Hare-Haren 11 ga Satumba a Amurka da tasirinsu kan tsaron Afirka

Hare-Haren 11 ga Satumba a Amurka da tasirinsu kan tsaron Afirka

A yau aka cika shekaru 22 da kai hare-haren da suka birkita Amurka da sauya duniya.
Tuna wa da 11 ga Satumba / Hoto: Getty Images

Daga William F.S. Miles

Shekara 22 da suka wuce, ban dade da dawowa Amurka ba daga tafiyar da na yi zuwa kasar Yammacin Afirka da mafi yawancin Amurkawa ba su san ta ko taba jin ta ba ma: Nijar.

A yanzu, tabbas, Nijar ta yi suna - ko kuma zama yadda take, duba da yadda kowa zai iya kallon- juyin mulkin da aka yi a kasar inda sojoji suka kifar da zababbiyar gwamnati, dakarun sun kira kansu da sunan Majalisar Kasa ta Kubutar da Kasa.

Daya daga cikin manyan dalilan da 'yan juyin mulkin suka bayar na kifar da gwamnatin Shugaba Bazoum a Yamai shi ne, yadda shugaban ya kasa yakar ta'addanci a cikin kasar da kan iyakokinta.

Na sake dawo wa Nijar a lokacin da juyin mulkin ya faru, tare da Hukumar Kula da Iyakokin Kasa.

A nahiyar da ta fuskanci juyin mulki da dama tun bayan samun 'yancin kai sama a shekara 60 da suka gabata, juyin mulki biyar na Nijar ba su kadai ba ne.

Masu aikata juyin mulki sun yi amfani da ta'addanci a matsayin dalilinsu, amma kuma akwai gaskiyar magana. Yaya duniya musamman ma Afirka suka sauya tun bayan da 'yan Alqa'eda suka shirya rusa dogayen gine-gine biyu na Cibiyar Kasuwanci ta Duniya wand ake nufin ayyana yaki kan Amurka?

Ba a dauki lokaci mai tsayi ba Amurka ta fara farautar Usama bin Laden da mabiyansa a Afganistan, hakan ya janyo tantamar daga ina ne wadannan 'yan ta'adar za su fito? Ina za su gudu, ina za su buya da sake shirya kansu?

Ma'ajiyar Yuraniyom

Masanin dabarun ayyukan sojin Amurka ya yi hasashen wannan abu zai zama babban batun da Musulman duniya za su sanya a gaba, tare da iyakoki marasa tsaro, gwamnatoci da ba sa aikata katamus, da talauci da ya karade ko'ina.

Har yanzu Amurkawa na nuna jimami a duk ranar tunawa da harin 9/11. Photo: Reuters

Et volla - Yankin Sahel. Hakan ya sanya aka kaddamar da shirin Ci-gaban Yankin Sahel tun 2002,

Kasashen da suke jagorantar shirin, karkashin kulawar Amurka, sun hada da Nijar da Chadi da Mali da Muritaniya, na kokarin yaki da yduwar ta'addanci a yankin da dukkan Yammacin Afirka.

Wannan ne abu na farko da ya sany Nijar zama kan sanya idanuwan Amurka, yayin da Shugaba George W. Bush a 2003 ya bayyana yankin a matsayin matattarar Alqa'eda - maboyar Yuraniyom din da ake hada makaman kare dangin da aka zargi Saddam Hussein da tara wa. Daga karshe an gano wannan duk karya ce.

Amma ko ma meye dai, an riga an yi zalunci: daga yanzu za a fahimci Sahel a matsayin mahada mai muhimmanci ta ta'addanci a duniya, wanda zai bayar da damar girmamar IS da rassan su na Iraki da Siriya ISIL, zuwa na Maghreb (Ansarul Al Sharia) zuwa Yammacin Afirka (ISWA).

Daga baya kuma, shirin na Sahel ya rikide ya koma Hadin Kan Sahara don Yaki da Ta'addanci (TSCTP), wanda yau ya tattara kasashe goma sha biyu na Sahel da Maghreb.

Ko an assasa tushen wadannan kawance sosai, ko kuma sun zama masu biyan bukatun masu hasashe ne, abu ne da za a dauki lokaci ana muhawara a kai, musamman a tsakanin kwararru da masana harkokin soji.

Amma abun lura kuma shi ne, a yanzu ta'addanci ya yi kaura daga gabas ta Tsakiya da kusa da yankin zuwa Yammacin Afirka. Ko suna da alaka ko a'a, yadda aka ki bayar da muhimmanci ga 'yan ta'addar IS da Alqa'eda a Siriya da Iraki, haka ma aka nuna halin ko in kula ga karfin fada a ji da Faransa ke da shi a Yammacin Afirka.

Yiwuwar Amurka ta zama ita kadai

Kyamar Faransa ce ta zama wata manufa ga masu juyin mulki a Burkina Faso, Guinea da Mali - yanzu kuma Nijar inda aka koma mulkin soji da nun kyamar Faransa.

Wannan daya daga cikin maduban alakar Faranda Afirka ne, da ke hada shugabannin da jama'ar tsaffin kasashen da aka yi wa mulkin mallaka.

Amurka na farin ciki game da yiwuwar zama mai maye gurbin Faransa a matsayin babbar mai yaki da ta'addanci a Sahel. Hoto: AFP

Amurka na farin ciki game da yiwuwar zama mai maye gurbin Faransa a matsayin babbar mai yaki da ta'addanci, idan za a yi batun samar da kayan aiki da bayar da shawarwari.

Da ma tuni Faransa ta kwashe sojojinta daga Mali zuwa Njar, a yanzu kuma ake matsa mata lamba da ta bar Nijar din, akwai yiwuwar Amurka ta zama ita kadai a yankin, sai dai idan za ta mika wa Rasha yankin.

Shekara 22 da suka gabata, an kaddamar da 'hari da jiragen sama' da aka shirya shi daga wasu tsaunuka a yankin Tsakiyar Asiya, an girgiza duniya da harin.

Gwamnatoci da nauyi ke kansu - Amurka da Faransa da na Afirka na da alhakin hana sake afkuwar hakan a nan gaba.

Haka kuma, yaki da ta'addanci ba zai zama dalilin kifar da gwamnatin farar-hula ba. Kuma bai kamata ya zama babban kalubale ga mafi yawan kasashen Afirka ba da hana su ci-gaba.

Marubucin wannan makala, WIlliam F.S. Miles, farfesa ne a sashen nazarin kimiyyar siyasa a Jami'ar Northeastern. Tsohon dan sa-kai na samar da zaman lafiya a tsakanin 1977 da 1977 a Nijar, kuma malamin Fulbright a kasar a tsakanin 1983 zuwa 1984, da kuma a 1986, shi ne ya rubuta littafin Hausaland Divided: Colonialism and Independence in Nigeria and Niger da My African Horse Problem

Togaciya: Wannan makala ta kunshi ra'ayin marubucin ne amma ba ra'ayin TRT Afrika ba.

TRT World