Shugaba Tinubu ya amince da saka haraji na kashi 15 cikin 100 kan man fetur da man gas da ake shigarwa cikin Nijeriya.
Matakin wanda ke da manufar kare matatun mai da kuma daidaita fannin tace man ƙasar ka iya haddasa ƙarin farashin mai a Nijeriya, a cewar rahotanni.
A cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 21 ga Oktoban 2025 da aka fitar ranar 30 ga Oktoban 2025 kuma wadda ya rubuta ga hukumar tara haraji ta gwamnatin tarayya (FIRS) da kuma hukumar da ake kula da fannin tace mai, Tinubu ya ba da umarnin ƙaddamar da harajin a matsayin wani ɓangare na abin da ya bayyana a matsayin “tsarin haraji mai la’akari da kasuwa.”
Wasiƙar, wadda magatakardansa na kansa, Damilotun Aderemi ya sanya hannu, wadda jaridar Punch ta samo ranar Laraba ta bayyana amincewar Shugaban Kasar bayan wata shawarar shugaban FIRS, Zacch Adedeji.
Shawarar ta nemi a saka haraji na kashi 15 cikin 100 na haraji kan farashi da inshora da kuma kimar man fetur da man gas da ake shigarwa domin daidaita farashin shigar da mai da yanayin kasuwa ta cikin gida.
Adedeji, a cikin wasiƙarsa ga shugaban ƙasar, ya bayyana cewa matakin wani ɓangare ne na garambawul da ake yi na haɓaka tace mai a cikin ƙasar da tabbatar da ɗorewar farashi da kuma ƙarfafa tattalin arziƙin man ƙasar bisa kuɗin naira daidai da manufar gwamnatin ta Renewed Hope Agenda, ta ɓangaren dogaro da kai ta makamashi da kuma ɗorewar tattalin arziƙi.
“Muhimmiyar manufar wannan shirin shi ne aiwatar da cinikin ɗanyen mai cikin kuɗi na gida da ƙarfafa ikon tace mai a gida da kuma tabbatar da samar da mai da sauƙi a faɗin Nijeriya,” in ji Adedeji.
Shugaban na FIRS ya kuma yi gargaɗin cewa rashin daidaiton da ake samu tsakanin man da aka tace a cikin ƙasar da kuma wanda ake shigowa da shi ya haddasa rashin daidaito a kasuwar.










