Danyen lu'u lu'u yayin da aka baje-kolinsu a kamfanin Lu'u lu'u na kasar wato Botswana Diamond Valuing Company a birnin Gaborone. Hoto: Reuters       

Daga

Calistus Bosaletswe

Lu'u-lu'un zai iya kasancewa har abada bai yi komai ba, sai dai babu dangataka mai karfi tsakanin kasar da ta fi kowace kasar arzikin lu'u lu'u a Afirka da babban kamfanin hako lu'u-lu'u na duniya.

Botswana tana kokarin kulla yarjejeniya mai tsawo da kamfanin da ke hakowa da kasuwancin Lu'u-Lu'u na De Beers don sabunta yarjejeniyar kasuwanci ta shekarar 2011, sai dai akwai damuwa cewa kamfanin yana tafiyar hawayyina kan batun ware kudin aikin.

Cibiyar tattaunawa kan Debswana wata yarjejeniyar raba ta daidai (50:50) tsakanin gwamnati da kamfanin De Beers da ta zo karshe a shekarar 2021.

Yarjejeniyoyin wadanda ba su cimma burin da ake so ba – an tsawaita su zuwa ranar 30 ga watan Yunin bana bayan duka bangarorin biyu sun ce annobar korona ce ta sa ba su iya cimma matsaya ba.

Shugaba Mokgweetsi Masisi ya bukaci cewa dole ne Botswana ta samu kaso mai tsoka daga Lu'u lu'u da ake hakowa, wani yunkuri da masana suke gani da na-je-ka-na-yi-ka ne yayin da wasu suke fatan cewa tattaunawar za ta amfani Botswana.

Botswana ita ce kasa ta uku da ta fi hako lu'u lu'u a duniya a shekarar 2021. Hoto: AFP

Shugaba Masisi ya yi barazanar cewa Botswana za ta kawo karshen huldar da take yi da kamfanin De Beers, idan har ba za ta samu riba a karshen kulla yarjejeniyar ba.

Sai dai Roman Grynberg wani tsohon mai bincike a Cibiyar Nazari da Ci gaba da Tsare-tsare ta Botswana, ya yi amannar cewa ba ta da sauran iko kan yadda yarjejeniyar za ta kasance.

Grynberg, wanda tsohon masanin tattalin arziki ne a wata hukuma da ke nazari mai zurfi kan al'amura ta BIDPA, a wani bincike kan lu'u lu'u da shi da wasu abokan aikinsa biyu suka gudanar, sun yi gargadin cewa — mai taken Gem Quality Diamonds and their Potential Impact on the Botswana Economy — ba sai ka yi dogon nazari ba kafin ka gane cewa Botswana ce za ta kwaru daga matsalar samar da duwatsu masu daraja da ake samarwa a dakin binciken kimiyya.

Ya ce yana jin tsoro yadda ake samun dimbin lu'u lu'u da ake samarwa a dakin bincike kimiyya da ke kashe kasuwar wadda Botswana take hakowa, wanda hakan ya sa shafi karfin tattalin arzikin Botswana a shekara 10 da suka wuce.

Yaya kamata a raba lu'u lu'un

Lu'u lu'u yana samar wa Botswana kaso 80 cikin na kudin ketare kuma yana samar wa kasar kaso 50 cikin 100 na gaba dayan kudin shigar da kasar ke samu. Kasar ta fitar da lu'u lu'u da kudinsa ya kai dala biliyan hudu a shekarar 2020.

Danyen lu'u lu'u yayin da ake sarrafa shi a kamfanin processed Botswana Diamond Valuing Company a Gab. Hoto: Reuters

Yarjejeniyar Debswana, wadda aka kulla tsakanin gwamnatin kasar da kamfanin De Beers wanda yake da ma'aikata fiye da 5,000 da 'yan kwangila masu tarin yawa.

Karkashin yarjejeniyar 2011, kamfanin De Beers zai samu kaso 90 cikin 100 na danyen lu'u lu'un da aka hako a Botswana. A shekarar 2020, an kara adadin da Botswana take samu da kaso 25 cikin 100.

Akwai maganganu da ke yawo da ke cewa Botswana tana bukatar fiye da kaso 25 cikin 100 na lu'u lu'un da kamfanin Debswana ya jako kuma ya sayar ta hannun kamfanin lu'u lu'un kasar mai suna Okavango Diamond Company.

Shugaba Masisi ya ce yarjejeniyar 2011 ba ta yi wa Botswana adalci ba, ya dage kan cewa kasar ta bukatar kaso mai yawa na albarkatun lu'u lu'un.

Ba a saka Ministan kamashi da albarkatu na kasar Moagi Lefoko, a cikin tattaunawar da ake yi tsakanin gwamnatin da kamfanin De Beers bayan da suka fitar da takardar hadin gwiwa kan cewa babu wanda zai yi magana kan batun.

Wasu ma'aikata yayin da suke gyara lu'u lu'u a birnin Gaborone a Botswana, daya daga cikin kasashen da suka fi samar da lu'u lu'u. Hoto: Getty

Obuseng Sennye, wani tsohon masani kan tattalin arziki a bangaren shirin ci gaba na Majalisar Dinkin Duniya ya ce Botswana tana 'yancin "neman" kaso mai tsoka kan albarkatun.

Ya ce bai amince da maganar da wasu suke yi cewa matasa ba sa son lu'u lu'un da aka samar a dakin bincken kimiyya kuma cewa hakan zai zama matsala ga lu'u lu'un Botswana.

"Ko da ana samun sauyin, ba wata babbar matsala ba ce ga lu'u lu'un. Kudin shiga musamman a tsakanin matasa da son yin amfani da kaya masu tsada kuma lu'u lu'un yana cikin abubuwan da ke sahun gaba da ake yin kawa da su," in ji shi.

Sennye yana ganin matasa ba kawai suna da fasaha ba, kuma suna da kudin shiga fiye da tsofaffin. "Ina sa ran kasuwar lu'u lu'u ta karu saboda mutane suna kashe kudi sosai kan abubuwan alatu," in ji shi.

Wani lu'u lu'un da aka samar da shi daga dakin binciken kimiyya yayin da aka baje-kolinsa a wani wajen bincike da nazarin lu'u lu'u na kamfanin De Beers a garin Maidenhead a Ingila. Hoto: Reuters 

Fiye da komai, Sennye ya ce "a ganina" kamfanin De Beers zai mika wuya, kodayake ba yadda Botswana take fata ba.

Titose Thipe, wani masani ne kan hako ma'adanai wanda yake aiki da Debswana, ya ce Botswana tana yin abin da ya dace wajen neman karin kaso dags lu'u lu'un da ake hakowa a kasar.

Ya kafe kan cewa raba ta daidai (50:50) yana nufin kowane kowane bangare ya amfana, idan aka hada hakan da tsantsar gaskiya da amfana da baje komai a faifai.

Kamar yadda Thipe ya ce, sauran kasashen za su iya kwaikwayon Botswana don neman kaso mai tsoka na kwangiloli da kamfanoni da suke hako ma'adanansu.

"Ya kamata kasashen Afirka su tashi tsaye kan albarkatunsu, ta yadda za a kulla yarjejeniya da za ta amfani duka bangarorin biyu."

Arzikin kasa

Mahakar ma'adanai ta Jwaneng,wacce take kudancin kasar, ana hako lu'u lu'u masu daraja a kowace shekara da nauyinsa ya kai carat miliyan 12.

Ba a samun wuraren hako ma'adanai ba bisa ka'ida ba a Botswana ban da wasu tsofaffin wuraren hakar ma'adanai da ke arewacin kasar.

Katlego Mphoeng, wata daliba da ke shekara ta hudu a Jami'ar Botswana ta ce ya kamata ne kasar da ta mallaki arzikin ta fi amfana da shi.

"Abin da ka wai kamfanin De Beers yake samarwa shi ne injinan aiki, wadanda za mu iya samarwa kanmu cikin sauki," in ji ta, ta kuma ci gaba da cewa yanzu lokaci ya yi da ya kamata kasashen su karbo abin da yake mallakinsu.

An gano lu'u lu'un da ya kai nauyin karat 1,174 a Botswana a shekarar 2021. Hoto: Reuters 

Ta ce ya kamata Botswana ta nemi yarjejeniyar da za a mata adalci da kamfanin De Beers, wato a samar da abin da yake daban daga wasu kasashen Afirka da ake ci da guminsu da sace musu albarkatu yayin da mutane suke zaune cikin talauci.

Mphoeng ta ce biliyoyin kudin da Botswana take asara za a iya karkatar da su wajen ayyukan ci gaba da samar da hanyoyi da samar da magunguna a asibitoci.

Wani dan Botswana Bakang Khumoila ya ce "kowane dan kasa" yana da hakki kan albarkatun lu'u lu'un kasar.

"Wadannan albarkatu za su iya zama silar matsaloli da suka addabi kasar kamar rashin aikin yi da talauci. An kwashe tsawon lokaci ana ci da gumin Botswana."

Shi ma wani dan kasar Dizzy Mpoloka, ya ce zai so ganin ranar da gwamnatin kasar za ta kulla yarjejeniyar raba ta daidai (50:50) da kamfanin De Beers.

TRT Afrika