WASANNI
2 minti karatu
Me zai hana Mbappe halartar bikin ba da kyautar Ballon d'Or na bana?
Tauraron ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe ba zai halarci bikin ba da kyautar Ballon d'Or ba, kuma ya sanar da zaɓinsa na wanda ya kamata ya lashe kyautar.
Me zai hana Mbappe halartar bikin ba da kyautar Ballon d'Or na bana?
/ AP
17 Satumba 2025

A karo na biyu a jere, tawagar Real Madrid ta Sifaniya za ta ƙaurace wa bikin ba da kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafa na duniya na bana, wanda za a yi ranar 22 ga Satumba.

Shi ma tauraron ɗan wasan Real Madrid, Kylian Mbappe ya tabbatar da cewa ba zai halarci bikin da za a yi a babban birnin ƙasarsa na Paris ba.

Maimakon haka, ɗan wasan ya sanar da cewa zai kalli bikin a gida a talabijin.

A kakar bara, haziƙin ɗan wasan ɗan asalin Faransa ya ci ƙwallaye 44 a duka gasanni, inda ya zama wanda ya fi kowa cin ƙwallo a gasar La Liga.

Sai dai duk da gwanintar da ya nuna a kakarsa ta farko a Madrid, Mbappe ba ya tunanin yana da nasibin lashe Ballon d'Or, saboda Real Madrid ba ta lashe wani babban kofi a kakar ba.

Mbappe ya sanar da wannan ne a tattaunawarsa da ‘yan jarida bayan wasan Real Madrid da Marseille a gasar Zakarun Turai a Santiago Bernabeu ranar Talata.

Waye zaɓin Mbappe?

Ko da aka tambayi Kylian Mbappe game da waye zaɓinsa na wanda ya kamata ya lashe kyautar a bana, ya ce, “Zan yi murna idan Dembélé ya lashe saboda abokina ne kuma na goyi bayansa tun usili."

Da ma dai ɗan wasan na PSG, Ousmane Dembele shi ne ke kangaba a jerin waɗanda ake ganin sun cancanci lashe babbar kyautar a fagen ƙwallo.

Dembele wanda shi ma ɗan asalin Faransa ne, ya ci ƙwallaye 35 da tallafin ƙwallo 16 a duka gasanni, inda ƙungiyarsa ta PSG ta ci kofuna uku har da na Zakarun Turai.

Baya ga Dembele, akwai ‘yan wasan Barcelona biyu, Lamine Yamal da Raphinha waɗanda zuka nuna bajinta a bara, inda suka taimaka wa Barca lashe kofuna uku a gida Sifaniya.

A halin yanzu dai, masoya Kylian Mbappe suna masa kyakkyawan fatan lashe kyautar a baɗi, musamman ganin yadda tuni ya fara yin zarra a kakar bana inda ya ci ƙwallaye 6 a wasanni 5.

Da taimakonsa, Real Madrid ta ci duka wasanni 5 da ta buga a bana, a duka gasanni zuwa yanzu.