| Hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
Turkiyya ta ba da sabbin shawarwari tsaro kan Bahar Aswad bayan ƙaruwar hari kan jiragen ruwa
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Fidan ya yi kira kan a samar da tsaro a Bahar Aswad a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar kai hare-hare kan jiragen ruwa ciki har da masu alaƙa da Turkiyya.
Turkiyya ta ba da sabbin shawarwari tsaro kan Bahar Aswad bayan ƙaruwar hari kan jiragen ruwa
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan / Anadolu Agency
2 awanni baya

Turkiyya ta gabatar da wata taƙaitacciyar shawara kan tsaro game da Bahar Aswad bayan harin da aka kai kwanan nan kan jiragen da ke da alaƙa da Turkiyya ya jawo damuwa kan sha’anin kasuwancin yankin da haɗarin yaɗuwar yaƙi zuwa wuraren da ke kewaye.

"Idan ba za a iya cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta zaman lafiya ba, muna kira a yi ƙwarya-ƙwaryar yarjejeniya a wurare biyu: dakatar da kai hari kan kayan aikin makamashi da tabbatar da tsaro ga zirga-zirgar jiragen kasuwanci a Bahar Aswad a cikin salama," in ji Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan a ranar Asabar.

Ya tuna yadda yarjejeniyar hatsi ta Bahar Aswad wadda Turkiyya da Majalisar Dinkin Duniya suka shiga a 2022 ta bayar da damar fitar da hatsi na Ukraine cikin aminci "ta kare dukkan jiragen daga hare-hare duk a yakin," kamar yadda Fidan ya bayyana inda kuma ya ce ana bukatar irin wannan yarjejeniya don kare kasuwanci.

"Yanzu akwai sabuwar bukata ga irin wannan tsari," in ji shi.Bayanin Fidan ya biyo bayan zargin harin Rasha kan wani jirgin Turkiyya da ke ɗaukar man sunflower a Bahar Aswad, wanda ya sanya rayukan ma'aikata 11 cikin haɗari, inda harin ya kuma zama na biyu irinsa a kan jirgin Turkiyya a cikin kwana biyu.

"Alhamdulillah, babu ma'aikatan Turkiyya da suka ji rauni zuwa yanzu," in ji Fidan, inda ya ƙara da cewa Turkiyya na "bibiyar lamarin sosai."

Bayan harin, rundunar sojin ruwa ta Ukraine ta ce Rasha ta yi amfani da jirgin sama mara matuki (drone) wajen kai hari kan jirgin Turkiyya VIVA yayin da yake tafiya zuwa Masar.

Zelenskyy ya bayyana harin a matsayin "kalubale kai tsaye daga Rasha ga duniya baki ɗaya," inda ya sha alwashin ramawa.

Erdogan ya yi kira a samar da kwanciyar hankali a Bahar Aswad

Maganganun Zelenskyy sun biyo bayan gargaɗin da Erdogan ya yi a rana ɗaya kafin haka game da guje wa mayar da Bahar Aswad yankin rikici, a yayin tattaunawar gaba da gaba fuska da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, a ranar Jumma'a.

"Bai kamata a mayar da Bahar Aswad wurin rikici ba. Wannan ba zai amfani Rasha ko Ukraine ba. Kowa na buƙatar 'yancin zirga-zirga da tsaro a Bahar Aswad," in ji Erdogan a ranar Jumma'a.

An kai harin kan jirgin Turkiyya ne a yayin da yake aiki a yankin tattalin arziki na musamman na Ukraine, yana amfani da hanyar hatsi da aka samar don wucewar kayayyakin gona a cikin aminci domin wucewar kayayyakin gona.

Haɗarin ya ƙaru a daidai lokacin da harin teku ya ƙaru dangane da rikicin.

Ruwa mai haɗari

Kiev ta kai hare-hare da dama na jirage marasa matuƙa kan masana'antun mai na Rasha a wannan shekarar don rage damar Moscow na samun kuɗin yaƙin a Ukraine.

Ana tafiyar da miliyoyin gangunan mai zuwa kudu daga Rasha ta tekun Bosphorus na Istanbul da ke Tukiyya da Dardanelles zuwa Mediterranean, inda kuma jiragen ruwan Turkiyya da dama ne wannan harin ke rutsawa da su.

A farkon Disamba, Ankara ta kira jakadan Ukraine da kuma mai rikon mukamin shugaba na ofishin jakadancin Rasha zuwa ma'aikatar harkokin wajen don isar da damuwarta a matsayin martani.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce irin waɗannan hare-hare na nuna wani mummunan ƙaruwa ne da ba za a iya yin uzuri ba.

Ukraine ba ta tabbatar ko musanta zarginta da ake yi a kan wannan harin ba.

Rasha, wadda ta kaddamar da mamayar ƙasa-da-ƙasa a kan Ukraine a watan Fabrairun 2022, ta zargi Ukraine da fashi a teku kuma ta yi barazanar mayar da martani ta hanyar katse Ukraine daga teku a matsayin mayar da martani ga hare-haren da aka kai kan tankokin mai.