| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Atiku ya buƙaci a yi bincike mai zaman kansa kan tsarin AI na INEC gabanin zaɓen 2027 a Nijeriya
Atiku Abubakar ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba, fasahar AI na iya jinkirta ko nuna sakamakon sahihin zaɓe a matsayin wanda ake zargi da matsala.
Atiku ya buƙaci a yi bincike mai zaman kansa kan tsarin AI na INEC gabanin zaɓen 2027 a Nijeriya
Atiku ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa da ta gayyaci jami’an INEC domin su yi bayani kan matakan kariya da tsarin binciken fasahar AI / TRT Afrika Hausa
 

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, kuma ɗantakarar shugabancin ƙasar ƙarƙashin Jam’iyyar ADC Atiku Abubakar, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) da ta fayyace tsarin fasaharta ta AI da take shirin amfani da shi domin gudanar da bincike mai zaman kansa gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

Atiku, ta bakin Daraktan Sadarwa da Dabarun Yaɗa Labaransa, Phrank Shaibu, ya ce ya aika da koke ga Shugaban INEC a madadin Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da sauran masu ruwa da tsaki, inda ya nemi a yi gaskiya wajen bayyana yadda tsarin ke aiki, tare da gudanar da bincike mai zaman kansa da kuma samar da ƙa’idojin sa ido na ɗan’adam.

Wannan buƙata na zuwa ne bayan INEC ta sanar da shirin haɗa fasahar AI da tsarin sarrafa takardu ta hanyar na’ura wajen tantance sakamakon zaɓe a matakin mazaɓu, ta hanyar tsarin Data Verification and Authentication System (DIVAS) da kuma shafin INEC Result Viewing (IReV).

Atiku ya yi gargaɗin cewa idan ba a samar da isassun matakan kariya ba, fasahar na iya jinkirta ko nuna sakamakon zaɓe na gaskiya a matsayin wanda ake zargi da matsala, sakamakon rashin ingancin hoton takarda, ko rubutun hannu ko kuma wasu matsalolin fasaha.

Masu AlakaTakarar Peter Obi da Atiku Abubakar a zaben 2027 - TRT Afrika - TRT Afrika

Ya buƙaci INEC da ta bayyana lambar sirrin tsarin AI wato (source code), da bayanan da aka yi amfani da su wajen horas da ita, da ƙa’idojin gudanar da aikinta da kuma sunayen waɗanda suka kirkire ta da kamfanonin fasahar da ke da hannu a aikin.

Haka kuma, ya buƙaci ƙwararru kan tsaron intanet masu zaman kansu, da wakilan jam’iyyun siyasa da ƙungiyoyin fararen-hula su gudanar da bincike kan tsarin kafin atisayen gwajin tantance masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar da aka shirya gudanarwa a ranar 28 ga Nuwamba, 2026.

Atiku Abubakar ya jaddada cewa ya kamata fasahar AI ta zama wani kayan aiki na taimakawa wajen gudanar da ayyukan zaɓen, ƙarƙashin kulawar ɗan’adam, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a ba shi ikon sauya sakamakon zaɓe da goge shi ko hana shigar da shi har abada ba.

Ya kuma buƙaci INEC da ta samar da wani bayyanannen tsari na sake duba sakamakon da na’urar ta nuna yana da matsala, tare da bai wa jam’iyyun siyasa damar sa ido kan yadda ake shigar da sakamakon zaɓe a kan lokaci.

Kazalika, Atiku ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Ƙasa da ta gayyaci jami’an INEC domin su yi bayani kan matakan kariya da tsarin binciken fasahar, tare da buƙatar masu sa ido kan zaɓe su yi bincike sosai kan yadda ake shigar da sakamako ta hanyar na’ura.

Haka kuma, ya ce dole ne ‘yan Nijeriya su samu damar tabbatar da cewa sakamakon da aka tattara a rumfunan zaɓe ya yi daidai da wanda aka shigar a shafukan hukumar na intanet.