| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Libya ta jaddada matsayarta ta ƙin zama fagen yaƙin ƙasashen waje bayan hare-hare a Benghazi
Majalisar dokokin Libya ta yi watsi da amfani da yankinta a matsayin filin daga na ƙasashen waje, yayin da MDD ke neman a gudanar da bincike mai zaman kansa kan hare-haren da aka kai wa jiragen ruwa mallakar Rasha da Malta a ƙasar.
Libya ta jaddada matsayarta ta ƙin zama fagen yaƙin ƙasashen waje bayan hare-hare a Benghazi
Libya ta ƙi zama fagen yaƙin rikicin ƙasashen waje bayan hare-haren jiragen sama marasa matuƙa a Benghazi / Reuters
 

Majalisar dokokin Libya ta yi watsi da amfani da yankin ƙasar ko ruwanta a matsayin sansanin kai hare-hare a yaƙi da rikice-rikicen ƙasashen waje, bayan zargin an kai hare-haren jiragen sama marasa matuƙa kan wasu jiragen ruwa biyu a birnin Benghazi.

"Libya ba ta cikin ɓangarorin da ke yaƙi a rikicin Rasha da Ukraine," in ji majalisar wakilan ƙasar a cikin wata sanarwa da aka fitar a hukumance.

Majalisar ta buƙaci gwamnatocin ƙasashen yankin da na duniya su mutunta ikon Libya da 'yancin cin gashin kanta, tare da gargaɗin ƙasashen waje kan matakan da ka iya jefa ƙasar cikin rikice-rikicen da ba nata ba ko kuma barazana ga zaman lafiyarta.

Ta kuma jaddada cewa, alaƙar diflomasiyya ko yarjejeniyoyin da Libya ta ƙulla da wasu ƙasashe ba za su zama hujjar kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin tsaron ƙasar ba.

Kira ga ƙasashen duniya kan a gudanar da bincike

Da take kira da a gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da alhakin hare-haren, majalisar ta bayyana cewa Libya na da cikakken 'yancin ɗaukar matakan shari'a da na diflomasiyya bisa dokokin ƙasa da ƙasa.

Masu AlakaTRT Afrika - Hukumomin Libya a Benghazi sun kori baƙin-haure fiye da 117,000 daga ƙasar

Majalisar ta kuma sake jaddada buƙatar samar da gwamnati guda ɗaya a ƙasar, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da rarrabuwar kawunan siyasa na barin Libya cikin haɗarin shiga rikice-rikicen ƙasashen waje.

Hare-haren da aka kai ranar Lahadi sun shafi wani jirgin ruwa mallakar Rasha da ke tashar ruwan Benghazi, inda ma'aikatan tashar su 10 suka jikkata, da kuma wani jirgin dakon kaya mallakar Malta da ke cikin teku, wanda daga bisani aka kwashe ma'aikatansa.

Mahukuntan yankin gabashin Libya sun tabbatar da cewa sun shigar da ƙorafi a hukumance ga Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman Babban Taron Majalisar da Kwamitin Tsaro, inda suka buƙaci a gudanar da bincike na ƙasa da ƙasa tare da neman Ukraine ta yi bayani kan ayyukan sojinta a Libya.

Ofishin Tallafawa Majalisar Ɗinkin Duniya a Libya (UNSMIL) ya bayyana matuƙar damuwa ranar Litinin kan ƙara ta'azzara hare-haren jiragen ruwa.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, ofishin ya ce yana sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa, tare da yin kira da a gudanar da "bincike cikin gaggawa, mai zaman kansa kuma a bayyane" kan hare-haren da aka kai a tashar ruwan Benghazi da kuma yankunan gabar tekun Bahar Rum da ke kewaye da ita.