Wata babbar tawaga ta masu shiga tsakani daga Kungiyar raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta gana da shugabannin riƙon ƙwarya na Guinea-Bissau a ranar Litinin, a wani yunƙuri na kawo ƙarshen rikicin siyasa da ke faruwa a ƙasar cikin lumana, hakan na zuwa ne bayan juyin mulkin sojoji da aka yi a makon da ya gabata.
Tawagar wadda Shugaban Ƙasar Sierra Leone Julius Maada Bio ke jagoranta, ta gana da hukumomin da shugaban riƙon ƙwarya na Guinea-Bissau Janar Horta Inta-A ke shugabanta.
Ɓangarorin biyu sun shaida wa manema labarai a babban birnin Bissau bayan wani taro na sirri cewa "an gudanar da muhimman tattaunawa."
Bio ya jaddada matsayar ECOWAS na Allah wadai da ƙwace mulki da sojoji suka yi, sannan ya yi kira da a gaggauta dawo da dokar tsarin mulƙin ƙasa da kuma harkokin zaɓe.
Joao Bernardo Vieira, Ministan Harkokin Wajen Guinea-Bissau na riƙon ƙwarya, ya ce taron ya "amfanar sosai."
Buƙatar mika mulƙi
Ya sanar da cewa za a gabatar da buƙatar mika mulƙi ta shekara guda ga taron ECOWAS da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga Disamba a Abuja, fadar gwamnatin Nijeriya, inda za a tantance taswirar mika mulƙin.
A ranar Alhamis ne ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da Guinea-Bissau daga hukumominta da ke yanke shawara bayan juyin mulkin sojojin wanda ya hambarar da Shugaba Umaro Sissoco Embalo.
Yayin da suke Bissau, masu shiga tsakani sun kuma gana da jami'an zabe don gano ko za su iya fitar da sakamakon zaben shugaban ƙasar da aka gudanar.
Sai dai wakilin Majalisar Dinkin Duniya na yankin Yammacin Afirka da Sahel, Leonardo Simao, ya ce Hukumar Zabe ta Kasa a Guinea-Bissau ta ce ba ta da hurumin wallafa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisu kamar yadda ECOWAS ta buƙata domin ba ta tattara dukkan sakamakon ba tukunna.
Tawagar masu shiga tsakanin dai za ta gabatar da rahotonta ga shugabannin ƙasashe, waɗanda za su yanke shawara daga ƙarshe.
Iƙirarin nasara daga masu adawa
A wata sanarwa da aka yada ta gidan talabijin ɗin gwamnatin ƙasar a ranar Laraba da ta gabata, wani gungun jami’an sojoji da suka bayyana kansu a matsayin “Manyan ƙwamandojin Sojin Maido da Tsaron Ƙasa da Tsarin Doka” sun sanar da cewa sun “karɓi cikakken iko na ƙasar.”
Juyin mulkin Guinea-Bissau ya biyo bayan ikirarin samun nasara a zaɓen da aka gudanar na ranar 23 ga Nuwamba da ɗantakara mai zaman kansa Fernando Dias da kuma magoya bayan Shugaba Embalo duk suka yi adaidai lokacin da al’ummar ƙasar ke jiran sakamakon zaɓen a hukumance.













