Shugaba Erdogan ya hadu da wadanda suka tsira daga girgizar kasa a watan Maris din 2023. Hoto/Others

A lokacin da aka samu gagarumin bala’in da ya fada kasar Turkiyya a watan Fabrairu, inda girgizar kasa ta kashe sama da mutum 50,000, masu sharhi na cikin gida da na waje sun yi ta hasashen cewa hakan zai iya kawo cikas ga Shugaba Recep Tayyip Erdogan wurin zamansa shugaban kasa a zaben 14 ga watan Mayu.

Sai dai sakamakon zaben da ya fito ya nuna musu kuskurensu. Erdogan da kawayensa na People’s Alliance sun ci zabe sosai a wurare da dama da girigizar kasar ta taba.

Daga cikin wuraren har da lardin Kahramanmaras inda nan girgizar kasar ta fi yi wa illa, da kuma wasu larduna kamar su Malatya da Gaziantep da Osmaniye da Kilis da kuma Hatay.

Cikin larduna 11 da girgizar kasar ta yi wa barna, Erdogan da kuma jam’iyyarsa ta AK Party su ne kan gaba a larduna takwas a zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa inda Kemal Kilicdaroglu wanda shi ne dan takarar shugabancin Turkiyya a Jam’iyyar Nation Alliance da kuma na Jam’iyyar CHP duka suna gaba a Adana da Diyarbakir.

Yankunan da Erdogan ya yi nasara a wuraren da aka yi girgizar kasa

A Hatay, Kilicdaroglu ya dan bayar da tazara kadan a zaben shugaban kasa inda Jam’iyyar AK ta samu kuri’u masu dumbin yawa sama da CHP a zaben ‘yan majalisa, inda ta samu kashi 34 gaba da kashi 28 da jam’iyyar Kilicdaroglu ta samu.

Shugaba Erdogan ya kai ziyarce-ziyarce wuraren da girgizar kasa ta yi wa barna, inda ya yi sauri ya kaddamar da sabbin dubban gine-ginen a madadin wadanda ko dai suka rushe ko kuma suka yi dameji matuka.

Gwamnatin Erdogan ta tsara gina sama da gidaje 650,000 wadanda suka hada da gidajen kauye 143,000 inda girgizar kasar ta yi sanadin rasa rayuka da kuma damejin gidaje.

Gwamnatin Turkiyyar ta yi alkawarin kammala gidaje 319,000 domin bayarwa ga jama’a a cikin shekara guda, inda kuma aka kai gidaje na kwantena dubbai wuraren da girgizar kasar ta rutsa da mutane domin samar musu da matsuguni.

Da duk wadannan abubuwan, kokarin da Ankara ke yi wurin taimaka wa wadanda girgizar kasa ta shafa ya nuna cewa jama’a sun ji dadin hakan idan aka yi da la’akari da yadda Erdogan da kawayen jam’iyyunsa suka samu nasara a lardunan da aka samu mummunar barna ta girgizar kasa.

Bari mu ga yadda wadannan lardunan da girgizar kasa ta yi wa matukar illa suka yi zabe a ranar 14 ga watan Mayu:

Kahramanmaras

Wannan lardin da ke gefen Tekun Bahar Rum yana da sama da mutum miliyan guda, inda gundumominsa Pazarcik da Elbistan suka kasance daya daga cikin wuraren da aka samu girgizar kasa sau biyu masu karfi a ranar 6 ga watan Fabrairu mai karfin maki 7.7 da kuma 7.6.

Kusan kashi 72 cikin 100 na mazauna Kahramanmaras suka zabi Erdogan a zaben shugaban kasa inda kashi 22 cikin 100 suka zabi Kilicdaroglu.

Kuri’un da Erdogan ya samu a Kahramanmaras ya kai kusan wanda ya samu a mahaifarsa Rize, wato kuri’un da ya samu mafi yawa a Turkiyya na 72.79.

A bangaren zaben ‘yan majalisa kuwa, jam’iyyar Erdogan ta AK Party ta taka rawar gani inda ta samu kusan kashi 48 cikin 100 fiye da kashi 16 da CHP ta samu.

Kawar Jam’iyyar AK wato National Movement Party (MHP) ta samu kashi 16, wanda hakan ke nufin ta kamo kason da CHP ta samu a lardin da girigizar kasar ta yi wa illa.

Erdogan ya kai ziyara Kahramanmaras sau da dama inda kuma ya kara jaddadawa a bayanan da ya yi kan cewa mutanen da suka rasa iyalansu da kuma gidajensu ba za a bar su haka ba.

A watan Maris, da kansa Erdogan din ya halarci bikin kaddamar da gidaje 7,353 da kuma gidajen kauyuka 620 a Kahraman maras. Inda daga nan sai aka yi t samun ginin gidaje a fadin lardin.

Adiyaman

Lardin kudu maso gabashi ya kasance lardin da Jam’iyyar AK Party ke da karfi matuka. Kamar Kahramanmaras, lardin Adiyaman shi ma girgizar kasa ta yi masa barna matuka.

Sai dai jama’ar Adiyaman sun ci gaba da yin ruwan kuri’u ga Shugaba Erdogan a zaben shugaban kasa da kashi inda suka bashi kashi 66 cikin 100 na kuri’u. Kilicdaroglu ya iya samun kashi 31 cikin 100 ne kawai.

A zaben ‘yan majalisa, Jam’iyyar AK ta bayar da tazara mai yawa ga CHP, inda ta samu kaso 52 cikin 100 inda CHP din kuma ta samu kaso 19.

Kamar Kahramanmaras, a Adiyaman ma gwamnatin Erdogan ta kaddamar da ginin gidaje.

“Adadin gidajen da za mu gina a Adiyaman za su kai kusan 50,000 haka kuma adadin gidajen kauye za su kai 23,640,” in ji Erdogan a lokacin wani jawabi da ya yi a watan Maris a lardin a yayin kaddamar da ginin gidajen 4,431.

Malatya

Kamar Kahramanmaras da Adiyaman, wannan lardin na gabashin Anatolia wanda girgizar kasa ta yi wa illa na daga cikin wuraren da Jam’iyyar AK Party ke samun kuri’u masu dumbin yawa, kuma hakan bai sauya ba a zaben 14 ga watan Mayu.

Kashi 69.39 na jama’ar da ke Malatya sun zabi Shugaba Erdogan a maimakon Kilicdaroglu mai kaso 27.02 cikin 100 a zaben shugaban kasa. Wannan lardin ya kuma zabi Jam’iyyar AK a maimakon CHP a zaben ‘yan majalisa da tazara mai yawa.

A tsakiyar watan Afrilu, Erdogan ya halarci kaddamar da ginin manyan gidaje a Malatya, inda gwamnatin kasar ta yi niyyar gina sama da gidaje 70,000 da kuma gidajen kauyuka 25,300 ga wadanda suka tsira daga girgizar kasar.

Hatay

Wannan lardin wanda ke kan iyaka kuma yake da tashar ruwa ta Iskenderun na daga cikin lardunan da girgizar kasar ta yi wa barna, inda ta lalata gidaje da dama da kuma wuraren tarihi a babban birnin lardin Antakya.

Duk da cewa magajin garin birnin dan Jam’iyyar CHP ne, an zo kusan kankankan a Hatay, inda Erdogan da Kilicdaroglu suka samu kashi 48 inda Erdogan ya dan dara abokin takarar nasa da kuri’u kadan.

Amma a zaben ‘yan majalisa, Jam’iyyar ta AK ta samu kashi 34 cikin 100 inda CHP ta samu 28 daga mazauna Hatay da girigizar kasa ta yi wa illa.

Sauran larduna

Baya ga wadannan lardunan hudu wadanda su ne girgizar kasar ta fi yi wa illa kamar yadda gwamnatin Turkiyya ta bayyana, Erdogan ya samu kuri’u masu dumbin yawa a Gaziantep (60/35) sai Sanliurfa (62/32) da kuma Osmaniye (62/31) sai Kilis (66/27) da kuma Elazig (67/28), wanda hakan ya sake nuna cewa har yanzu shi ne kan gaba a wadannan lardunan.

A duka wadannan larduna biyar din, Jam’iyyar AK ta ci zabe da tazara mai yawa.

A Adana da Diyarbakir, Kilicdaroglu shi ya ci akasarin kuri’u. Amma jam’iyyar AK ita ce ke gaban CHP a zaben ‘yan majalisa.

TRT World