An shafe shekaru ana amfani da asawaki. Hoto/ TRT Afrika

Hassan na jingine da bangon Masallacin Noor da ke Mombasa a kasar Kenya. Yana ta asawaki a daidai lokacin da ladan ke kiran Sallar Magriba.

“Ina amfani da wannan asawakin sau uku ko hudu a rana. Yana tsaftace bakina. Na shafe shekaru ina amfani da shi – tun ina yaro ma,” in ji Hassan. Ana kiransa da siwaak, wato Asawaki.

A birnin Mombasa, asawaki wani abin tsaftace baki ne da aka san shi sosai, musamman ga dattawa. Suna kiran shi da “mswaki” da harshen Swahili.

Yayin da mutane ke gittawa zuwa masallaci daya bayan daya, akasarinsu suna amfani da shi.

Hassan ya bayyana cewa yana ganin asawaki na masa amfani don kare lafiyarsa, “Wannan asawakin ana kiransa Msija. Yana taimakawa wurin kawar da warin baki da kashe cututtuka.”

A kauyen Korogwe da ke birnin Tanga na Tanzania mai nisan kilomita 260, Paulo Matini na kan hanyarsa ta zuwa aikin gadi da na dare. Ya saka tufafin gargajiya na kabilar Maasai kuma yana amfani da asawaki.

“Tun muna yara muke amfani da asawaki ba tare da wani man goge baki ba,” in ji shi.

Saukin samu da saukin amfani

Ana iya samun asawaki daga itace daban-daban, ya danganta da inda mutum yake. Zai kuma iya bambanta dangane da launinsa da yanayin girmansa ko kuma dandanonsa.

A India, asawakin da ake yawan amfani da shi ana samunsa ne daga bishiyar dalbejiya. A Yammacin Afirka kuwa, an fi amfani da icen lemun tsami ko kuwa lemun zaki.

A wasu sassa kuma na nahiyar Afirka, ana amfani da tafasa.A Gabas ta Tsakiya da kuma Gabashin Afirka, ana samun asawaki daga bishiyar faru, wadda ake yawan samu a cikin daji.

Ana samun asawaki daga itace iri daban-daban. Hoto/TRT Afrika

Asawaki dai ana yawan samar da shi ne da tsawon 15cm sa’annan fadin sa ya kasance 1cm domin shiga baki cikin sauki da kuma amfani da shi.

A tsakiyarsa akwai wani abu mai kama da soso.

Idan aka tsoma shi cikin ruwa na tsawon akalla minti daya zuwa biyu, asawakin yana saukin taunawa da kuma amfani. Idan aka taune karshensa, yakan zama kamar buroshi wanda mutum zai iya amfani da shi wurin goge bakinsa.

Dadewar asawaki

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar soma amfani a asawaki tun a 1986.

Zuwa karni na 21, wani rahoto na kasa da kasa kan tsaftar baki ya karkare da cewa akwai bukatar a kara bincike idan ana so a tabbatar da illar asawaki kan lafiyar hakori ko baki.

A gargajiyance, akasarin mutanen da ke Arewacin Afrika da Gabashin Afirka da kuma kasashen Larabawa na alakanta amfanin asawaki da karantarwar Annabi Muhammadu (S.A.W).

“Ana so a yi amfani da asawaki kafin Sallah, da bayan tashi daga bacci, kafin zuwa masallaci, kafin shiga gida da kuma bayan dawowa daga tafiya,” kamar yadda Sheikh Shaaban daga Nairobi ya shaida wa TRT Afrika.

Amma ga ‘yan Afrika da dama, ya fi zama wani lamari na al’ada da aka gada kaka da kakanni.

“Iyayenmu da kakanninmu suka koya mana amfani da asawaki tun muna kanana,” kamar yadda Paulo na kasar Tanzania ya kara bayyanawa.

Paulo Matini ya bayyana cewa tun yana yaro karami ya fara amfani da asawaki. Hoto/TRT Afrika

Akwai ra’ayoyi daban-daban kan binciken da aka yi game da amfanin asawaki ko akasin hakan.

Dakta Ramadhan Shaali, malami a Sashen Nazarin Hakori a Jami’ar Zanzibar, ya ce duk da masu bincike sun samu bambancin ra’ayi dangane da amfanin asawaki, amma wasu binciken kuma sun nuna amfaninsa.

Hujjojin da ake da su a kasa sun yi kadan a kimiyyance a yanke hukunci da su.

“Daya daga cikin sinadaran da man goge baki yake dauke da su shi ne fluoride, wanda yake taimakawa wurin kare baki daga rami na hakori.

Amfani da asawaki kadai zai sa mutum ya rasa wannan kariya,” in ji Dakta Ramadhan.

Likitoci ba za su iya bayar da cikakkun bayanai ba saboda bukatar karin bincike, amma Dakta Ramadhan ya bayyana cewa akwai wasu nau’in barazana da ke tafe da amfani da asawaki da suka hada da kawo matsala ga dasashi da lalata tushen hakori ko kuma saman hakori sakamakon yawan gurza asawakin.

“Za ka iya zabar asawaki a maimakon buroshi da man goge baki domin samun biyan bukata,” in ji Dakta Ramadhan. “Kalubalen shi ne amfani da shi a maimakon na gargajiya.”

Tsafta ba ta da tsada

A wasu yankuna musamman wuraren da ake samun itacen da ake samun asawaki daga gare su, amfani da asawaki ya fi sauki ta bangaren tattalin aljihu a maimakon wanda aka saba da shi.

Koyarwar addinin Musulunci ta jaddada amfani da asawaki musamman kafin gudanar da salloli. Hoto/TRT Afrika

Misali a Uganda, akwai wasu nau’in itace biyu da ake amfani da su kuma daya daga cikinsu shi ne "akakwansokwanso".

“Wani abu mai kyau game da wannan shi ne zan iya amfani da shi sau daya, na jefar da shi na sake karyo wani domin amfani daga baya,” in ji Paulo mai gadin dare.

A birnin Korogwe na Tanzania, dan jarida Majuka na da asawaki a cikin bakinsa a lokacin da yake zaune a wajen gidansa da dare.

“Akwai itace da dama da ke da dandano iri daban-daban da za a iya zaba. Za ka iya amfani da daya da safe daya kuma da dare,” in ji shi.

Kamar yadda WHO ta bayyana, amfani da buroshi da man goge baki ya fi nagarta idan ana maganar tsaftar baki.

Shi ma asawaki zai iya yin wannan aikin ta hanyar yakar cututtukan da ke kan hakori ko dasashi.

Saboda yana dauke da sinadarai kamar Chloride da sodium bicarbonate da kuma potassium, zai iya taimakawa wurin kara kwarin hakori daga tushensa, wanda zai sa baki ya zama cikin tsafta.

TRT Afrika