Aikin ceton mutanen da ke da rai yana ci gaba a Mbankolo, bayan zaftarewar kasa da ta kashe mutane 30. / Hoto: TRT Afrika

Daga Anne Nzouankeu

Mako ɗaya baya, a daidai wajen nan, gida ne ke tsaye, da mutane a ciki suna rayuwarsu. Amma a yanzu babu komai sai tarin tabo cakuɗe da ɓaraguzan katako da duwatsu.

Yayin da ma'aikatan ceto suke tsaka da neman alamar wani mai sauran numfashi, Madame Salatou tana tsaye tana kallon irin barnar da zaftarewar kasa ta yi wa gidan da mutane ke rayuwa a baya.

Ta fada wa TRT Afrika cewa, "'Yar-uwata ta rayu a nan tare da 'ya'yanta uku. Ban ƙara jin labarinsu ba tun Lahadi (8 ga Oktoba). Shi ya sa na zo nan don na duba".

Kusan mako daya bayan zaftarewar ƙasa da ambaliya da suka auku a gundumar yammacin Yaoundé, babban birnin Kamaru, amma fatan samun mutane da ransu cikin ɓaraguzan yana ƙarewa a hankali.

Akalla mutum bakwai har yanzu ba a gan su ba, amma Salatou ba ita kaɗai ce ke tararrabin jiran labari mai daɗi ba. Wata matar ita kuma tana neman 'ya'yanta biyu da ɗan ƙanwarta wanda ya zo halartar bikin ranar haihuwa a maƙwabta.

Jagoran rukunin jami'an kashe gobara na yankin, Bomba Etoundi ya ce, "A hukumance mutum 30 ne suka mutu, yayin da mutum 20 suka jikkata. Tawagarmu suna ƙoƙari don ceto rayuka."

Rayuwa a bakin gaba

Binciken matakin farko ya nuna cewa dalilai da yawa ne suka haifar da zaftarewar kasa, daya daga cikinsu shi ne gini ba tare da izinin hukumomi ba.

Gidajen da abin ya shafa duka an gina su ne a bakin Tsaunin Mont Mbankolo, wani sanannen tsauni mai tsayin sama da mita 1,000.

Wata hanyar ruwa wadda asali take gangarowa kasa, an toshe ta da ginin katangar da ta samar da wani gulbi a kasan tsaunin.

Mamakon ruwan sama a Yaoundé ya janyo zaftarewar kasa. / Hoto: TRT Afrika

Etoundi ya bayyana cewa, "Mutane sun fara yin gini a wuraren da ruwa ke gudana, wannan shi ne tushen matsalar".

Ruwan sama marka-marka a garin Yaoundé tsawon darare biyu wanda ya faro daga 8 ga watan Oktoba shi ya yi silar wannan musiba.

Etoundi ya ƙara da cewa, "Sakamakon mamakon ruwan, yawan ruwan da ke taruwa a tafkin ya ƙaru har ya ɓalla katangar da ke tare shi. Yayin da katangar ta kau, ruwan ya tumbatsa ya lahanta gidaje da ke kan hanyarsa".

Mazauna yankin da abin ya shafa sun ambata yadda mummunan abin ya faru. Virginie Tchaleng ta ce, "Da kusan karfe 6.30 na yamma, mun ji wata kara, tamkar katon dutse yana fadowa kan mu. Kawai sai muka samu kanmu cikin ambaliya. Tafkin da ke saman mu ya yanke ya tafi da kanwata da yara uku."

"Ban samu lokacin ankarar da makotana ba. Ni da 'ya'yana da kyar muka kubuta, sai da taimakon sauran makota."

Virginie ta ambata lokacin da ita da iyalanta suka tare a wajen a shekarar 2013, tafkin ya kasance a nan kuma mutane suna kiwon kifi a cikinsa.

Virginie ta fada wa TRT Afrika cewa, "Ba mu taba sanin yankin yana cikin hadari ba".

Célestine Ketcha Courtes, Ministan Gidaje na Kamaru, bayan ziyartar wajen da abin ya faru, ya ce dole a tsaurara bin ka'idojin gine-gine.

Ya ce, "Asarar rayuka abu ne mara dadi, kuma muna mika ta'aziyyarmu ga iyalan da abin ya shafa.

"Abin lura na farko shi ne an toshe hanyar ruwa, kuma mazaunin ruwan ma an cike shi. Idan ruwa ya so wucewa, sai ya nemar wa kansa hanya."

Yin gini da kaya marasa inganci ya taimaka wajen zaftarewar kasar. / Hoto: TRT Afrika

Ministan ya yi alkawarin za a "takaita gini barkatai wanda ke haifar da matsalar", ta hanyar wajabta yin takardun izinin gina gida.

Ta ce, "Sau da yawa, wadannan gidajen ba su da izinin gini, babu takardar kasa, ko kuma sun yi gini ba tare da biyayya ga dokar gini ba. Muna yawan fadakarwa kan bukatar biyayya ga tsarin dokar gini".

"Ya wajaba mutane su samu izini kafin yin kowane gini. Za mu tabbatar da mutane, da masu kamfanin gini a yankin sun bi ka'idar yin gini."

Masifa mai yawan faruwa

Ba wannan ne karon farko da rashin biyayya ga dokar gini ke janyo musiba a Kamaru ba. A kasa da shekara daya, kusan mutum 100 sun mutu sakamakon gina ba tsari. Kafin musibar Mbankolo, zaftarewar kasa a gundumar Damas ta kashe mutum 15.

A watan Yuli, gidaje biyu sun rushe a Douala, mutane 37 suka rasu. Kuma a wannan watan, wani gini ya ruguje a Limbé, ya kashe mutum biyu.

Atanga Nji, Ministan hukumar yanki, ya ce babbar manufar ita ce ceton rayuka, da samar da tsaro a yankin, da wayar da kan gamagarin mutane, da tashin mutane daga wuraren da ba su dace da zama ba.

Ministan Gidaje Ketcha Courtes ya sanar da cewa, "Tsarin da za a jaddada shi ne haramta masu gina matsuguni, da mayar da hankali kan mutane su gane hadarin zama a wuraren da ba su dace da zama ba".

Ta ce, "Muna neman mutane su taimaka wajen kawo rahoton gine-ginen da suka nuna alamun suna cikin hadari, domin a rushe su saboda kawar da bala'i".

A Mbankolo, ana ajiye da iyalai sama da 60 da suka rasa muhallinsu a cibiyoyin walwalar jama'a da ke gundumomi makota. Sake gina rayuwarsu ba abu ne mai sauƙi ba, amma a yanzu, suna sanbarkar cewa sun tsira da ransu bayan gamo da masifa.

TRT Afrika