An fara nuna fim din "Tsakanin Paya da Koulou" a birnin Dakar na kasara Senegal. Hoto: Dramane Minta

Daga Daouda Sow

Shirin talabijin mai dogon zango na kananan yara ya kawo labarin wasu yara guda biyu ‘yan uwan juna, wato “Paya” da kuma “Koulou".

Fim ne da ya kawo wa mai ba da umarni, Darakta Dramane Minta, kyaututtuka har guda biyu, bayan fitowar shirin a birnin Dakar na kasar Senegal.

An yi fim din ne cikin harshen Faransanci inda aka kaddamar da shi da sunansa na Faransanci, wato “Entre Paya et Koulou’’, wanda ke nufin “Tsakanin Paya da Koulou" a Hausa.

Fim din mai dogon zango na zane ne mai motsi, kuma an raba shi zuwa kashi 10, inda aka ba da labarin wasu ‘yan uwa guda biyu makusanta, amma masu yawan husuma tsakaninsu.

An zabi silimar Pathe don gabatar da fim din. Mahalartan da suka halarci bikin fara nuna fim din sun hada da taurarin fim, da mawaka, da matasa da ma iyaye da suka zo da yaransu.

An nuna fim din ne a dakin kallo na Room 7, inda masu kallo suka kalli kashi 10 na fim din, kuma abin ya kayatar da su.

Fim din ya nuna duka kaloli da kamannin Afirka, daga ado, da tufafi, da muhalli da kuma salo tsara labari.

Dariya da tararrabi

A tattaunawarsa da TRT Afirka, daraktan fim din Dramane Minta, ya ce, "Ka san fim din zane mai motsi wani fagen fim ne da ba a shige shi sosai ba, inda kowa zai iya shiga kuma ya yi tasiri.

Fim din “Between Paya and Koulou” na darakta Dramane Mintaya ci kyauta a bikin FESPACO. Hoto: Dramane Minta

“Kalubalena shi ne yin fim mai inganci, wanda mu ‘yan Afirka za mu ji dadin kalla. Wannan ce hanyar da za mu nuna Afirkar da muke so duniya ta gano, ba wai yadda wasu suke tunannin Afirka ba.”

An yi ta jin kyakyatawar dariya da annashuwa yayin kallon fim din, kuma tun a farkon fim din yara da manya suka yi ta nuna farin cikinsu

Wannan fim din ya burge Samba Diop, wanda ya zo kallo a silimar. Ya fada wa TRT Afrika cewa, ya zo kallon fim din "Entre Paya et Koulou" ne tare da yaransa mata su biyu. Ya ce shi mai sha’awar kallon fim din zane mai motsi ne.

A zahiri ma, yana cikin masu kallon da suka yi ta bibiyar zango-zango na fim din, sanda darakta Dramane yana sakin shi a manhajar kallon-koyaushe, ta WIDO.

Shiri na farko a fagensa

“Abin alfahari ne sosai ga WIDO da ta yi aiki tare da matashi kamar Dramane don yin wannan shiri. Fim din zane mai motsi yana da matukar wahalar shiryawa.”

Yara sun samu ilhama a rayuwarsu bayan kallon fim din. Hoto: Dramane Mint

"Wannan wani sabon abu ne garemu, a ce mun shirya fim din zane mai motsi da aka nuna a silima. Wannan ya nuna akwai kafofi a kasar Senegal da suka shirya tallafa wa matasa masu fikira, a kokarin inganta fagen al’adu." In ji Mr. Diop.

A bangaren Ms. Ndiaye, tsohuwar mai aiki tare da Dramane. Ta yi dokin bayyana irin karfin gwiwar daraktan, inda ta ce, "Minta, ka san yadda abin nan ya faro, yanzu ga shi mun ga nasara."

“Amma a ra’ayina, na gano shi tun da wuri, shekaru da yawa baya. Zan iya ce maka saboda irin wannan basirar tasa, zai ci gaba da kayatar da masu kallo. Ina masa fatan alheri a aikinsa na ba da umarnin fim.”

Ms Ndiaye, mai kamfanin dillancin fim din zane mai motsi, ta hada gwiwa da Dramane cikin shekaru masu yawa. A cewarta, irin wannan hadin gwiwa ta janyo mata gamsuwa mai yawa.

Haka nan, shirya fim din na "Between Paya and Koulou" ya bai wa darakta damar tattaro kwararru a harkar da kuma sauran ‘yan wasa, kamar Stanislas Gomez, gwani kan tsara sauti da tace bidiyo.

Ta fada wa TRT Afrika cewa, “Wannan ne karon farko da muka ga irin wannan fim.

Amma a baya, mun taba hada gwiwa da Dramane wajen shirya fim mai gajeran zango, mau suna "Rama da Aisha", wanda lokacin annobar Covid-19 ya taimakawa yara suka fahimci yadda za su wanke hannayensu.”

Daraktan ya sanar da TRT Afrika cewa masu kallo su saurari fitowar wasu karin fina-finan. Hoto: Dramane Minta

Shi ma Othniel Ogoussan, dan shekara 11, ya yi muryar Paya a shirin na "Between Paya and Koulou".

Yaron ya kara da cewa, “ina son aikin yin murya a fim ya zama sana’ata." Wannan shi ne karon farko da na fara yin wannnan aiki.”

A baya dai Dramane Minta ya shirya wasu fina-finan kamar "Rama and Aicha" (2021), da "Coco laye laye" (2019), da "Touche pas" (2015), da "Oh My Mind" (2020). Kuma ya halarci bukukuwan fim da al’adu.

Fim din "Between Paya and Koulou" yana samun farin jini sosai. Ya ci babbar kyautar nan ta FESPACO a shekarar 2023, a Ouagadougou, Burkina Faso. Sannan ya ci gasar bikin Vues d'Afrique a Montreal, Canada.

Dramane Minta ya dauki wadannan kyautuka a matsayin kaimi don ya kara kwazo. Ya ce. "Dole fim din Paya da Koulou ya kara kaimi. Ka san yayin da ka kai wani mataki, ba a tunanin ka yi wani kuskure. Dole ka cimma burin masu kallo da masoya”.

Bayan an saki kashi 10 na farko a silima, da kuma manhajar kallon bidiyo, daraktan yana shirya kashi 20 na fim din "Tsakanin Paya da Koulou". Wannan zai burge masu kallo kuma ya ilmantar da su.

TRT Afrika