‘Yan jarida bakwai mambokin Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa (NUJ) ranar Litinin sun rasa rayukansu a hanyarsu ta komawa gida daga ɗaurin auren abokin aikinsu a Ƙaramar Hukumar Kaltungo da ke jihar Gombe a arewacin Nijeriya.
Bayan halartar ɗaurin auren, tayar motar bas ɗin da suke ciki ta fashe a kusa da garin Kumo, Ƙaramar Hukumar Akko, inda motar ta ƙwace wa direban tare da nufar cikin daji.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) reshen Gombe, Samsan Kaura da Darakta Janar na Watsa Labaran Gidan Gwamnati, Ismaila Misilli, sun tabbatar da rasuwar mutanen bakwai, inda wasu huɗu kuma suka jikkata, kuma suna samun kulawa a asibiti.
Waɗanda suka rasa rayukansu sun haɗa da Zarah Umar, Manajar Labarai kuma Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamna a Ofishin matar Gwamna; Manu Haruna Kwami, Manajan Gudanarwa a NTA, da Musa Tabro, Manajan Labarai da ya yi ritaya.
Sauran sun haɗa da Aminu Adamu, Babban Direba; Adams Danladi na Star Times; Judith Kutus, Jami’in Yaɗa Labarai a Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya ta Jihar Gombe.
Tuni Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suma mutu inda ya yi musu fatan samun rahama da sauki cikin gaggawa ga waɗanda suka jikkata.
Gwamnan ta bakin Misilli ya ce “Wannan ibtila’i na da bakanta rai. Mun rasa abokan aiki, abokan kawo cigaba, kuma ma’aikata da suka sadaukar da kawunansu wajen hidimta wa al’umma.”
Ya ƙara da cewa zukatansu kuma na tare da waɗanda suka jikkata, suna kuma yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa.

















