Lallasawar da Manchester City ta yi wa Manchester United da ci 3-0 ranar Lahadin makon jiya, ya kara wage bakin masu sukar kocin United, Ruben Amorim.
Tun bayan karbar ragamar United daga hannun Erik ten Hag, Amorim ya ci wasa 8 ne kacal cikin wasanni 31 na gasar Firimiya.
Watannin 10 kenan bayan zuwansa, an kwatanta tagomashin United da wasu kungiyoyin gasar Firimiya 17, sai aka gano Amorim ya ciyo maki 31 ne daga wasanni 31, wanda ke nufin shi ne mafi karancin samun maki.
Tun bayan baro kungiyar Sporting SP ta Portugal, Amorim ya tarar da tarin matsaloli a United, ciki har da matsalar mai tsaron gida.
Sai dai duk da cewa ya aike da golan da yake yawan jawo musu matsala, Andre Onana zuwa aro a Trabzonspor ta Turkiyya, wanda yake tsare masa raga a yanzu, Altay Bayindir shi ma yanz ta nuna rashin tagomashi.
Alamu na nuna cewa sabbin ‘yan wasan da Man United ta kawo a kakar bana, irinsu Bryan Mbeumo, suna bukatar lokaci kafin a ga kyawun kamun ludayinsu.
A halin yanzu, Amorim mai shekaru 40 yana fuskantar wani babban wasa da Chelsea ranar Asabar mai zuwa a gida, kuma ana ci gaba da tararrabi kan makomarsa a Old Trafford idan rashin nasarar ta ci gaba da bin sa.