Rundunar sojin saman Nijeriya ta musanta cewa ita ce ta kai harin na Kaduna amma daga baya rundunar sojin ƙasa ta amince da hakan. Hoto: AFP

Abdullahi Musa ya kaɗu sosai da rasa ƴaƴansa uku a wani hari da rundunar sojin Nijeriya ta kai "bisa kuskure: ranar 3 ga watan Disamba, wanda ya faɗa kan wasu taron fararen hula a lokacin da suka taron Maulidi, a garin Tudun Biri da ke Jihar Kaduna.

"Abin da ya fi tsaya min a rai shi ne yadda ƴata ɗaya daga cikin ƴaƴana da suka mutu, take da tsananin son karatu da matuƙar ƙoƙari a makaranta," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Harin "kuskuren" da jirgin yaƙin sojin ya kai kan mutanen ƙauyen wanda ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 90, ya jawo fushi da ɓacin rai a ƙasar, wacce tun daga shekarar 2014 zuwa yanzu kusan fararen hula 400 aka kashe a irin wadannan hare-haren sama "na kuskure".

Shugaba Bola Tinubu ya yi alkawarin gudanar da sahihin bincike a kan lamarin don gano abin da ya jawo harin, wanda rundunar sojin Nijeriya ta ce an kai ne da nufin samun ƴan ta'adda.

Mutane na ta nuna buƙatar ganin an bai wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa diyya, duk da cewa kusan babu wani abu da zai iya sanyaya ran Musa da sauran mutanen da suka rasa masoyansu a harin.

Musa na daga cikin waɗanda suka shirya taron Maulidin na tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu, Baya ga ƴaƴansa uku, akwai kuma wasu danginsa 12 da suka mutu a harin.

Tsohon gyambo

Tun shekara 10 da suka wuce a farkon yaƙi da ƙungiyar Boko Haram da ƙasar ke yi aka fara samun hare-haren kuskure daga lokaci zuwa lokaci.

Kafin harin kuskuren na baya-bayan nan na Kaduna, hukumomin tsaron ƙasar sun sha ɗaukar alhakin kai hare-haren sama "bisa kuskure" a kan fararen hula.

A yayin da aka sha samun saɓani a kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu a irin waɗannan hare-hare tun daga 2014, yawan waɗanda suke mutuwa ɗin ya ci gaba da ƙaruwa a duk lokacin da aka samu akasi haka.

A ranar 6 ga watan Maris din 2014 rundunar sojin Nijeriya ta kai wani hari bisa kuskure wanda ya kashe mutum 10 a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

Sai wanda ya biyo baya a jihar Borno a ranar 17 ga watan Janairun 2017, inda wani hari ta sama ya yi ajalin mutum 53.

Akwai wasu mutum 20 da aka kashe a ranar 28 ga watan Fabrairun 2018 a jihar Borno bisa kuskure.

Kusan shekara ɗaya bayan nan kuma an kashe 11 bisa kuskure a ranar 11 ga watan Afrilun 2019 a jihar Zamfara.

A dai cikin 2019 din a ranar 2 ga watan Yuli an kashe mutum 13 su ma bisa kuskure a jihar Borno.

Har wa yau, a Borno an sake kashe mutum 30 a ranar 25 ga watan Afrilun 2021. Sai a makwabciyar Bornon, wato jihar Yobe inda aka kashe mutum tara su ma bisa kuskure a ranar 16 ga watan Satumban 2021.

Kwanaki kadan bayan nan aka sake kashe mutum 20 a ranar 26 ga watan Satumban 2021 a jihar Borno.

A ranar 20 ga watan Afrilun 2022 an kashe wasu mutum shida a wani hari bisa kuskure a jihar Neja.

Sai mutum biyu da aka kashe a jihar Katsina a ranar 6 ga watan Yulin 2022.

Mutum 60 sun mutu a jihar Zamfara sanadin wani hari da sojin Nijeriya suka kai bisa kuskure a ranar 17 ga watan Disambar 2022.

Wani iftila'in ya sake faruwa a ranar 24 ga watan Janairu, wani hari ta sama ya yi sanadin mutuwar mutum 18 a jihar Neja.

Washe garin ranar kuma wato 25 ga watan Janairu mutum 28 suka mutu a jihar Nasarawa sanadin wani hari da rundunar sojin Nijeriya ta kai bisa kuskure.

Sai na ranar 5 ga watan Maris din bana, wanda harin rundunar sojin kasar ya kashe mutum uku bisa kuskure a jihar Kaduna. Sannan a ranar 18 ga watan Agustan da ya wuce aka sake kai wani harin da ya kashe mutum daya a jihar Neja.

Neman mafaka

To me ya kamata hukumomi su yi don hana faruwar irin waɗannan hare-hare a gaba?

Duk da cewa an samu ci gaba sosai a tsarin magance rashin tsaro a ƙasar, akwai buƙatar hukumomin tsaro su inganta aikinsu, kamar yadda Dr Kabiru ya shaida wa TRT Afrika.

Duk da cewa rundunar sojin ta bayar da haƙuri kan wannan lamari na baya da ya faru, inda har hafsan rundunar sojin ƙasa ta Nijeriya Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya je ƙauyen Tudun Biri don ta'aziyya, masu sharhi na ganin akwai buƙatar rundunar ta yi wa ƴan ƙasa bayani kan sahihan hanyoyin da suka kamata su bi don kauce wa irin waɗannan hare-hare na kuskure.

Dr Kabiru Adamu, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro, ya yi amannar cewa dole Majalisar Dokokin Nijeriya ta tabbatar da cewa ta sa ido don ganin an daina samun afkuwar hare-haren kuskure daga ɓangaren hukumomin tsaro, tare da gano bakin zaren matsalar.

"Duk da cewa an samu ci gaba sosai a tsarin magance rashin tsaro a ƙasar, akwai buƙatar hukumomin tsaro su inganta aikinsu, kamar yadda Dr Kabiru ya shaida wa TRT Afrika.

Ya ce dole kuma hukumomin tsaro su koyi dabarun yaƙi da ƴan bindigar da ke sajewa da fararen hula a lokuta da dama, inda ya ce akwai lokutan da ba a buƙatar amfani da jirgin yaƙi wajen yaƙar su.

Dr Kabiru ya bayar da shawarar cewa ya kamata hukumomin tsaron su dinga la'akari da dDuk wata na’ura da za a mallaka a nan gaba don yaƙi da matsalar tsaro, ta yadda za ta kasance tana cikin tsari, kuma a dinga duba wadda za ta dace da yanayin kasar.

TRT Afrika