Ambaliyar ruwa ta afku a watan Mayu a Gabashin Afirka tare da tagayyara dubunnan daruruwan mutane. Hoto / Reuters

Daga Firmain Eric Mbadinga

Fusatar yanayi, salon maganar da ake amfani da shi wajen bayyana sakamakon ayyukan ɗan'adam da ke yin mummunan tasiri kan duniya, ta bayyana a baya-bayan nan ta hanyar afkuwar ibtila'o'i - daga ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a Afirka da suka janyo mutuwa ko raba dubban mutane da matsugunansu, zuwa ambaliyar ruwan da ta afku a Dubai tare da samun ruwan saman watanni 18 a awanni 24.

Kenya, Tanzania, Burundi, Rwanda, Somalia da Ethiopia duk sun fuskanci ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a 'yan watannin nan, inda masana kimiyya ke cewar sauyin yanayi ne babban dalilin da ya janyo afkuwar waɗannan bala'o'i da ake yawan samu.

A lokacin da ambaliyar ruwan ta fara ja da baya, sai mahaukaciyar guguwar Hidaya ta kunna kai gaɓar tekunan Kenya da Tanzania a ranar 4 ga Mayu, tare da janyo mummunar asara a ƙasashen na Gabashin Afirka. Aƙalla rayuka 400 aka rasa tare da janyo asarar dukiyoyi na miliyoyin daloli.

To, mene ne kimiyya ke son yi baya ga rage raɗaɗin da sauyin yanayi ke janyowa - har ma da ƙoƙarin ganin an yi amfani da hakan wajen samun ruwa da makamashi?

Abu ne da kamar ba zai yiwu ba, wannan ne tunanin da masana kimiyya ke yi a lokacin da ibtila'o'i ke afkuwa ɗaya bayan ɗaya a cikin watanni.

Ambaliyar ruwa a Gabashin Afirka ta munana sosai a 'yan shekarun nan kuma an alakanta ta da sauyin yanayi. Hoto / Reuters

Sabbin dabaru

Ƙwararru na alaƙanta mamakon ruwan sama a lokacin da ba na damuna ba a wasu yankunan Kudancin Amurka da nahiyar Afirka da mahaukaciyar guguwar El Nino.

"El Nino na afkuwa a lokacin da ruwan Tekun Pacific ya yi ɗumi sannan kuma iska ta fara kaɗawa daga ɓangaren gabas, inda yanayi ke ƙara zafi a ɓangaren duniya daga arewa, tare da daɗuwar ruwan sama a Kudancin Amurka da kudancin Afirka," in ji Dr George Mwaniki, shugaban kula da ingancin iska a WRI Africa.

A yayin da El Nino da sauran 'btila'o'in da ke da alaƙa da sauyin yanayi ke ci gaba da zama babbar barazana ga bil'adama, nazarin kimiyya ya samar da dabarun da za iya amfani da mamakon ruwan sama da tsananin zafi don samar da tsaftataccen ruwa da makamashi.

Waɗannan dabaru za su sa a amfana da yawaitar ruwa da zafin da ake samu, kamar dai yadda wasu suka samar da ruwan sama a yankin Sahara.

Masanan kimiyya sun gamsu cewa irin waɗannan bincike da dabaru na iya bayar da kariya ga illolin da sauyin yanayi ke haifarwa, su kuma kai ga samar da hanyar rarraba arziki a duniya da hanya mafi adalci.

Jovanie Sonie Ndong Songo, masanin gine-gine da tsara birane a ƙasar Gabon, na da ra'ayin cewa dole ne a samar da ingantacciyar hanyar tsara birane a ƙasashen Afirka kafin samar da fasahar amfani da mamakon ruwan sama da tsananin zafi don amfanin ɗan'adam.

Ya faɗa wa TRT Afrika cewa "Baya ga yaƙi da sauyin yanayi, akwai kuma batun amfani da filaye da samar da dabarun kaucewa fuskantar hatsari. Ibtila'o'in baya-bayan nan a Kenya da wasu ƙasashen Afirka sun nuna muhimmancin samar da kyawawan magudanan ruwa da tsarin tunkarar matsalolin gaggawa."

"Yana da muhimmanci a ƙirƙira tare da tsara sabbin hanyoyi da za su dinga riƙe ruwan sama da wanda ba na sama ba a waje guda."

Rabin jama'ar Zimbabwe za su fuskanci samar da abinci a karshen wannan shekarare, kamar yadda jami'an kasar suka bayyana. Hoto / AFP

Dabarun kimiyya masu yawa

Dabarar da Jovanie ya kawo, wadda ake kira da madatsar mamakon ruwan sama, ta yi nasara sosai a ƙasashe irin su Canada. Bayan ambaliyar ruwan 2011 da Tafkunan Champlan da Richelieu suka janyo, wani bincike ya bayar da shawarar cire dukkan katangun da ake da su.

Charlene Mouboulou, 'yar jarida kuma injiniyar kula da muhalli, ta bayar da shawarar cewa ƙasashe za su iya ƙirƙirar madatsun ruwa don riƙe ruwan, ko su ƙirƙiri tafkunan da babu su, duba da yanayin yadda ƙasa da yankin suke, domin amfani da ruwan nasu.

"Za a iya amfani da ruwan da ke zuwa daga waɗannan madatsun don gine-gine, ayyukan jama'a, noma da kiwon kifi, ko ma a gidaje. Duk waɗannan ɓangarori na buƙatar ruwa sosai," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Hassan Chouaouta, abokin aikinta daga Maroko kuma Shugaban Cibiyar Ci gaba Mai Ɗorewa, ya ce za a iya amfani da duk wani yawaitar gangarowar ruwa da madatsu don samar da makamashin lantarki.

"Za mu iya kawo ƙarshen wannan matsala. Na yi amanna cewa garuruwa na buƙatar kayan more rayuwa da za su magance afkuwar wani ibtila'i, amma mafi muhimmanci shi ne a samu damar kawar da ambaliyar ruwa zuwa tafkuna da wuraren da za a iya ajiye su ba tare da wata matsala ba," in ji Chouaouta.

"Za mu iya samar da lantarki daga ruwa, mu yi amfani da wannan ibtila'i don ci gabanmu."

Kafin ambaliyar ruwa, Somaliya ta shaida mummunan fari a shekaru 40. Hoto / Reuters

Amfana da tsananin zafi

Kafin ambaliyar ruwan baya bayan nan, watanni shida na biyu na 2023 sun yi fama da ƙaruwar zafi a yanayin duniya, wanda ke janyo fari a wasu yankunan da wutar daji a wasu.

A jihar California ta Amurka, zafi ya taɓa kai wa 54°C, wanda ke nufin za a iya soya ƙwai a kan kwalta. Tsananin zafin ya kuma janyo asarar rayuka da dama.

A 2020, a lokacin da tsanantar zafin ya kai maƙura, Dr Mikael Philippe na Ofishin masu Bincike Kan Yanayi a Faransa na shirin samar da cibiyar samar da makamashi daga sararin duniya a matsayin hanyar sanyaya gidaje.

Dr Philippe ya bayyana fasahar samar da makamashi daga sararin duniya a matsayin "kimiyyar da ke nazari kan zafin da duniya ke ƙunshe da shi da kuma fasahar bayar da damar amfana da zafin".

Mouboulou ya bayar da shawarar amfani da muhimmin sauyi zuwa ga fasahar amfani da hasken rana. "Za mu iya amfani da wannan makamashi don faɗaɗa ayyukan noma. Wasu yankunan ba za su iya samar da wasu kayan amfanin gona ba saboda yanayinsu," in ji ta.

A yankunan da ba sa samun ruwan sama sosai, ana amfani da dabarar narka gajimare don kawo ruwa daga yankunan da suke da shi sosai.

A shekarar 1948 ne ɗan ƙasar Amurka Charles Mallory Hatfield ya ƙirƙiri wannan fasaha tare da ba ta sunan "mai yin ruwan sama". Ana zuba wani irin sinadari na aerosol da ɓaraguzan ƙanƙara a kan gajimaren da suke komawa su zama ruwa. Dubai na amfani da wannan fasaha tsawon shekaru.

TRT Afrika