Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai tsawaita tsagaita wuta da Iran domin ba ta ƙarin lokaci na tattaunawa, amma za a ci gaba da ƙawanyar sojin ruwan Amurka kan tashoshin jirage ruwan ƙasar.
Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta ranar Talata cewa shi zai "tsawaita tsagaita wuta" har zuwa lokacin da Iran za ta fitar da shawarar kawo ƙarshen rikicin. Sai dai kuma ya “ba da umarni ga sojojinmu su ci gaba da ƙawanyar."
Tsawaita tsagaita wutar Trump na zuwa ne sa’o’i kafin lokacin da aka yi imanin cewa za ta ƙare.
Ya kuma zo a wani lokaci da Fadar White House ta ce mataimakin shugaban ƙasa JD Vance ba zai tafi Pakistan ba kan abin da ake tsammanin zai kasance zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya.
Shugaban Amurka ya bayyana katsewar ƙarin tattaunawa a matsayin abin da ya samo asali daga rashin jituwa tsakanin ‘yan Iran, yana mai ƙarawa da cewa shugabannin Pakistan ne suka nemi ya tsawaita tsagaita wutar.
"Bisa rarrabuwar kai mai muni tsakanin gwamnatin Iran, abin da bai zo da mamaki ba kuma bisa ga buƙatar Fild Mashal Asim Munir, da kuma Firaminista Shehbaz Sharif na Pakistan, an nemi mu dakatar da harinmu kan ƙasar Iran har zuwa lokacin da shugabanninta da kuma wakilanta suka samo wata shawara ta bai-ɗaya," kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social.
Ƙawanyar sojin ruwa za ta ci gaba
Sai dai kuma, ƙawanya ta tashoshin jiragen ruwa na tekun Iran a mashigar ruwan Hormuz za ta ci gaba, in ji Trump, yayin da sojin Amurka za su " ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana."
Tsagaita wutar, in ji shi, za ta tsawaita "har zuwa lokacin da aka miƙa shawararsu, kuma aka kammala tattaunawa, ta wata hanya ɗaya."
Jami’an Iran sun zargi Amurka da karya yarjejeniyar a ƙarƙashin sharuɗɗa 10 da Tehran ta zayyana daga farkon tsagaita wutar mai rauni.
Abin da ya fi jan hankali a batun shi ne mashigar ruwan Hormuz, wata muhimmiyar hanyar gudanar mai ta duniya, wadda Iran ta rufe daga farkon rikicin. Trump ya ce ya amince da tsagaita wutar bisa sharaɗin cewa za a buɗe mashigar gaba ɗaya.
Sai dai kuma tafiya ta mashigar ta kasance yar kaɗan. Bayan zagayen tatttaunawa na farko ya rushe, sojin ruwan Amurka sun ƙaƙaba ƙawanya kan tashoshin jiragen ruwan Iran kusa da hanyar ruwan.










