Afirka na fatan habaka tattalin arzikin mutane biliyan 1.3 da kasuwanci mara haraji. Hoto: Wasu

Daga Johnson Kanamugire

Ya zuwa yanzu, ayyana 2023 a matsayin shekarar Yarjejeniyar Saukaka Kasuwanci ta Nahiyar Afirka da Tarayyar Afirka ta yi ta wayar da kan al'umma da bayar da damar musayar ra'ayoyi kan abubuwan da suke bukatar kulawar sosai, don gaggauta tabbatar da gudanar da kasuwanci a saukake a tsakanin kasashen nahiyar.

Tattaunawa ce ake yi a lokacin da ya dace, duba da yadda ta zo bayan Afirka ta cika shekara biyu da fara shiga da fitar da kayayyaki zuwa kasashen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da kasuwanci a saukake a Afirka.

Yarjejeniyar AfCFTA na sa ran kawo karshen nakasun da kasuwannin Afirka suke fama da shi, inda za a bude kofar kasuwancin mutum biliyan 1.3 idan har yarjejeniyar ta fara aiki.

Amma kuma, a yayin da kasuwanci ke ci gaba da habaka sosai, 'yan kasuwa daga kasashe takwas suna musayar kayayyaki karkashin yarjejeniyar, tambayar kudin da za a dinga gudanar da kasuwancin na ci gaba da kai komo a zukatar jama'a.

Cajin aika kudade

Misali, tare da kasashe da dama da ake sa ran za su shiga yarjejeniyar, su kuma habaka yawan ta'ammulin kudade da ake yi, ya nuna karara cewa kudaden da ake samu daga kasuwancin za su yi ta tafiya ga kokarin aika kudade.

Rashin kudin bai daya a nahiyar, ko kuma wani tsarin biyan kudade da zai bai wa kowa damar sayayya da kudin kasarsa, ya sanya sai 'yan kasuwa sun sayi wani kudin na daban.

Alkaluman bankin Shga da Fitar da Kayayyaki na Afirka sun nuna amfani da kudi na uku na janyo wa Afirka asarar dala biliyan biyar a shekara. Hoto: Rueters

Yin hakan zai dauki lokaci da cin kudade idan aka yi duba zuwa ga cajin aika kudade ko kudaden da ake samu ta hanyar amfani da bankunan tsakiya da suke wajen nahiyar.

Ya zuwa yanzu, kasashen Afirka tara ne kawai suka yi kokarin raba jama'arsu daga wannan asara bayan sun rungumi tsarin Biyan Kudade na Afirka Baki Daya (PAPSS), tsarin da Bankin Shiga da Fitar da Kayayyaki na Afirka ya samar don saukaka aika kudade tsakanin kasashen nahiyar.

Aika kayayyaki

Jami'an Tarayyar Afirka da akalla kasashe tara ne suka rungumi wannan tsarin, wanda idan duk nahiyar ta karbe shi, zai bayar da dama ga dan kasar Rwanda ya sayi kayan gini daga Nijeriya ya biya kudinsa da Faransa na Rwanda, shi kuma mai sayarwa a Nijeriya ya karbi kudinsa a Naira kwatancin kayan da ya sayar.

Irin hakan ne dai zai faru idan misali aka ce dan kasuwar Kenya ya aika da tufafi ko ganyen shayi ga wanda ya saya a Ghana. Dan Ghanan zai biya da Cedi, shi kuma wanda ya sayar a Kenya zai karbi sulai a asusunsa na banki.

Tsarin na son bayar da dama amfani da kudaden kasashen nahiyar 42 da ake amfani da su, kamar yadda jami'an da ke jagorantar shirin suka sanar.

Sai dai kuma, duk da a watan Janairun bara aka kaddamar da shirin a hukumance, nasarar PAPSS za ta dogara ne kan saurin da gwamnatoci suka yi wajen karbar tsarin tare da shigar da shi tsarin bankunansu.

Ba abu ne na kai tsaye ba, kuma ba za a dakatar da gudanar da kasuwanci ba.

Tsadar gudanar da kasuwanci

Lokaci ya yi da kasashen Afirka za su farfado da hadin kansu na ta'ammali da kudade, wanda aka fara tun 1991, da ke da tsarin tabbatar da kudin bai daya a dukkan Afirka a 2021, kamar yadda yarjejeniyar Abuja ta tanada.

Kungiyoyin kasashe na yankunan nahiyar irin su EAC da SADC da COMESA da ECOWAS da wasun su na ta kokarin yin wannan abu kan hadewar bangarorin kwastan da kai komo cikin sauki.

Wani abun da ke durkusar da kokarin 'yan kasuwa shi ne yadda sai sun sayi kudi na uku sannan su je sayi hajar da suke so. Hoto: OTHERS

Wasu daga cikin kalubalen da ke fuskantar wannan yunkuri na kudaden kasuwanci a saukake a Afirka tsakanin kasashen nahiyar daban-daban sun hada da canjin kudin da yadda 'yan kasuwar kasashen ba sa son sayar da kayansu da kudaden cikin gida.

Wannan, na kira ga hade dukkan kudaden waje guda su zama kudi daya tilo wanda za a dinga kula da darajarsa ta hanyar kungiyar kasashen da babban bankin da za su kafa.

Kudin bai-daya

Bankin Fita da Shigar da Kayayyaki na Afirka (Afreixm) ya bayyana amfani da wani kudi na daban a kasuwancin da ake yi tsakanin kasashen Afirka na janyo wa nahiyar asarar dala biliyan biyar a kowace shekara, kudaden da suke tafiya aljihun 'yan kasuwar da ba a Afirka suke ba.

Wannan na haramta wa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka habaka lantarki, samar da kamfanunnuka da ayyukan yi ga miliyoyin jama'ar nahiyar, inda ake aiki da tsarin kasuwanci da 'yan mulkin mallaka suka dora nahiyar a kai.

Baya ga haka, abun da ke durkusar da kokarin 'yan kasuwa shi ne yadda sai sun sayi kudi na uku sannan su je sayi hajar da suke so a wasu kasashen na Afirka.

Cajin kudaden da ake yi, kamar yadda ake asara yayin da kudade ke hawa da sauka, na takura wa masu sayen kayayyaki da ke zuwa kasuwanni.

A yayin da yarjejeniyar AfCFTA ke samun tagomashi, ya kamata shugabannin Afirka su bayar da muhimmanci ga kudin bai daya, fifikon da ke gaba da sauran duk wasu al'amuransu, kamar irin su kai komo ba tare da tsangwama ba, 'yancin kafa kamfanoni da safarar jiragen sama.

Johnson Kanamugire dan jarida ne da ke kasar rwanda wanda ya kware kan batutuwan a suka shafi al'umma.

Togaciya: Ra'ayin marubicin ba lallai ne ya zama daidai da manufofin yada labarai na TRT Afirka ba.

TRT Afrika