Sanarwar da tawagar Sauti Sol ta fitar cewa za su rabu ta jawo muharawa a masana'antar kade-kade a duniya.      

‘’Dukanmu muna bukatar soyayya. Muna bukatar kauna. Kuma yadda kake kallona ina jin abin yana shiga raina…"

Idan ka fadi wadannan kalmomi a ko ina a kan titi a Gabashin Afirka, watakila ma, a ko ina a Afirka wani zai iya ci gaba daga nan, idan ma bai fada cikin wakar ba tsundum.

Wakar, wadda ta samu karbuwa sosai da tawagar maza ta Sauti Sol ta yi kuma suka yi wa take da 'Unconditionally Bae', an kalle ta fiye da sau miliyan 15 a shafin YouTube.

Ana sanya wakar a bayan fage a wani shirin rediyo mai farin jini na kade-kaden Afirka da William Tuva ke gabatarwa a birnin Nairobi a kasar Kenya.

"Tawagar Sauti Sol suna da hazakar kansu saboda yadda kade-kadensu ya hade da su," kamar yadda Tuva ya shaida wa TRT Afrika.

"Na san lokacin da suke tasowa ba kawai lokacin da suke yara ba, hatta lokacin da suka fara kafa tawagar, har zuwa lokacin da suka shahara a fagen kade-kade a Afirka," in ji shi.

An kafa tawagar Afropop ta Sauti Sol ne a birnin Nairobi a shekarar 2005 wadanda suka kafa ta su ne: Bien-Aimé Baraza da Willis Chimano da kuma Savara Mudigi inda suka ja hankalin masoya daga fadin nahiyar.

Sai dai tawagar wadda ta kunshi mutum hudu a watan da ya wuce ta sanar da cewa za ta "tafi hutu har ila masha Allahu" inda ta ce mambobinta sun "zaku su kara yin wasu abubuwa na hazaka kuma kowa yana so ne ya yi hakan shi kadai."

Masoya suna shaukin tawagar

Yawanci a Afirka tawagar mawaka tana tarwatsewa ne bayan samun takaddama ko kuma rashin jituwa, a wasu lokutan ma ba a iya fahimtar ainihin abin da ya jawo rabuwar.

Mutum hudu ne suka kafa tawagar mawaka ta Sauti Sol a shekarar 2005. Hoto: Sauti Sol

Game da tawagar Sauti Sol, mambobinta za su ci gaba da sana'o'in da suke so bisa cin gashin kansu, rabuwarsu ba ta nufin kawo karshen alakarsu da juna.

Faduwar wata tawagar ta kan jawo tashin wata tawagar a bangaren nishadi.

Wata mai sharhi kan kade-kade da harkokin nishadi Anyiko Owoko ta yi amannar cewa a ko da yaushe wata tawagar ta sake tasowa, kamar yadda ta ce, nahiyar tana bukatar su.

"Bayan wasu tawagogi da suka yi suna nan da can, babu wasu tawagogi da yawa da za ka iya kira," in ji ta.

"Bangaren kade-kade a shirye yake kuma za a samu ci gaba idan aka samu karin tawagogi. Ban taba ganin wata tawaga da ta taso da za a ce kanta ba a hade yake ba," in ji Owoko.

A tsawon shekaru, tawagogi iri-iri sun taso a fadin nahiyar sai dai kuma suna bacewa cikin sauri, inda suke barin masoyansu da shaukin ayyukansu.

"Yana da kayatarwa mutum ya rika kaunar tawagar mawaka fiye da daidaikun mawaka. Suna abubuwan kayatarwa da dama da su iya. Suna bayar da salo da dama. Basira iri-iri a dunkule waje daya," in ji Owoko.

Ana danganta Saidi Fella da kafa wata tawagar mawaka maza a Tanzaniya wadda ta yi suna kuma ake kiranta Yamoto.

A baya tawagar mawaka ta Tanzaniya ta Yamoto ta wargaje. Hoto: Yamoto

Tawagar ta wargaje kuma tuni wasu daga cikin mambobinta suka zama manyan mawaka masu cin gashin kansu a Gabashin Afirka.

Saidi ta ce yana da wuya a tawagar mawaka masu jini a jika da basira su ci gaba da kasancewa tare har zuwa lokaci mai tsawo.

"Za ka ga wani mamba yana kokarin ya fi sauran mambobin haskawa," in ji shi. "Wasu ba sa son su ji ra'ayin wasu. Suna so su rika tafiyar da tawagar kuma su rika tafiyar da tawagar su kadai. Hakan ba zai yiwu ba a irin wadannan tawagogin."

Tawaga kamar aure ne

Sai dai manaja Owoko ta ce a wasu lokuta bambance-bambancen su ne suka bunkasa tawagar, kawai ana bukatar a fahimci hanyar da tawagar za ta amfana da basirar kowa.

"Wani zai iya zama kwararren mai rubuta waka ko kwalliya ko kuma harkokin gudanarwa da kasuwanci. Kana bukatar gano basirar kowa da cin amfaninta saboda ta haka ne kowa zai fahimci cewa ana gamsuwa da gudunmuwarsa kuma ana tafiya da shi."

Ali Suleiman ne yana daya daga cikin mutanen da suka kafa tawagar mawakan Afro-pop ta Lafrik a Kenya kuma ya ce aiki tare a matsayin tawaga yana da sauki amma kana bukatar mayar da hankali don dorewar tawagar.

An kafa tawagar Lafrik ne a shekarar 2013 kuma har yanzu suna tare. Hoto: Lafrik

"Abin yana kama da aure. Wasu suna yin aiki wasu kuma ba sa yi. Kana bukatar koyon yadda za ku kasance tare, ku fahimci juna, sai ka yi aiki a kan haka," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

An kafa tawagar Lafrik shekaru tara da suka wuce kuma har yanzu yana nan. Suleiman ya ce tawagar mawaka tana ci gaba da samun farin jini a tsakanin matasa.

"Suna maraba da mu yanzu. Na yi aiki da wasu tawagogi kamar Les Wanyika. Na ga mutane masu mabambantar shekaru suna cika inda muke wasa.

Muna ganin karuwar matasa suna zuwa don su kalli wasanmu," in ji shi, ya ci gaba da cewa " wasanmu ba ya kwantai."

A yawancin wadannan tawagogi suna ganin irin karbuwar da suka samu a wasu kasashe shi ne taka matakin nasararsu.

‘‘Ba mu dade daga dawo daga wasa a Tanzaniya ba wanda muka yi a watan Afrilu. Na yi dadin irin yadda suka karbe mu," in ji Suleiman.

Daya daga cikin wadanda suka kafa tawagar mawaka ta Lafrik, Suleiman, ya ce koyon yadda za a zauna da juna yana da muhimmanci. Hoto Lafrik 

Duk da wadannan kalubale da tawagogi suke fuskanta kade-kade suna ci gaba da bunkasa a Afirka.

Kade-kaden sun wuce gaban Afirka

Bambance-bambancen al'ada da sauti da harshe da kuma na salon tafiyar rayuwa wadannan suna samar da yanayin da basira ke wanzuwa.

Masana kade-kade sun ce ana saran masana'antar za ta ci gaba da bunkasa kuma za ta ba da gudunmuwa wajen bunkasar tattalin arziki da bunkasar basira da kuma fagen nishadi.

Kamar yadda Mai sharhi kan kade-kade da nishadi Owoko ta bayyana cewa yawancin tawagogin suna samun cikas ne saboda rashin kyakkyawan tsarin gudanarwa daga manajoji marasa kwarewa ko wanda ma'aikata suka yi wa yawa.

"Ya kamata tawagogi su dauki masu aikin tafiyar da tawagar daidai ruwa daidai tsaki. Ajiye manajoji da dama ba abu ba ne mai yiwuwa. Kowannensu sai an biya shi kudi, sai ka ga ayarin manajoji suna samun kudi fiye da ainihin mawakan tawagar," in ji ta.

Wasu abubuwa da suka faru a kafafen sada zumunta a kwana-kwanan nan sun nuna cewa kade-kaden Afirka idan aka yi su da kyau za su iya yin kasuwa hatta a wajen nahiyar. Wakoki kamar 'Jerusalema' daga Afirka ta Kudu ta ja hankalin duniya sosai.

Salon Amapiano shi ne ke tashe a duniya yanzu wanda ke da 'masoya 'yan gani kashe ni'.

Owoko ta ce alama ce da ke nuna cewa mutane suna jiran abu na gaba da Afirka za ta yi.

Tawagar Yamoto wacce aka kafa a Tanzaniya tana da farin jini hatta a wajen kasar. Hoto: Yamoto

‘’Lokacin da aka fara salon Amapiano babu wanda ya yi zaton cewa zai hada kan duka nahiyar kamar yadda ya yi. Kuma ya je har gaban Afirka kuma duka duniya ta amfana daga salon," in ji ta.

Ta nuna kwarin gwiwa. "Ban san abin da ke gaba ba amma abu babba na nan take," in ji ta.

Mawaki kuma mai kada jita Suleiman ya yi murmushi yayin da yake tunanin abin da ke tawowa zuwa gaba. Tawagarsa ta Lafrik tana shirye-shiryen wasan da za ta yi na gaba a Kenya, wato a gida kenan.

"Mutane suna so a gauraya musu da na kasashe makwabta. Hakan yana nufin za ka iya bunkasa kuma ka yi wasa a wajen gida," in ji shi.

"Wasu tawagogin suna bata lokaci wajen rangadi a wasu kasashe maimakon cikin kasarsu," a cewar Suleiman.

Karin damarmaki

Kodayake tawagar mawakan Sauti Sol za ta wargaje ne bayan kammala rangadin wasanni a Amurka da Kanada da kuma Turai.

Wasu masu sharhi ba su yarda cewa tawagar za ta tarwatse ba saboda yadda mambobinta suka kwashe lokaci mai tsawo suna tare da kuma cewa babu wata rashin jituwa da aka sani a tsakaninsu.

Sauti Sol sun ce ko bayan sun rabu za su ci gaba da hulda da juna. Hoto: Sauti Sol 

Sai dai DJ Tuva ya ce idan da gaske fitattun mawakan Afro-pop din suka rabu, to lalle hakan zai matukar sosa zuciyar miliyoyin magoya bayansu a fadin Afirka.

Ya ce hakan kuma zai taimakawa tawagogin mawaka masu yasowa wajen samar musu da damarmaki da kuma mawaka da za su "nishadantar" da jama'a

Ya ce a baya akwai tawagogin mawaka da yawa da suka yi sama kuma daga baya suka yi kasa, kuma za a ci gaba da samun wadanda suka yi sama.

"Na yi aiki da tawagogin mawaka da dama. Ba zan iya mantawa da tawagar Yamoto daga Tanzaniya ba, sun samar mana da shahararrun mawaka da suka sauya salon kade-kade na bongo," in ji shi.

Ya ci gaba da cewa "Ina sara wa tawagar mawaka ta H_art daga Kenya, Na mamakin yadda suka kasance a tare duk tsawon wadannan shekaru. Amma na san wasu kari suna nan tafe," in ji shi.

TRT Afrika