WASANNI
2 minti karatu
Jose Mourinho zai zama kocin Benfica, ƙungiyar da ya fara horarwa a rayuwarsa
Rahotanni daga Portugal na cewa Benfica za ta naɗa Jose Mourinho bayan sallamar kocinta Bruno Lage, sakamakon rashin nasara a wasansu na farko na gasar Zakarun Turai.
Jose Mourinho zai zama kocin Benfica, ƙungiyar da ya fara horarwa a rayuwarsa
/ AFP
17 Satumba 2025

Ranar Talata 16 ga Satumba ne aka fara Gasar Zakarun Turai ta UEFA, inda ƙungiyar Benfica ta Portugal ta yi rashin nasara a hannun Qarabag ta Azerbaijan da ci 2-3.

Faɗuwar da Benfica ta yi ta ƙona ran masoya ƙungiyar, musamman ganin yadda su suka fara zura ƙwallaye biyu a minti na 6 da minti na 16 na wasan, kafin Qarabag ta farke har ta doke su.

Kwana ɗaya bayan wannan wasa, rahotanni daga Portugal na cewa Benfica ta sallami kocinta Bruno Lage mai shekaru 49, kamar yadda Reuters ya ruwaito.

A safiyar Laraba ne Benfica ta fitar da sanarwar da ke cewa sun cim ma matsaya kan raba gari da Koci Lage.

Shugaban Benfica, Rui Costa ya ce za su yi gaggawar sanar da ɗauko sabon koci gabanin wasansu na gasar cikin gida tare da AVS Futebol SAD a ranar Asabar.

Bugu da ƙari rahotannin na cewa Benfica za ta naɗa shahararren kocin nan ɗan asalin ƙasarsu Portugal, wato Jose Mourinho mai shekaru 62.

Dawowa gidan jiya

A tarihi, Jose Mourinho ya fara aikin horar da ƙungiyar ƙwallo ne a ƙungiyar ta Benfica a shekarar 2000, wanda ke nufin dawowarsa ƙungiyar zai zama abin tarihi.

Mourinho dai ya yi aiki a manyan ƙungiyoyin Turai, wato Porto, Chelsea, Real Madrid, Manchester United, Inter Milan, Roma, da Tottenham.

A watan Agustan nan ne ya bar Fenerbahce ta Turkiyya, kwana biyu bayan da ya sha kaye a hannun Benfica a wasan share fagen gasar Zakarun Turai.

Kocin ya yi suna wajen lashe kofuna daban-daban a duk ƙungiyar da ya riƙe, idan ban da Tottenham da kuma Fenerbahce wadda ya baro a watan jiya.

Ita kuwa Benfica ta ƙare kakanni biyu da suka gabata a matsayi na biyu, sannan a halin yanzu tana mataki na shida a teburin gasar Primeira da maki 10 bayan wasanni huɗu.

Idan Mourinho ya karɓi aiki yanzu, to zai kama hanyar karawa da tsofaffin ƙungiyoyi biyu da ya jagoranta a baya, wato Chelsea ran 30 ga Satumba, da Real Madrid a Janairun 2026.