Ƙungiyar Likitocin Masu Aikin Neman Ƙwarewa ta Ƙasa (NARD) ta bayyana cewa fiye da kashi 35 cikin 100 na yara ‘yan Nijeriya da ke ƙasa da shekaru biyar na fama da rashin abinci mai gina jiki, inda ta bayyana matsalar a matsayin babban ƙalubale ga lafiyar jama’a.
A wani rubutu da ta wallafa a X a ranar Alhamis, NARD ta ce fiye da kashi 35 cikin 100 na ‘yan ƙasa da shekara biyar suna fama da matsalar.
“Rashin abinci mai gina jiki yana da babban tasiri wajen mutuwar yara. Haka kuma yana shafar ci gaban ƙwaƙwalwa, saurin kamuwa da cututtuka, da kuma aikin ƙasa,” in ji ƙungiyar.
NARD ta bayyana cewa matakan magance matsalar sun haɗa da rabon abinci na musamman da ake amfani da shi wajen magance matsalar rashin abinci mai gina jiki (RUTF), da shirin al’umma na kula da rashin abinci (CMAM), da kuma ba da shawara kan ciyar da jarirai da ƙananan yara (IYCF).
Bincike ya nuna waɗannan dabaru suna taimakawa sosai wajen ƙara yawan murmurewa da kuma samun lafiyar yara, in ji ƙungiyar.
“Mambobin NARD na gaba-gaba wajen aiwatar da shirye-shiryen yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma bincike a faɗin Nijeriya,” in ji ƙungiyar.
Ƙungiyar ta yi kira da a ba da tallafi ga shirye-shiryen abinci masu ɗorewa domin kare lafiyar yara a faɗin ƙasa.
A watan Agusta, Gwamnatin Tarayya ta bayyana matsalar rashin abinci mai gina jiki a Nijeriya a matsayin “matsalar gaggawa ya ƙasa”.
Asarar da ake samu a duk shekara saboda rashin abinci mai gina jiki ta haura dala biliyan 1.5, in ji mai taimaka wa shugaban ƙasa kan lafiyar jama’a, Uju Rochas-Anwuka.
Rochas-Anwuka ya bayyana cewa wannan matsala tana rage ƙarfin ɗan adam da kuma ci gaban ƙasa.
A farkon watan Yuli, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya gargadi cewa rashin abinci mai gina jiki yana hana kusan kashi 40 cikin 100 na yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar ci gaban da ya kamata su samu.
A yayin taron ƙasa kan Abinci da Tsaron Abinci a Abuja, ya bayyana wannan matsala a matsayin “ƙalubalen ƙasa.”
Ya kuma jaddada cewa wannan tunatarwa ce kan cewa rashin wadatar abinci ba yunwa kaɗai ba ne.