Mawakan Nijeriya sun samu riba sosai tare da kamfanonin sayar da wakoki.

Daga Charles Mgbolu

Al'adar kade-kade da raye-rayen zamani na kara habaka da samun karbuwa a duniya inda masu yin ta ke samu nasarar lashe kambi, suna zaga duniya da jin dadin rayuwa.

Mawakan Nijeriya sun samu riba sosai tare da kamfanonin sayar da wakoki, yayin da suke kuma hada kadai da sanannun mawakan kasa da kasa.

Amma nasararsu a duniya a yanzu ta zama abun takaddama a kai a Nijeriya, inda masu shirya casu da mahalarta ke zargin su da yaudara, saboda yadda suke cewa sai an biya su a dala don yin casu a cikin gida Nijeriya.

Batun da ake takaddama a kansa na da fasali biyu: Na farko, tattalin arzikin Nijeriya na cikin tsaka mai wuya.

Na biyu kuma shi ne magoya bayan na jin cewa ya kamata casu a cikin gida Nijeriya ya zama wata dama ga mawakan wajen ramakon alheri ga magoya bayansu da suka dade tare da su tsawon shekaru.

Nasarar samun kudade

Abun tunanin a nan shi ne mawakan sun riga sun yi kudi saboda suna da shuhura da suka yi a kasashen waje.

Mai jagorantar gudanar casu Oladotun Ojuolape Kayode da aka fi sani da Dotun, ya sake tayar da hazo kan yadda nacewa sai an biya kudi da dala yake killace mawakan daga mago bayansu a cikin gida Nijeriya.

"A yanzu kuna cajin mutanenku da dalar Amurka. Kun manta da budewa da fadada kusancin da wakokinku ke ba ku da al'ummarku. Abu ne na ban mamaki da ta'ajibi." in ji shi, a wani rubutu da ya yi a shafin X.

Wannan abu da ya rubuta ya janyo mayar da martani da dama daga magoya bayan mawaka, wadanda suka bayyana rashin jin dadinsu kan wannan abu sabo.

Wani mai goyon bayan mawaka da ke da sunan @gbana_producer a shafin na X ya tunatar da mawaka cewar suna dogara ne kan 'yan Nijeriya d ake sauraren su kafin su yi shuhura a san su a duniya.

'Daukakar farko'

"Mawakan zamani a yau da z asu samu daukaka tare da 'yan Nijeriya sannan su isa ga fagen kasa da kasa, saboda 'yan kasashen waje na biyan su da yawa, sai suka fara yin yanga ga 'yan Nijeriya da suka ba su damar samun daukaka tun farko." Ya rubuta a shafin X

"Sun ma daina gudanar da casu a nan," in ji wani mai amfani da shafin X.

Dotun na da amsar wannan.

"Lamarin ya fara ne shekaru biyu da suka gabata. Yanzu ya fi munana. Kamfanunnuka sun soke bukin karshen shekara da suke yi; masu shirya casu ba za su iya biya ba har sai dai idan kudin sata ne kuma ba za ka tsammaci riba daga kudin da ka kashe ba."

"Ba za ka ga casun da ya kai darajar kudin da ka biya ba. Mawaka da masu shirya casu ku daure ku gyara farashinku na sayar da kati.

"Lokaci ne na a dafa a wanke. Muna godiya ga mawakanmu ma basira saboda kirki da tsadar su. Za mu rera wakokinku a madadinku," in ji shi.

Sanannen mai gabatar da shirye-shiryen rediyon na cikin wadanda aka rawaito suna cewa ai kowa da ke masana'antar na da laifi irin nasa, jagororin casu da masu gabatar da shiri a rediyo ma na cajin mawaka su biya su da dalar Amurka kafin su yada wakokinsu a rediyo.

Sai dai kuma Dotun ya musanta zargin akan su amma kuma ya yarda da cewa matsalar cajin dala babbar matsala ce da ke damun masana'antar kade-kade da raye-raye ta Nijeriya.

TRT Afrika