The Mosque of Mopti iwill soon be a hundred years old, according to records.

Daga Kudra Maliro

An tsara shi da fasahar salon ginin Sudan, Babban Masallacin Mopti da aka fi sani da Masallacin Komoquel, na da girman sukwayamita 12 zuwa 76.

An gina Masallacin da ke tsakiyar kasar Mali a 1933 da 1935. Ya maye gurbin Masallacin da aka fara ginawa a 1908.

Babban Masallacin Mopti na cikin mummunan yanayi a lokacinda Asusun Raya Al'adu na Aga Khan Trust ya farfado da shi.

Tsawon shekaru, Masallacin ya wanzu tare da zama kyam, madalla ga al'ummun yankin da suka kula da shi ta hanyar yi masa yabe da kasa da robar shinkafa. A kowace shekara, mutane da dama daga garin Mopti na haduwa tare da yi wa Masallacin kwaskwarima da sabon tabo.

Amadou Ba, mai shekara kimanin 45, ya kasance yana shiga aikin kwaskwarima ga Masallacin tun yana matashi.

Masallacin Mopti na samun gyara da kwaskwarima kowace shekara

Al'ada

"Kakana ne ya fara kawo ni na shiga wannan aiki a karon farko. A lokacin ina dan shekara takwas. Mun karanta Alkur'ani Mai Tsarki kuma an yabe Masallacin da tabo gaba daya." Amadou Ba ya shaida wa TRT Afirka.

Kamar sauran mutanen Mopti, Malam Ba ya yi tafiya mai nisa don shiga wannan aikin, yana mai kara wa da cewar Masallacin ne abin alfaharin al'adar garin.

"Ina rayuwa a Bamako a yanzu amma ban taba gaza zuwa aikin yi wa Masallacin kwaskwarima ba," in ji Ba dan Mopti mai shekara 45.

Masallacin na da tsayin mita 31, fadin mita 17 da tudun mita 15, kuma an gina shi da bulallukan kasa da tare da yi masa yabe da kasar. Yana da bangarori biyu: na farko na kewaye,, inda na biyun kuma shi ne harabarsa.

An zagaye shi da ktanta wadda ke da tsayin mita 2.40 zuwa 2.90. An yi wa rufinsa turaku manya da suka daura da Alkibla.

Yara kanana ma na taka rawa sosai a wajen yi wa Masallacin Mopti kwaskwarima duk shekara.

Sake haduwa da dangi

A wajen Malam Ba, wannan aiki ba wai sake farfado da Masallacin ba ne kawai, yana sake hada 'yan uwa da dangi a waje guda wadanda suke rayuwa a can wata duniya nesa da Mopti.

Masallacin na Komoquel na karbar masu ibada mafi yawa a lokacin Sallah, musamman ma lokacin Sallar Juma'a.

Wannan tsari da ke hada mutane waje guda ya sanya wannan waje na addini rike kambi da muhimmancinsa a yanayin zamantakewa.

Amadou N'idaye, wani mai fada a ji a yankin, na da ra'ayin cewa tare da wannan al'ada da ake yi duk shekara ta farfado da Mopti, ginin zai ci gaba da zama wata alama ta alfahari.

Alkaluman Ma'aikatar Harkokin Addinai da Ibada ta ce, Musulmai na d ayawan kaso 95 na jama'ar Mali. Masallacin na da muhimanci ta fuskar tarihi, fasahar gini al'adu da imani, kuma na jan hankalin 'yan yawon bud eido sosai.

Malam N'diaye ya karkare da cewa "Ina fatan cewa wannan al'ada za ci gaba har zuwa al'ummu masu zuwa.... Bari mu yi fatan cewa jikokina da jikokin jikokina z asu shiga wannan aiki na farfado da Masallacin."

TRT Afrika