| hausa
TURKIYYA
4 minti karatu
UNGA: Matar Shugaban Turkiyya ta baje-kolin kayayyakin al’adun Anatolia a Amurka
Emine Erdogan ta alaƙanta al’adu masu ɗorewa da ƙalubale na zamani, inda ta yi gargaɗi kan shafe tarihin Falaɗinu.
UNGA: Matar Shugaban Turkiyya ta baje-kolin kayayyakin al’adun Anatolia a Amurka
Emine Erdogan
23 Satumba 2025

Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan, wadda ke jagorantar kwamitin shawarwari na Majalisar Dinkin Duniya game kawar da shara ta yi baje kolin kayayyakin al’adun Anatoliya da ya kai ɗaruruwan shekaru kuma ta nemi a ƙara samar da matakai na diflomasiyya wajen kare Gaza.

"Rayuwa a Anatoliya wani tasiri ne da yake nuna yadda za a iya cim ma muradu masu ɗorewa. Saboda ƙofofin Anatoliya a buɗe suke ga ingantawa da tarawa da ƙarewa bisa dubban shekaru na rayuwa," a cewar Misis Erdogan ranar Talata yayin da ta karɓi baƙuncin matan shugabannin ƙasashe da gwamnatoci a New York wajen taron MDD na 80 a Gidan Turkiyya (Türkevi Center), a wani ɓangare na shirin ‘’Yan Anatoliya’ ƙarƙashin jagorancinta.

Ita da sauran matan shugabannin ƙasashe daga wasu ƙasashe da gwamnatoci sun yi yawo na kallon baje kolin da ya nuna ilimi da ƙwarewa da al’adu na Anatoliya da ya kai shekaru dubu tare da tsari na zamani.

Baje-kolin ya nuna kimanin kayayyakin al’ada 40 da kafet da aka saƙa da hannu da sarƙar ado samfurin filigree da kazaziye da tangaran da akwatuna da kayayyakin da aka ƙera da jan ƙarfe.

Baƙi sun bi ta ƙofofi da aka saka wa suna “zagayawa” da “ci-gaba” da “haɗin kai” da “ƙwarewa”, lamarin da wakiltar al’adar ƙirar Anatoliya.

‘Dunƙulewar duniya a wuri ɗaya ya saka al’adu cikin tukunya mai narkewa’

A jawabinta, Erdogan ta ce ta ji daɗin maraba da baƙi a gefen taron MDD kuma ta gabatar musu da al’adar Anatoliya mai tarin yawa.

"Kowace al’ada, kowane yare, kowane addini na taruwa waje ɗaya wajen hada wata daidaito na mutane.

“Duk da haka dunƙulewar duniya wuri ɗaya na saka al’adu cikin tukiunya mai narke abubuwa, lamarin da ke saka duniya ta zama bai ɗaya da murya ɗaya da kuma launi ɗaya."

Ta jaddada cewa, yayin ake da harsuna sama da 7,000, an yi kiyasin cewa rabinsu za su ɓace zuwa ƙarshen ƙarni na 21.

“Mutuwar wani harshe, kamar yadda ta bayyana, yana nuna mutuwar al’adar wasu mutane da abubuwan da ke motsa wa mutanen zuciya da yadda suke ganin duniya.

Erdogan ta jaddada cewa kashi 18 cikin 100 ne muradun ci-gaba mai ɗorewa na MDD ne kawai aka cima.

"A matsayinmu na bil'adama, muna neman hanyar da ta dace, mai juriya, mai daraja aiki, ya rungumi dabi'a, da kuma samar da zaman lafiya. Maganin matsalar ba ta da nisa - yana cikin tushen wayewarmu. Hikimar Anatolia hanya ce ta taswirar rayuwa mai ɗorewa, "in ji ta.

Matar Shugaban Ƙasar ta jaddada cewa, abincin Turkiyya da kansa ba mai sa a tara shara ba nea kuma ana kiyaye ayyuka irin su samar da ɗa'a, da sabuntawa da kayan kwalliya masu ɗorewa da kayan halitta, da tallafa wa sana'o'in mata a yankin Anatoliya tsawon shekaru aru-aru.

Ta bukaci yada wannan ruhi zuwa yankunan da yaki ya daidaita kamar Gaza da Ukraine: "Bari mu mayar da hikimar wayewarmu zuwa gada na 'yan’uwantaka da ke haɗe nahiyoyi."

‘Ba za mu bar Isra'ila ta shafe Falasdinun da aka samar kafin 1945 ba’

Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya ta jaddada mahimmancin tsayin daka wajen ganin bayan shafe tarihi tana mai cewa: "Bai kamata mu bari Isra'ila ta shafe mu daga tarihin kasar Falasdinu ba kafin shekarar 1945. Sabanin haka, dole ne mu adana da koyar da wannan tsohowar tarihi da al'adu. A kan bama-bamai, dole ne mu yi tsayin daka da alkalami, littattafai, da kuma tunawa."

Ta yi gargaɗi kan matsananciyar matsalar jin-ƙai a Gaza inda ta ce: "Ko kunsan, yara a Gaza suna fara barci amma sai su gaza farfaɗowa? Kudan yara 19,000 aka kashe cikin shekaru biyu kacal. Gaza ta zama makabartar yara kuma wajen binne imanin al’umma."

Ta kuma yi kira ga al’ummar duniya su zama masu magan kan Gaza, su buɗe kafofin jin-ƙai, da ƙarfafa dokokin duniya. Ta yi maraba da matakin ƙasashe da dama da suka amince da ƙasar Falasɗinu, ina ta kira shi da “babban sauyi kan zaman lafiya da adalci.”

Al’adun Anatolia ‘suna bunƙasa ɗorewar hikimar al’adu’

Matar shugaba Erdogan ta ce ta yi “matuƙar farin ciki” da saukar matan shugabannin duniya a wani taro a New York inda ta nuna al’adun Anatolia, da fasahar ƙere-ƙere.

A wani saƙo da ta wallafa bayan taron, Matar shugaban Turkiyyar ta bayyana bikin nune-nune kayan gona da ake nomawa a Anatolia, da al’adun girke-girke da aka samo daga kakanni da gwanintar masu ƙere-ƙere.

Ta ce shirin na neman kawo kyawawan hikimomin Anatolia, da basirar ƙere-ƙere da girmama yanayin halittu a duniya. Matar Erdogan ta ce tana fatan ganin an “ɗinke ɓarakar al’adu, don kyautata ƙawancen al’ummar duniya.”

 

 

Rumbun Labarai
Turkiyya ta yi umarnin kama Firaministan Isra'ila Netanyahu da wasu mutane kan kisan kiyashi a Gaza
Turkish Airlines ya sayi hannun jari na dala miliyan 355 a kamfanin Air Europa na Spain
Erdogan ya yi Allah wadai da kashe fararen-hula a birnin Al Fasher na Sudan
Za a gudanar da tattaunawa a Istanbul kan yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza da matsalolin jinƙai
Tsarin duniya na yanzu ya fi ba da fifiko kan iko fiye da adalci: Babban Daraktan TRT Sobaci
Hamas ba ta da nukiliya, amma Isra'ila na da su: Erdogan ya nemi Berlin ta ɗauki mataki kan Tel Aviv
Ana shirin fara taron TRT World Forum karo na 9 a Istanbul
Cikin hotuna: Yadda aka yi bukukuwa a duk faɗin kasa na cikar Ranar Jamhuriya ta Turkiyya ta 102
Turkiyya ta yi kira a tsagaita wuta nan-take a yaƙin da ake yi a birnin Al Fasher, Sudan
Turkiyya za ta mika wa dakarunta tankar yaki ta Altay da aka samar da yawa a karon farko
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta sanar da janyewa baki ɗaya daga Turkiyya
Babu wani lissafin siyasa ko na tsaro da zai yiwu a duniya ba tare da Turkiyya ba: Erdogan
Rumfar Karfe: Fasahar Turkiyya ta cikin gida mai aiki da Ƙirƙirarriyar Basira a sabon zamanin tsaro
Shugaba Erdogan ya shirya ziyartar yankin Gulf don haɓaka alaƙar tattalin arziki da ƙawance
Turkiyya ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar Afghanistan da Pakistan
An Fara Taron Yaki da Shara na ‘Zero Waste’ a Istanbul karkashin jagorancin Emine Erdogan
Matar Shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira a bunkasa shigar mata cikin harkokin duniya
Cinikayya tsakanin Turkiyya da Afirka ta wuce $37b ana sa ran ta kai $40b a 2025: Minista
Turkiyya na da rawar da za ta taka a tsaron Turai, ta shirya domin aikin Gaza: Ministan Tsaro
Turkiyya ta yi maraba da amincewar majalisar dokokin TRCN kan ƙudurin samar da ƙasashe biyu