Ocloo na amfani da waka wajen magance damuwar yaran da ke da matsalar magana da masu fama da cutar killace kai/Photo TRT Afrika

Daga Charles Mgbolu

Da wata tattausar murya mai fita jefi-jefi a daidai lokacin da yatsunta suke kada jitarta, mawakiya kuma marubuciyar kalaman jinyar nan ‘yar Ghana, Mawuyrami Ocloo ta rika raira wasu baitoci da harshen Twi.

Harshen Twi yana daya ne daga cikin kabilun birnin Accra na kasar, a gaban wasu kananan yara masu shekara kasa da 10.

Yaran, wadanda suna zauna ne a zagaye da ita sun bambamta a yanayinsu. Wasu sun yi zuru-zuru, suna tsimayin lokacin da za su fara amshi.

Wasu kuma suna zaune gum ne ba tare da mayar da hankali kan abin da ake ciki ba, amma suna ta kallon sauran yaran wadanda murmushinsu yake kai wa ga sauran.

“Wadanda ba sa maganar sababbin zuwa ne. Su ma din nan gaba kadan za su fara jin dadin wakar su fara amshi,” in ji mawakiyar wadda ta koyi waka a Amurka.

Wannan ajin wakar mai daukar sa’a daya an fara shi ne sama da shekara bakwai da suka gabata.

Ocloo tana amfani da waka wajen magance damuwar yaran da suke da matsalar magana, musamman masu fama da cutar killace kai.

“Na fara waka ne a matsayin mawakiyar yara a Cocinmu na garinmu, sannan na taso na ga yadda waka ke matukar sauya tunanin mutane.

Wannan ya sa na fara tambaya, ‘Me kuma waka za ta yi sama da wannan”,” in ji Ocloo a tattaunawarta da TRT Afirka

"Wannan tambaya ce da ta dade da maimaituwa a zuciyata. Ina sakandire sai na fara bincike a kan amfani da waka wajen yin jiyar marasa lafiya, inda bincikena ya kai ni ga abubuwan da suka sauya rayuwata.

Sai na fahimci cewa na gano amsoshin da nake bukata. Burina shi ne wakokina su kasance ba wakoki ba ne kawai na nishadi. So nake wakokina su zama waraka.”

Bayan kammala sakandire, sai Ocloo ta tafi kasar waje inda ta halarci jami’a a Amurka. Bayan shekara hudu ta dawo da digiri a wakokin waraka.

Mece ce cutar killace kai?

Kamar yadda Cibiyar Binciken Cutar Killace kai ta Birtaniya ta bayyana, cuta ce da take bayyana mataki zuwa mataki.

Wasu suna iya magana da kyau kuma suna da basira sosai, amma suna fama da rashin shiga mutane da nuna wasu dabi’u na daban.

Yanzu aikin Ocloo ya sa an fara neman ta don yin aiki a asibitocin yara da makarantu da asibitocin Ghana/Photo TRT Afirka

Wasu suna fama da matsalar magana da mutuwar gabbai masu muhimmanci da wasu dabi’u na daban, ciki har da yawan fada da damuwa da maimaita abubuwa da sauransu.

Amfani da wakokin waraka wajen magance matsalar magana a wajen masu fama da cututtukan nan ya samu goyon bayan kimiyya.

Kamar yadda wani bincike da aka yi a Jami’ar Auckland a shekarar 2012, kadawar sautin da aka saba da ita, na habaka hanyoyin tunani da natsuwa a kwakwalwa.

Masu binciken sun kuma gano cewa tunani da rike abubuwa a kwakwalwa duk za su iya karuwa saboda sauraron wakoki.

Cibiyar Kwakwalwa ta American Institute for Neurological Function ta bayyana a shafinta na yanar gizo cewa wakokin baka suna taimakawa wajen taimakon sake koyar da magana.

Waka za ta iya tamakon koyon magana domin tana amfani da bangaren kwakwalwa daya magana.

Sautin wakar na taimakawa wajen fito da magana da hada abubuwan da ake bukata domin a yi maganar.

“Ohimiba yaro ne da ya taso da matsalar magana. Yana i’ina ne,” in ji Vero Osei-Atwenebona, mahaifiyar yaron dan shekara 10.

“Kusan shekara biyu, Ohiniba ba ya magana da kyau. Don haka a matsayinmu na iyaye, sai muka je asibiti bangaren kunne da harshe da makogoro, inda muka yi tunanin akwai matsala a kunnensa muka yi ta fadi-tashi.

"Da muka ga Mis Ocloo a makarantarsu, sai muka yanke shawarar mu same ta domin ganin ko wakar za ta taimaka.”

Dokta Olugbenga Owoeye, wanda kwararren likitan kwakwalwa ne a Jihar Legas, ya yi bayanin cewa mawakin waraka yana fara duba yadda girman matsalar take ne kafin dora shi a hanyar waraka da ta dace.

“Abin da mawakin waraka yake fara yi shi ne duba shekara da matsayin maganar da yaron yake,” in ji Dokta Owoeye.

“Sai su kwatanta yanayin maganar da matakin maganar da ya kamata a ce mai shekaru irin wannan yana yi. Idan maganar ba ta kai yadda ake bukata, sai su faro daga farko.

"Daga sauti da haruffa zuwa kalmomi sannan zuwa jera magana. Wannan zai iya daukar lokaci, amma suna samun nasara.”

A wajen mawakin waraka da daliban, suna yawan amfani da kalmomin “uuuh”da “aaah” a wakokinsu.

“Muna amfani da tashin sauti masu haruffa masu saukin kamawa wajen yara. Muna hada su da kida domin su ingantu.

"Wannan kadai yana jawo hankalin har da yaran da suke da matsananciyar cutar su fara bude bakinsu sannan kalmomin su fara shiga zuciyarsu...sannan su furta da bakinsu,” in ji Ocloo.

Yara masu fama da cutar a Afirka

Kungiyar Lafiya ta Duniya WHO ta ce a cikin yara 160 daya na fama da wannan cutar a duniya.

Ba a samu wannan kididdigar ba game da Afirka, amma a Ghana, Cibiyar Koya da Taimakon Kananan Yara ta ce kashi 38.7 na yara masu ’yan kasa da shekara 14 suna fama da cutar.

Ocloo ta ce tana jin dadin yadda take kokarin cike gibin da ke akwai wajen samar da rayuwa mai inganci ga yaran/Photo TRT Afrika

A Najeriya, wani binciken Tsangayar Kimiyyar Lafiya ta Jami’ar Legas ya bayyana cewa yaro daya a cikin 125 zuwa 150 yana fama da cutar. Wannan ke nufin kusan yara 600,000 ne suke fama da cutar a Najeriya.

Ocloo ta ce tana jin dadin yadda take kokarin cike gibin da ke akwai wajen samar da rayuwa mai inganci ga yaran.

“Akwai dadi ka ga rayuwar yaro ta daidaita. Iyaye suna shiga damuwa sannan bangaren ilimi a nan Ghana bai yi tanadi na musamman ba ga irin wadannan yaran.

"Wannan ne ya sa yake farin cikin ganin yadda waka ke ba mu wata dama wajen taimakon yaran da suke fama da wannan cutar.”

Francis Sarpong, mahaifi ne ga wani yaro dan shekara 12 da ke fama da cutar killace kai, ya ce ya ga cigaban da yaronsa ya samu ba a magana ba kadai, har ma mu’amalarsa.

“Suna koyon tafiya da magana, suna cewa ‘daga hannunka ka yi magana’. Wannan wasu abubuwa ne da ba za ka gansu ba a sauran makarantu.”

Yanzu aikin Ocloo ya sa an fara nemata domin ta yi aiki asibitocin yara a makarantu da asitocin Ghana.

A Disamban bara, ta zama mawakiyar waraka ta farko a Cibiyar Lafiyar Jami’ar Ghana. “Waka hanyar ce ta gyara ruhi. Ina farin cikin ganin tasirin da wakokina suke yi,” in ji Ocloo.

TRT Afrika