Rokiatou Traoré ta fahimci amfanin zogale ne a lokacin da take rayuw aa Turkiyya.  Hoto:

Daga Firmain Eric Mbadinga

Ganyan zogale na tattare da sinadaran vitamin da masu gina jiki, kwayoyin irin bishiyar kuma na dauke da kitse, sinadarin protein da antioxidant, kuma ana amfani da jijiyar bishiyar don magunguna

Bawon kwayoyin na dauke da sinadaran karfafa garkuwar jikin dan adam. Nikakken irin bishiyar na iya rarrabe wa tsakanin ruwa da dattin da ke cikin sa.

Lamari mafi kyau shi ne me? Yadda bishiyar ke girma da sauri, hakan ya sanya take sake zama tushen samar da bishiyu a daji kuma noma ne mai dorewa. Wani karin abu mai muhimmanci shi ne yadda take iya rayuwa a yanayin zafi da karancin ruwan sama kama irin wadanda ake fari a Afirka.

Ko ba don komai ba ma, shin zogale dangin tsirran oleifera ne ko kuma stirrai masu jurewa karancin ruwa, bishiya da yankunan Indiya ke kira da "Bishiya mai mu'ujiza".

A wajen mai sana'ar noman zogale 'yar kasar Mali wato Rakiatou Traore, ta fahimci amfanin zogale shekaru 10 da suka gabata a lokacin da take rayuwa da mijinta da ya rasu a Turkiyya.

'Yar shekara 32 ta fada wa TRT Afirka cewa "Na yi bincike tare da gano cewar zogale na amfanar da muhalli, al'umma da lafiya."

"Ni da mijina muna da niyyar dawo wa gida da wata sana'a da za ta dinga amfanar da tattalin arzikin mata, da kuma tasiri kan muhalli ta hanyar yaki da kwararowar hamada, shuka bishiyu da sauyin yanayi. Sai muka ga zogale kenan."

Noman zogale da Rakiatou ke yi na taimaka wa wajen yaki da kwararowar hamada, karewar dazuka da sauyin yanayi. Hoto: Rakitaou

Sana'a don samun sauyi

Kamfanin Herou Alliance na Rakiatou, wanda ya zama mai habaka "zogale a matsayin hajar tattalin arziki, tsaftace muhalli da tasirin zamantakewa," kuma ta mayar da hankali wajen shuka zogalen tare da amfani da ganyensa wajen abinci da saura kayan inganta lafiya.

"Idan na fito a kowacce rana, ina kallon yadda hamada ke kwarorwa cikin sauri da kuma irin tasirin da take da shi ga muhalli da alfanun al'umma wajen samar da kayayyaki," in ji Rakiatou.

Gudun hijira wani sakamako ne na daban. Ga sh kuma mata na yanke hukuncin gudun hijira zuwa wasu wurare don yin ayyuka, suna barin hamada na lalata gonaki da daduwar zafi a yankunansu.

Rakoiatou ta shaida wa TRT Afirka cewa "An samu raguwar ayyukan gona a wasu yankunan Mali."

Kamfanin hero Alliance na kokarin daidaita kasuwanci da ingantuwar muhalli ta hanyar sake farfado dazuka a yankin Sahel.

Domin inganta aikin nata, Rakiatou da mijinta, wanda ya rasu watannin baya jim kadna bayan kaddamar da shirin, sun zabi yankin Koulikoro, wanda ke da yawan jama'a kimanin 18,000.

Sun yi duba na tsanaki ga kowanne bangare a yayin kaddamar da kamfanin herou Alliance a 2020, tun daga injinan aiki zuwa aikatau da musayar dabaru.

Babban abinda ake tattaunawa da jama'ar yankin na kauye shi ne yadda amfanin zogale ga tattalin arziki da kare muhalli.

"A tsakanin kwararru, muna da wani mai bayar da shawara da ya gina gidansa, ya yi aure a haifar yara a wajen, wanda shi ma yake sayar da zogalen. Horon da yake bayarwa na taimaka wa mata wajen fahimtar tsari da yadda ake noman zogalen a zamanance," in ji Rakiatou.

Herou Alliance na sarrafa zogale ya koma sinadarai, gari, sabulu da suaran kayayyakin amfanin dan adam. Hoto: Rakiatou 

Sana'a mai ɗorewa

Herou Alliance na sarrafa zogale sinadarai, gari, sabulu, mai, kayan kamshi, zuma da abincin jarirai, duk kuma ana sayar da su a yankunan kasar, Afirka da sauran kasashen duniya.

Matan da suka fi yawa wajen aikin sarrafa zogalen sun samu horo kan dabarun noman, kula da su d ama girbewa. A shekarar farko, an shuga bishiyun zogale 5,000 a gona mai girman hekta biyar.

"Ministan kwadago da koyar da sana'o'i na Mali a lokacin da 'yan tawagarsa ne suka albarkaci shuka bishiyun zogalen na farko. Taro ne babba d aaka gudanar a ranar 18 ga Agustan 2020," in ji Rakiatou.

Koma baya ga Rakiatou

A watan Nuwamban wannan shekarar, bayan rasuwar mjinta, Rakiatou ta shiga yanayin dimuwa da ya shafi kasuwancin. Cikin nasara gare ta da sauran ,a'aikatan da ta dauka aiki, 'yan uwa da abokai sun agaza mata wajen farfadowa.

Jim kadan bayan hakan, matashiyar ta farfado sosai ind ata fara aikin habaka sana'ar ta hanyar bayar da horo ga mata.

Rakiatou ta kuma bayyana cewa "Tun da mijina ne ya dauki nauyin dukkan shirin har zuwa lokacin da na rasa shi, sai na zama ba ni da yadda zan ci gaba da tafiyar da aikin. A sannan ne na fara neman tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da Gidauniyar Tony Elumelu."

Dala $2,500 da aka baiwa kungiyar, ya taimaka wa wajen farfadowar Herou Alliance zuwa turba.

Karsashin Rakiatou na yin sana'a da kasuwanci ya samu yaba wa d akauna daga jama'a, mahukunta da kungiyoyin da ba na gwamnati ba. Daga dimbin kyaututtukan da ta samu har da "Green Ambassador for Climate in Africa da "Jarumar Gona" ta Majalisar Dinkin Duniya.

TRT Afrika