Kasashen G7 ne mafiya karfin tattalin arziki a duniya/ Hoto: Rueters

Kungiyar bayar da tallafi ta Birtaniya Oxfam ta bayyana cewar kasashe matalauta na bin kasashen duniya bakwai na G7 da suka fi kowa arziki bashin dala tiriliyan 13 na ayyukan taimakon ci gaba da alkawurran magance illolin sauyin yanayi.

Maimakon su mayar da hankali wajen cika alkawurran da suka dauka, amma sai suke neman kasashe matalauta su biya basussukan dala miliyan 232 da aka ba su rance, in ji Oxfam.

Sanarwar da Daraktan Zartarwa na Oxfam, Amitabh Behar ya fitar ta bayyana cewa “Kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki na yawan son bayyana kawunansu a matsayin masu kubutar da kasashe daga kangin talauci.

"Amma abun da suke yi tsagwaron munafurci ne --- suna amfani da wasu dokoki inda ake takurawa kasashen da suka yi wa mulkin mallaka a baya su biya wani bangare”.

Sanarwar ta ce “Dole wannan abu ya dakata. Lokaci ya yi da za a bayyana wa duniya irin yadda munafurcin G7 yake: kokarin kaucewa nauyin da ke kawunansu, sannan su ci gaba da mulkin mallaka ta sabuwar siga ga kasashe.”

Shugabanni bakwai na kasashen G7 na gudanar da taro a garin Hiroshima da ke yammacin Japan.

Akwai yiwuwar su tattauna kan kokarin karfafa tattalin arzikin duniya, tare da magance matsalar hauhawar farashi da suke takura wa kasafin kudin iyalai da gwamnatoci a duniya, musamman ma a kasashe masu tasowa da ke Afirka da Asiya da Latin Amurka.

Oxfam ta bayyana cewa ana gudanar da taron G7 a lokacin da biliyoyin ma’aikata suke fuskantar yanke musu albashi da hauhawar farashin kayan masarufi kamar abinci.

Ta ce “Ana ci gaba da samun karancin cimaka a duniya a karo na biyar a jere, a yayin da samun arziki da yawa da kuma talaucewa ke kara yawa a bangarorin biyu a shekaru 25 da suka gabata.”

Kungiyar ta bukaci kasashe masu arziki da su yafe basussukan da suke bin kasashe matalauta, sannan su kuma samar da dala biliyan 100 duk shekara don taimakon kasashen su magance matsalar sauyin yanayi.

TRT World