China ta shiga jerin ƙasashen duniya da ke nuna damuwa da kuma yin adawa da amincewar da Isra'ila ta ce ta yi da yankin Somaliland da ya ɓalle, Somaliya a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Waje, Lin Jian a ranar Litinin ya ce China na nuna damuwa kuma tana yin ƙaƙƙarfar adawa da matakin, a martani ga wata tambaya da aka masa kan matakin Tel Aviv na yarda da Somaliland a makon da ya gabata.
Yayin da ya tuna yadda kasashe daban-daban da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka ƙi kuma suka yi suka ga wannan mataki, Lin ya ce China "ta tsaya tsayin daka wajen goyon bayan 'yancin Somaliya, sake haɗa ƙasa, da cikakken ikon yankinta," kasancewar Somaliland wani "bangare ne da ba za a iya rabawa ba" na ƙasar.
Beijing tana adawa da kowanne yunƙuri da zai raba yankin Somaliya. Batun Somaliland lamari ne na cikin gida na Somaliya gaba ɗaya kuma ya kamata al'ummar Somaliya su warware shi ta hanyar da ta dace da yanayin ƙasa.
Lin ya ce kasashe "da ke wajen yankin su daina tsoma baki marar dacewa. Babu wata ƙasa da ya kamata ta tallafa wa ko ta taimaka wa ƙungiyoyi masu rarrabuwar kawuna a wasu ƙasashe don amfanin kanta na ƙashin kai."
Mai magana da yawun ma'aikatar ya kira ga hukumomin Somaliland da su fahimci inda al'amura suka dosa, sannan su yi gaggawar dakatar da ce-ce-ku-ce tsakaninta da masu neman yin katsalandan 'yan ƙasashen waje.
A ranar Jumma'a, Isra'ila ta zama ƙasa ta farko a duniya da ta amince da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, wanda ya haifar da martani na ƙin yarda daga ƙasashe da dama a Afirka da Gabas ta Tsakiya, ciki har da Turkiyya, wadda kuma ta kasance cikin sanarwar da Qatar ta fitar a ranar Asabar.
Somaliland ta ayyana 'yancinta daga Somaliya a 1991 kuma ta yi aiki a matsayin ƙasar da ta ɓalle fiye da shekaru 30, amma ba ta samu amincewa a hukumance daga kowace ƙasa mamba ta Majalisar Dinkin Duniya ba.
Gwamnatin Somaliya ta ƙi yarda da Somaliland a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta, tana ɗaukar ta a matsayin ɓangare na ƙasar, kuma tana ganin duk wata yarjejeniya kai-tsaye ko hulɗa da ita a matsayin take 'yancin ƙasa da haɗin kan ƙasar.















