Shafin X ya gudanar da sauye-sauye da dama a kwanakin baya ciki har da sauya masa suna. Hoto/Reuters

Shugaban kamfanin X wanda aka fi sani da Twitter a baya Elon Musk ya bayyana cewa akwai yiwuwar duka masu amfani da shafin su rinka biyan wasu ‘yan kudade a duk wata.

Musk ya bayyana haka ne a a ranar Litinin a lokacin da yake tattaunawa da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bayan firaiministan ya yi tambaya kan yadda Musk zai magance yadda ake amfani da shafukan bogi wurin tunzura kiyayyar Yahudawa.

Daga nan ne Musk ya ba shi amsa inda ya ce kamfanin zuwa gaba na son a fara biyan kudade kadan kafin a rinka amfani da shi.

Babban dan kasuwan mamallakin kamfanin SpaceX da Tesla ya gudanar da sauye-sauye da dama tun bayan da ya karbi jagorancin Twitter inda ya sayi kamfanin kan sama da dala biliyan 44 a Oktobar bara.

Musk ya kori dubban ma’aikatan kamfanin da kuma fito da wani sabon tsarin biyan kudi, da kuma mayar da wasu shafuka wadanda aka dakatar kamar na tsohon shugaban Amurka Donald Trump.

A watan Yuli, Musk ya bayyanan cewa shafin na X ya rasa rabin kudin shigar da yake samu ta hanyar tallace-tallace.

Akwai shafukan bogi wadanda akasarinsu kwamfuta ke kirkiro su da kuma gudanar da su a maimakon bil adama a shafin na X, inda ake amfani da su wurin aika sakonni na siyasa ko kuma na nuna wariyar launin fata.

AFP