Tsarin ilimin yana da rauni amma ana kokari wajen tallafar sa. Hoto: Shule Direc

Daga Nuri Aden

Lokacin da ta hau minbari a matsayin 'yar takara sarauniyar kyau, kwarjininta ya sanya mutane ajiyar zuciya, saboda kyawunta. Faraja Nyalandu, ta zamo Sarauniyar Kyau ta Tanzaniya a 2004, inda bayan nan ta kaddamar da ayyuka don kawo sauyi a kasarta.

Faraja ta kafa cibiyar Shule Direct, wani dandali na fasaha wanda ke bai wa miliyoyin yara a kanana da manyan makarantun sakandare a fadin Tanzaniya, damar samun kayayyakin karatu, wadanda a baya ba sa samu.

Ta dauki shekara hudu bayan kammala jami'ar East London, inda ta karanci shari'a a shekarar 2009, kafin ta shiga aikin da yake kawo gagarumin cigaba ga bangaren ilimi a kasarta.

Kishin da Faraja take da shi ya sanya tsarin ilimin kasar ya cimma mafi nisan kuryar kasar Tanzaniya, bayan an kaddamar da shirin a babban birnin kasar na Dar es Salaam.

Ga masu karamin karfi a karkarar Tanzaniya, wannan hanya ta samar da tallafin kayayyakin ilimi cikin sauki, wata alfarma ce ga mutanen kasar, wadanda yaransu suke samun damar kubuta daga talauci, ta bin tafarkin ilimi.

Faraja mace ce da aka haifa cikin arziki kuma ta yi karatu a mafi kyawun makarantu, kuma tana cikin mutane masu hannu da shuni, amma ta yanke hukunci fara tallafawa marasa galihu.

Labarin Faraja yana nuna fahimtar mutane game da tasirin fasahar zamani wajen kawo sauyi a kasa.

  Faraja Kotta Nyalandu ta ce burinta shi ne tabbatar da ilimi mai inganci. Hoto: TRT World

"Fasaha tana da gagarumin tasiri wajen cimma manufofin ilimi da karantarwa. Cibiyar Shule Direct tana samar da kayayyakin ilimi ta intanet, da wayar hannu. Wannan ya hada da horo a darussa da dama, wanda suka dace da tsarin ilimin kasa," Faraja ta sanar da TRT Afrika, bayan taron TRT World Forum's NEXT conference.

Ta bayyana cewa, “Fasaha tana da muhimmanci ga ilimin yara mata, idan yarinya ta rasa darasi saboda aikin gida, ko wasu lokuta saboda juna biyu, ko matsalolin iyali, to Shule Direct za ta saukaka mata samun karatu a gida".

Kudurin rayuwa

Duk da ta samun rayuwa mai sauki a yarintarta, kamar karatu a birnin Dar es Salaam da fita kasar wajen don karatun jami'a, Faraja ba ta banzantar da bukatun marasa galihu ba.

A 2013, ta kafa cibiyar Shule Direct don karfafa kwarewar da ta samu na karatu ta intanet, don kyautata daidato tsakanin neman ilimi da rayuwar gida.

Faraja ta san kalubalen da ke cikin neman ilimi a gida Tanzaniya, wanda ya karfafe ta wajen samar da mafita da za ta inganta bangaren ilimi, ta amfani da kwamfuta wajen samar da kayan karatu ga dalibai daga ko'ina.

Tanzaniya children from less privileged are expected from the education app. Photo: Shule Direct

Faraja ta ce cibiyar Shule Direct yanzu tana tallafawa dalibai marasa galihu. Kafar da ta samar tana taimakon su kwarewa kan dabarun iya kwamfuta, don musu tanadin aiki a nan gaba.

Cibiyar Shule Direct tana hada gwiwa da kwararrun malamai don gina kafar intanet don samar da kayayyakin karatu kamar horo, da darussa, da jarrabawa, da hotuna da bidiyo.

A cewar Faraja, cibiyar Shule Direct tana cike gibin yawan malamai a kasa. Bayanan da aka samu a baya kan ilimin firamare a Tanzaniya ya nuna akwai matsalar yawan malamai ga duka dalibai, wanda yake a malami 1: dalibai 180, inda ake neman malaman firamare 40,000.

Daidaiton Ilimin

Tanzaniya kasa ce mai yawan mutane masu kananan shekaru, sama da kashi 50 na 'yan kasar suna da shekara 18 ko kasa. Suna fuskantar kalubalen ilimi, duk da gwamnati ta kaddamar da ilimi kyauta a matakin firamare da sakandire.

Rahotanni kan cigaban ilimi a Tanzaniya ya nuna bangaren yana fama da kalubale kamar karancin kwararrun malamai, rashin kayan aiki, da azuzuwa, da kayan karantarwa.

A farkon 2023, Hukumar Jarrabawa ta Kasa ta Tanzaniya ta dakatar da tsarin jera martabar makarantu

Yayin sanar da shirin, shugaban hukumar na riko, Salumu Amasi, ta ambata matsalar rashin daidaiton gogayya, da tazara tsakanin makarantun birni da na kauye, ya yawaitan wuraren karatu marsa inganci.

Faraja ta ce tana fatan cimma bukatun cigaban ilimi a Tanzaniya. Hoto: Shule Direct

Ta ce, "A nan ne cibiyar Shule Direct take taka rawa. "Muna amfani da dandalin fasaha don samar da ilimin ga daliban firmare da sakanadire da samar wa malamai karin ilimi don kwarewa".

Yunkurinta yana janyo hankali, inda ayyukan cibiyar Shule Direct ya sanaya ta samu kyautukan yabo.

Faraja ta samu lambar yabo ta "Jagorar mata Fagen fasaha a Afirka". A 2016, an ba ta kyautar Nagartar Shugabanci a Tanzaniya Leadership. Sai kuma lambar Africa Youth Awards, wanda ta ayyana Faraja cikin Matasa100 Masu Fada a Ji a Afirka.

Faraja tana cikin kwamitin gudanarwa na cibiyoyi, kuma ita ce shugaban kwamitin Gamayyar Ilimi a Tanzaniya, wato Mtandao wa Elimu Tanzaniya.

A karshen bara, an zabe ta a matsayin mambar Shirin Global Campaign for Education (GCE). A 2020, an ambaci sunanta cikin Jagororin Ma taron World Economic Forum.

A matsayinta na matashiya, kuma mafi karancin shekaru a danginta, wanna ya nuna nasarar da Faraji ta samu, bayan lashe gasar sarauniyar kyau.

TRT Afrika