Masu sayar da kayan miya a Nairobi na fama da yadda kasuwancin ke durkushewa saboda illar sauyin yanayi. Hoto TRT Afrika 

Daga Dayo Yussuf

Kullum da asuba, Nuria kan bi jerin gwanon masu sayar da kayayyaki zuwa kasuwa, inda take sarin kayan miya ta sayarwa mutanen unguwarta don samun ribar da ba ta taka kara ta karya ba.

Ta shafe shekara bakwai tana wannan sana'a, amma a yanzu da kyar take iya ciyar da iyalanta da dan abin da take samu din.

"Da dan kudin da nake samu nake kula da 'ya'yana. A da kudin kan ishe ni," kamar yadda matar 'yar kasar Kenya ta shaida wa TRT Afrika. "Amma yanzu komai ya yi tsada, kuma ina fargabar kar yau da gobe ta saka ni yin wani abin daban. Komai ya yi tsada."

A lokuta da yawa Nuria kan je kasuwa amma haka take komawa gida hannu rabbana. Ko dai kaya sun yi matukar tsada babu rangwame, ko kuma ta rasa irin kayan miyar da aka fi son saya a unguwarta.

"A da ina sayen dan karamin buhun albasa a kan kudi shilling 1,200 kwatankwacin dala tara, a yanzu kuwa farashinsa ya koma shilling 2,800 wato dala 19," ta fada. "Idan na saya a kan wannan farashin, to nawa zan sayar wa mutane?"

Nuria na daga cikin miliyoyin mutane a nahiyar Afirka - da biliyoyi a fadin duniya da ke fama da tasirin sauyin yanayi da suka hada da fari da rashin samun amfanin gona.

Tasirin sauyin yanayi na shafar ayyukan gona inda farashin kayan abinci ke sake hauhawa. Hoto : TRT Afrika 

Manoma a fadin Afirka suna cewa ba sa samun amfanin gona da yawa kamar yadda suke samu a baya. Wasu lokutan har damina ta fita amfanin gonar ba ya samuwa sosai, lamarin da ke ta'azzara karancin abinci da hauhawar farashi.

"Ana tattauna batun sauyin yanayi a dukkan manyan taruka na shugabannin gwamnatoci da kungiyoyin kasa da kasa da masu fafutuka. Abin lura shi ne cewa wannan abu ne da ya shafi mutanen kauyuka kai tsaye," a cewar Ellen Otaru, wata kwararriya kan muhalli a Tanzania.

"Amma dai abu ne da ke shafar kowa da kowa — daga kan manoma zuwa masunta, da masu noman zuma da ma duk wanda ya dogara kan amfanin noma ko ma'adanai don ya rayu."

Kaduwa da mamaki

A yayin da fari ke ta'azzara a wasu yankunan Afirka, inda gonaki ke ta bushewa, su kuwa sauran sassan duniya fama suke da munanan ambaliyar da ke lalata amfanin gona tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Idan har da a ce sauyin yanayi yana da kamanni, to da barna ce za ta fi dacewa da duskarsa.

Gurbataccen hayaki da masana'antu ke fitarwa na sake dumama yanayi. Hoto Reuters

Bayan da aka sake samun wata kakar mai cike da yanayi mai tsanani a wasu sassan duniya, a yanzu ana hada karfi da kardw don yaki da bala'in da ke tunkaro mu.

Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin irin kalubalen da ke tattare da hakan tare da yin kira kan a bai wa lamarin fifiko.

A cikin dan yankin da take rayuwa can nesa da inda ake tattauna batun sauyin yanayi a duniya, Nuria ba za ta iya fahimtar dalilin da ya sa ba ta iya sayen kayan miya ba a farashin da a baya take samun ribar da take iya daukar dawainiyarta. Tana yawan korafin cewa "hadamammun manoma" ne suke kara farashin kayayyaki don rashin tausayi.

A cikin mako dayan da ya wuce, babban birnin Kenya, Nairobi ya kasance a cike inda ya karbi bakuncin mutane daga fadin duniya a taron sauyin yanayi da ya karbi bakunci, inda aka tattauna tasirin sauyin yanaui da yiwuwar warware kalubalen da suke ta'azzara shi.

Nuria ta ce ta san Nairobi na karbar bakuncin taron Sauyin Yanayi na Afirka ne a ranakun 4 zuwa 6 ga watan Agusta, wanda shi ne na farko da nahiyar ta yi, a labaran yamma, amma ba ta fahimci aklakar taron da rayuwarta ba.

A wannan gabar ne masu fafutukar alkinta muhalli irin su Otaru suka shigo ciki.

"Batun da muka raina ba ma ba shi muhimmanci a yanzu shi ke ta'azzara matsalolin da duniya ke fuskanta," ta ce. "Dole a yi ta wayar wa da mutane kai sosai cewa ba a masana'antu ake samar da ruwa ba fa.

Idan ka yi barnar ruwa a gida, to kana barnata ajiyarmu ne. Yanzu idan aka ce babu ruwan sama, ta ina za mu mayar da ruwanmu? Idan ka bar wuta a kunne ba dalili tsawon yini, hakan na kara sa dumamar yanayi."

Hayakin masana'antu ma na yi wa muhalli mummunar illa. "Ba ma fahimtar cewa dukkanmu muna da hannu wajen kara lalata muhallanmu. Don haka ya kamata a ce muna sa hannu wajen ceto duniyar tamu ma," a cewar Otaru.

Neman mafita

Manyan batutuwan duniya kamar sauyin yanayi da dumamar yanayi da komawa amfani da makamashi marar gurbata muhalli ba abubuwa ne da suka kamata a dinga tattauna su cikin sirri ba.

Kwararru sun ce idan ana tattauna su a bayyane, to za a fi saurin iya samar musu mafita.

Masu fafutuka sun ce ya kamata mata da dama su shiga cikin fafutukar don magance sauyin yanayi. Hoto : AP

"Idan har mutumin kauye bai fahimci sauyin yanayi ba, ba ta kuma fahimci irin tasirin da yake yi a ranta ba, to ba za ta iya saisaita rayuwarta yadda ya kamata ba," kamar yadda Otaru ta bayyana.

"Abu ne mai kyau yadda a yanzu ake yawan kiran mata wajen irin wannan tattaunawa don su san me ake ciki."

Masu fafutuka sun ce ya kamata mata da dama su shiga cikin fafutukar don magance sauyin yanayi.

"Idan har mace ta fahimci sauyin yanayi, za ta gane dalilin da ya sa abubuwa da yawa ba sa tafiya daidai a rayuwarta. Idan har iyali ba za su iya ci gaba da samun abin tafiyar da rayuwarsu ba, musamman wadanda suka dogara kan noma, kuma idan babu kudin da za su yi bukatunsu, tabbas ba za a samu zaman lafiya ba a gidan," in ji Otaru.

Kai tsaye ta kuma alakanta wasu gama-garin matsaloli kamar cutar tsananin damuwa da talauci wanda sauyin yanayi ke jawowa.

"A wasu lokutan, matsin lambar tattalin arziki na tursasa wa iyalai rabuwa. Maigidan da a baya yake aiki noma a gonatare da iyalansa a yanzu ya koma birnin don neman wasu hanyoyin samun kudin. Hakan yakan shafi 'ya'yansa," ta shaida wa TRT Afrika.

Kowane karamin mataki zai taimaka

A cewar kwararru, ba ko yaushe ne za a ce gwamnati ce zat samar da mafita ba. Kowane dan karamin kokari zai iya tasiri, musamman idan aka saka matasa a cikin lamarin.

Lokaci ya yi da za a sako matasa a cikin tattaunawar da ta shafi wayar da kai kan sauyin yanayi in ji kwararru. / Hoto : Reuters

"Sauyin yanayi matsala ce ta kowa. Yana da muhimmanci kowa ya fahimce shi tare da sa hannu wajen magance shi tun daga kan yara kanana," Otaru ta fada. "Mafi muhimmanci, ya kamata kowa ya sauya salon rayuwarsa bisa ga abin da ke faruwa a kewayensa, ciki har da sauyin yanayi."

Bankin Duniya ya bayyana cewa nan da 2025 Afirka ce z ata zama mamallakin kaso 40 na matasa masu kananan shekaru a tsakanin kashe masu taso wa.

"Ana bukatar manyan dabaru don tabbatar da biyan bukatu, da suka hada da abinci. Game da hakan, akwai bukatar a shirya abubuwa don tabbatar da cigaba da dorewar tsarin samar da abinci," in ji bankin.

A kauyensu, Nuria na jin a kowacce rana ba ta iya samun kudaden da za ta dauki nauyin iyalinta.

Ta yi korafi da cewa "A wadannan ranaku, mutane ba sa sayen kayan abinci kamar su tumatur. Ana takura min ne ina tallan su."

A Nairobi, inda aka kammala taro kan Sauyin Yanayi a ranar 6 ga Agusta, gidajen rediyo da talabijin sun cika da labaran alkawuran da wakilan kasashen duniya suka yi da shirin da suke da shi na makomar duniya.

Nuria ta kalli labaran tare da iyalanta don sanin me ke gudana, amma za a dauki lokaci mai tsawo don fahimtar da mutane irin ta su gane me ya sa ya kamata su ma su zama jakadaun ayyukan kubutar da duniyar nan da muke ciki.

TRT Afrika