Wasu da dama sun shafe fuskarsu da fenti a yayin bikin. Hoto: AA

Daga Charles Mgbolu

Senegal ta sake yin bikin mabambantan al'aduna kasar wanda ake yi duk shekara a Dakar, wanda ake yi da nufin bunkasa kade-kade da raye-raye da adon suturu na 'yan asalin kasar Senegal.

An yi kade-kade da raye-raye. Hoto AA

Wannan shekarar ita ce karo na hudu. An gudanar da shi ne a ƙarshen mako, inda aka yi raye-raye da waƙoƙin ‘yan ƙabilar “Lebu” da ke zaune a gundumar Yoff da ke Dakar babban birnin kasar.

An gudanar da wasanni daban-daban a wajen bikin al'adar na shekara-shekara na Dakar. Hoto AA

Wadanda aka yi da daddare inda aka haske sansanin taron da fitilu da suka haska fuskokin masu rawa a daidai lokacin da ake buga ganguna da wakokin da ake rerawa a yaren Lebu Wolof na yankin, ya matukar kayatarwa.

An yi baje kolin tufafin gargajiya a wajen taron. Hoto AA

An kuma yi faretin nuna tufafin gargajiya kala-kala a taron. Baƙi sun sami damar ɗanɗana nau'ukan abincin gargajiya da kuma kallon nunin fasaha da zayyana.

An gudanar da bikin raye-rayen na kabilar Lebu a Dakar. Hoto AA

Bikin dai wani muhimmin al'amari ne na yawon bude ido ga wannan kasa ta yammacin Afirka, inda dubban maziyarta daga ciki da wajen kasar ke halarta duk shekara.

Gasar kamun kifi na daya daga cikin manyan abubuwan da ake yi a yayin bikin. Hoton AA

Da yake Lebu al'umma ce ta masunta, an gudanar da gasar tseren kwale-kwale na kamun kifi da ake kira Pirogue a gabar Yoff na Tekun Atlantika, a matsayin wani ɓangare na bikin.

TRT Afrika