Daruruwan mutane sun mutu sakamokon wata mahaukaciyar guguwa a Myanmar

Daruruwan mutane sun mutu sakamokon wata mahaukaciyar guguwa a Myanmar

Sama da mutum 400 ne suka mutu a jihar Rakhine ta kasar Myanmar, yayin da dubbai suka rasa matsugunansu.
Guguwar ta sauka ne a tekun da ke tsakanin gundumar Cox Basar ta Bangaladash da garin Kyakpyu na Myanmar/ Hoto: Reuters

Wata mahaukaciyar guguwa ta yi sanadiyyar mutuwar mutum sama da 400 a jihar Rakhine ta kasar Myanmar.

Guguwar ta sauka ne a tekun da ke tsakanin gundumar Cox Basar ta Bangaladash da garin Kyakpyu na Myanmar, a cewar kungiyar siyasa ta mutanen Rohingya, ARNA.

A sanarwar da Kungiyar ARNA ta fitar a ranar Laraba ta bayyana cewa, kauyukan da ke gabar teku a Sittwe babban birnin jihar Rakhine, sun fuskanci barna mai tarin yawa sannan fiye da mutum 400 wadanda galibinsu Musulmai ne sun mutu, adadin da ake ganin zai iya zarce hakan.

Sannan sama da gida 10,000 ne suka rushe a cewar sanarwar.

Mahauciyar guguwar mai tafe da ruwan sama da ake kira da ‘Cyclone Mocha’ na daga cikin guguwa mafi karfi da yankin ya taba fuskanta, kuma ta yi sanadiyyar hallaka mutane tare barnata dukiyoyi da dama.

Cibiyar hadin gwiwa da ke sa ido kan aukuwar bala’o’i a kasar ta ce guguwar mai karfin gudun da ya kai maki 135 ta shiga gabar Tekun Rakhine mai nisan kilomita 217 cikin sa'a guda.

"A Sittwe, an tabbatar da cewa kimanin 'yan Rohingya 130,000 ne ke tsare a sansanonin 'yan gudun hijira, kwatankwacin adadin da ke sansanonin tun daga 2012. Kuma mafi yawan 'yan sansanin ba a kwashe su ba.

Ambaliyar ruwan sama ta shafe kusan taku 30 na daya daga cikin sansanonin da ke dauke da mutum 380, kamar yadda daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar 'yanta 'yan Rohingya Nay San Lwin, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

A cewar majiyoyi da dama, adadin wadanda suka mutu a dukkan sansanonin da ke Sittwe na iya zarce 400.

Ana ganin saboda katsewar ayyukan wayar hannu da na Intanet a yankin, za a dauki wani lokaci kafin a iya samun ainihin adadin mutanen da suka mutu. Sannan kashi 90% na gine-gine sansanonin gabaki daya sun lalace.

A cewar sanarwar baya-bayan nan da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, karfin guguwar ya haura maki 9-9.5 a kananan yankuna da ke Arakan da kuma gabar Tekun Bangladesh.

Mahaukaciyar guguwar Mocha ta lalata kusan dukkan gidaje da makarantu da masallatai da asibitoci da sauran ababen more rayuwa a Sittwe.

Kazalika ta afka wa garuruwan Ponnagyan da Kyauktaw da Mrauk-U da Myebon da Pauktaw da kuma Rathedaung.

Sanarwar kungiyar ARNA ta yi Allah-wadai da kakkausar murya ga gwamnatin mulkin soji na Myanmar kan abin da ta kira rashin daukar matakin gaggawa na hukumar takaita aukuwar bala’o’i na kasar wajen kokarin ceto rayukan al'umma.

“Yanzu haka mutane na cikin tsananin bukatar ruwan sha da magunguna da matsugunai da kuma abinci, don haka muna kira ga kasashen duniya da kungiyoyi masu zaman kansu da su kawo musu dauki.

Ya kamata gwamnatin sojin kasar ta kyale dukkan hukumomin agaji da masu taimaka wa kowane mabukaci ba tare da wata matsala ba, ba kuma tare da nuna bambanci ba,” inji sanarwar.

TRT World