| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Da haɗin gwiwarmu Amurka ta kai hari Nijeriya: Ma'aikatar Harkokin Waje
Da tsakar daren Alhamis ɗin nan ne a wani saƙo ta shafin sada zumunta na Truth Social, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasarsa ta kai hare-hare a kan 'yan ta'adda na ƙungiyar ISIS (Daesh) a arewa maso yammacin Nijeriya.
Da haɗin gwiwarmu Amurka ta kai hari Nijeriya: Ma'aikatar Harkokin Waje
Tun a baya dai Trump ya saka Nijeriya a jerin kasashe masu damuwa ta musamman bisa zargin ana aikata kisan kare dangi ga Kiristocin kasar. / Reuters
11 awanni baya

Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya ta tabbatar da hare-haren da Amurka ta kai a Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar, tana mai cewa da haɗin gwiwar ƙasar aka kai su.

Wata sanarwa daga ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya da ta biyo bayan sanarwar shugaban Amurka Donald Trump da Cibiyar Bayar da Umarni ta Sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ta nuna cewa hukumomin Nijeriya suna da masaniya kan harin da Amurka ta kai a yankin Sokoto na arewa maso yammacin Nijeriya.

Hasali ma, sanarwar wadda Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Nijeriya KImiebi Imomotimi Ebienfa ya fitar ta bayyana cewa da amincewa da haɗin gwiwarta hakan ta tabbata.

A cewar sanarwar, an kai harin ne domin kawar da barazanar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, tana mai cewa hare-haren ba su da alaƙa da addini tun da dai ‘yan ta’adda suna kashe kowa, ciki har da Musulmai da Kirista.

“Bisa yin la’akari ga ayyukan ƙasa da ƙasa da kuma yarjeniyoyin fahimtar juna na aiki tare, wannan haɗin gwiwa ya haɗa da musayar bayanan sirri, dabarun gudanar da ayyuka, da sauran taimakon juna da suka yi daidai da dokokin ƙasa da ƙasa na girmama ikon juna da tabbatar da aniyar bai-ɗaya ta samar da tsaro a duniya,” sanarwar ta bayyana.

Masu AlakaTRT Afrika - Jiragen Amurka na nazarta da tattara bayanan sirri kan Nijeriya bayan barazanar Trump: Reuters

Sanarwar ta kuma ce duk wani matakin da za a ɗauka na yaki da ta’addanci yana da manufar kare rayukan fararen-hula, kare haɗin kan ƙasa, da kare ‘yanci da mutuncin dukkan ‘yan ƙasa ba tare da la’akari da ƙabila ko addini ba.

Kazalika sanarwar ta ce “Aikata kowane irin ta’addanci a kan Kiristoci, Musulmai ko wasu wasu al’ummu na daban ya saɓa wa aƙidun Nijeriya da tsaro da zaman lafiyar ƙasa da ƙasa.”

An kuma bayyana cewa gwamnatin tarayyar Nijeriya za ta ci gaba da mu’amala da ƙawance ta tabbatattun hanyoyin diflomasiyya da tsaro don kassara ‘yan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗaɗe da kayan aikinsu, dakatar da barazanar tsallaka iyaka da kuma inganta ƙarfin tsaro da tattara bayanan sirri na Nijeriya.

A ƙarshe sanarwar ta ce Nijeriya za ta ci gaba da aiki da kawayenta kuma ma’aikatar Harkokin Waje za ta dinga sanar da jama’a ko me ake ciki ta hanyoyin da suka kamata.

Masu AlakaTRT Afrika - Amurka ta kai hari kan mayaƙan Daesh a Nijeriya, in ji Donald Trump

Da tsakar daren Alhamis ɗin nan ne a wani saƙo ta shafin sada zumunta na Truth Social, Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya sanar cewa Ma'aikatar Yaƙi ta ƙasarsa ta kai hare-haren a kan 'yan ta'adda na ƙungiyar ISIS (Daesh) da ke arewa maso yammacin Nijeriya.

Kuma jim kaɗan bayan sanarwar ta Trump, Cibiyar Bayar da Umarni ta Sojin Amurka a Afirka (AFRICOM) ta tabbatar da kai harin.

Sanarwar da AFRICOM suka fitar ta shafin X ta ce an kai harin ne a yankin jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Nijeriya.