheikh Tukur Al-Mannar da ke Kaduna a arewacin Nijeriya ya yi mana karin bayani:
Allah Ya rantse da ranakun 10 farko na Zul Hijjah
Kamar yadda Sheikh Al-Mannar ya ce: "Allah Madaukakin Sarki ya rantse da kwanakina cikin ayoyin farko na Suratul Fajr.
"Ya yi haka ne domin ya nuna mana falalar wadannan ranaku da darajarsu da kuma matsayinsu a wajen Allah."
Haka zalika malamin ya ce an samu Hadisi daga Manzon Allah SAW da yake cewa: "Babu wani aiki a wajen Allah (SWT) da yake da matukar lada kamar aikin da bawa zai yi a kwanakin 10 na farkon Zul Hijja.
Sai Sahabbai suka tambaye shi, 'Ko da kuwa jihadi ne saboda Allah?' Manzo SAW ya amsa da cewa, "Ko da kuwa jihadi ne saboda, sai dai idan mutum ya fita jihadin da dukkan dukiyarsa ya kuma koma gida ba tare da komai ba." Bukhari ne ya ruwaito wannan hadisi.
Sheikh Al-Mannar ya ce saboda wannan matsayi na wadannan ranakun ne ake kwadaitar da Musulmi su yawaita ayyukan ibada a cikinsu kamar haka:
1. Azumi
Yawaita yin azumi yana daga cikin ayyukan ake so Musulmi ya yi, kamar yadda malamin addinin ya shaida wa TRT Afrika.
Ya ce ko da Musulmi bai samu damar azumtar duka ranakun ba, to yana da kyau ya yi azumin ranar 9 ga watan wato azumin ranar Arfah kenan, musamman idan idan mutum bai samu damar zuwa aikin hajji ba.
"Manzon Allah (SAW) ya ce azumin ranar Arfah yana kankare zunubi shekara biyu wato shekarar da ta wuce da zunubin shekarar da ke tafe," in ji Sheikh Al-Mannar.
2. Tsayuwar dare
Bayan azumi, malamin ya ce yana da kyau sosai a rika yawaita tsayuwar dare wato sallolin dare a cikin kwana 10 farko na Zul Hajji.
3. Yawaita yin istigifari
Ana so bawa ya yawaita tuba da neman gafarar Ubangijinsa. Ana so bawa ya daina aika zunubai, "inda aka ce ya yi, ya yi. Inda kuma aka ce ya bari, to sai ya bari," in ji malamin.
4. Yawan yin Karatun Al-Kur'ani
Sheikh Al-Mannar ya ce idan da hali ana so bawa ya sauke Al-Kur'ani a cikin kwanakin, ko kuma abin da ya sawwaka.
5. Yawaita sadaka
Ana so bawa ya kara kaimi wajen yin kyawawan ayyuka kamar sadaka da taimako da sauransu.
Ana so a yi sadakar abinci da kayan sawa da kuma kudi saboda marasa karfi domin a wadatu ranar idin babbar sallah, a cewar malamin.
6. Sadar da zumunci
Malamin ya ce ana so Musulmi ya sadar da zumunci da 'yan uwansa musamman iyaye da 'yan uwa da abokan arziki.
"Idan mutum ba shi da halin kai ziyara, to zai iya buga waya don ya sadar da zumunci kuma ya gaishe da su," in ji Sheikh Al-Mannar.
7. Layya
Ga wanda Allah Madaukakin Sarki Ya hore ma ana so ya yi layya."Ba a so ga wanda zai yi layya ya aske farcensa da kuma gashin jikinsa a cikin wadannan ranaku 10," kamar yadda malamin addinin ya shaida wa TRT Afrika.
8. Yawaita yin addu'o'i
Abu ne mai kyau a cikin kwana 10 farko na Zul Hajji bawa ya yawaita yin addu'o'i ga iyayensa da iyalansa da shugabanninsa da kasar da yake zaune da kuma dukkan Musulmin duniya, a cewar malamin.
9. Aikin Hajji
Ana so ga wanda yake da hali ya je Saudiyya don ya sauke farali.
10. Halartar sallar Idi
A karshe ana son Musulmi su halarci sallar idi - inda za su yi raka biyu a cikin jam'i a ranar 10 ga watan. Kuma ana so a yawaita zikiri da kabbara a wadannan ranaku 10 na farkon watan Zul Hijjah.