Kona Alkur'ani da wasu suka yi a Sweden da Denmark ya jawo kakkausan martanin Musulmai daga sassan duniya daban-daban, ciki har da zanga-zanga a ofishin jakadancin kasasen. / Hoto: AA Archive

Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba ya jefar da Alkur'ani mai tsarki a kasa, ya tattaka shi a wajen ginin da karamin ofishin jakadancin Turkiyya ko Turkevi yake a birnin New York na Amurka.

Lamarin ya faru ne ranar Juma'a da misalin karfe biyu da arba'in da shida a agogon GMT, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Anadolu na kasar Turkiyya ya rawaito.

Jami'an tsaron ofishin jakadancin Turkiyya sun yi gaggawar daukar mataki inda suka fitar da mutumin daga ginin, wanda ke dauke da Karamin Ofishin Jakadancin Turkiyya da wani ofishi na Majalisar Dinkin Duniya.

Alkur'anin da mutumin ya wulakanta wanda aka fassara da Turancin Ingilishi ne.

An shaida wa Jami'ai a ofishin rundunar 'yan sandan New York (NYPD) da Jami'an Tsaron Ofishin Jakadanci (DSS) faruwar lamarin.

Wani bidiyo da aka watsa a soshiyal midiya ya nuna mutumin yana jifa da Alkur'ani a kasa sannan ya tattaka shi yayin da yake ihu yana cewa "Wannan Alkur'ani ne."

TRT World