Wani bincike ya nuna cewa kashi 48 na mutanen Afrika suna shiga damuwa da zarar cutarsu ta kai matakin da za a yi musu tiyata. Others

Kudin jinyar da ke tsiyata mutane-wannan batun mai ban tsoro gaskiya ce a wajen mutane da dama, musamman mutanen kananan kasashe masu tasowa.

Idiba Loudy Diane, wata ’yar kasar Gabon ce, wadda rashin aikin yi da kuma wata cuta mai sa raunin jiki da yake cinye mata ’yan kudaden da take tarawa suke damunta.

Cutar ta yi zafi ne a shekarar 2021 a lokacin da otel din da take iki a birnin Libreville ya daina aiki.

A shekarar 2023 kuma abubuwa suka kara rincabe mata kasancewar ga talauci, ga kuma cutar koda wadda tun tana karama take fama da ita.

“Sai komai ya kara lalacewa. Zazzabina ya kara zafi, inda nake amai ga kuma yawan gajiya,” inji ta a tattaunawarta da TRT Afrika, sannan ta kara da cewa, “sai da na kwashe wata daya a asibiti. Kodata sun daina aiki, sannan huhuna ma ya fara ciwo. Dole aka daura ni a wankin koda.”

A kasar Gabon, ana biyan CFA 200,000 domin wankin koda, wanda ya yi daidai da kimanin Dala 325.

A wajen Diane, biyan wannan kudin, abu ne mai kamar wuya. “Babbar damuwar ita ce zuwa asibiti lokaci bayan lokaci. Ga kudin motar zuwa asibitin shi kansa, kuma duk mako sau uku nake zuwa asibiti,” inji Diane.

’Yan uwanta sun taimaka mata domin ganin tana samun kulawa, amma ba kowa ba ne ke samun irin gatar da ta samu.

A Nahiyar Afrika, masana a bangaren kiwon lafiya na fargabar cewa mutanen yankin da dama suna talaucewa sakamakon jinyar a sanadiyar babbar cuta guda daya tal, matukar jinyar na daukar dogon lokaci.

Bayan kudaden da ake kashewa a asibiti, ana kuma kashe kudin mota, sannan wasu majinyatar sukan rasa hanyoyinsu na samun kudade. Hoto: Reuters

A shekarar 2020, an kiyasta cewa kashi 48 na mutanen Afrika suna shiga damuwa da zarar cutarsu ta kai matakin da za a yi musu tiyata.

Ko ma a jinyar cututtukan da ba sa bukatar tiyata, majinyata da dama sukan sayar da gonakinsu ko gidaje domin samun kudin jinya.

Wani bincike na kwanan nan da Hukumar Lafiya ta Duniya ta dauki nauyi ya yi kiyasin cewa kashi 55 na masu fama da cutar tarin fuka da iyalansu a kasashe maso tasowa guda 135 suna kashe akalla 20 na kudin da dukka iyalan gidan suke samu a shekara wajen daukar dawainiyar mutum daya daga cikinsu.

Masana sun ce, idan ya kasance kudin da ake kashewa wajen jinyar mutum daya daga cikin iyali ya ketare kason da suka shirya biya, sannan ya tilsta wa iyalan rage abinci da sauran bukatun gida, za a iya bayyana iyalan a matsayin wadanda suka shiga bala’i.

Bayan kudaden da ake kashewa a asibiti, ana kuma kashe kudin mota da abinci. Kungiyar TB Alliance, wadda aka assasa domin bincike da samowa tare da raba magungunan tarin fuka ga masu cutar, ta ce majinyata wadanda magunguna da dama suka daina aiki a jikinsu sun fi shiga cikin damuwa.

A kasar Afirka ta Kudu, majinyata da suke fama da tarin fuka, musamman talakawa, dole suke hadawa da neman abinci masu gina jiki domin samun karin garkuwar jiki.

“Majinyata da suke jinyar tarin fuka suna jin yunwa da sauri da kuma ciwon ciki,” inji Zani De Wit, wani ma’aikacin Cibiyar Huhu ta Jami’ar Cape Town a tattaunawarsa da TRT Afrika.

“Bayan rashin aikin yi da ya yi katutu da yawan mutane da karuwar aikata laifuka, Afirka Ta Kudu na kuma fama da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi. Wasu majinyatan sukan koma shaye-shaye domin ya dauke musu damuwar da suke ciki.”

Yanzu yawancin shirye-shirye da tarukan wayar da kan mutane a kan tarin fuka gwamnati da wasu kungiyoyi ne ke daukar nauyinsu domin rage wa majinyata radadi.

Amma kamar yadda Zani ya bayyana, iyalan da suke da mai fama da tarin fuka sukan, “daga kafa wajen shan maganin tarin da gangan domin samun tallafin da za su cigaba da rayuwa.”

Bayan matsalolin rashin kudi, majinyatar tarin fuka sukan shiga damuwa da fargaba da zarar an fara tunanin suna da cutar kafin su fara sabawa.

Haka ma wasu masu fama da wasu cututtukan sukan yi fama da wadannan matsaloli, duk da cewa gwamnati ke cigaba da kokarin samar da hanyoyin da za su saukaka wa marasa lafiya samun saukin jinya.

TRT Afrika