| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce za a taƙaita ba da biza kan 'muzguna wa Kiristoci a Nijeriya'
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce Amurka za ta takaita bayar da biza ga wasu mutane kan abin da ya ambata cuzguna wa Kiristoci a Najeriya.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya ce za a taƙaita ba da biza kan 'muzguna wa Kiristoci a Nijeriya'
Sakataren Harkokin Waje Marco Rubio ya ce Amurka za ta takaita biza kan zargin tsananta wa Kiristoci a Najeriya. / Reuters
7 awanni baya

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Laraba cewa, Amurka za ta takaita bayar da biza saboda abin da ya kira cuzguna wa Kiristoci a Najeriya.

Tuni Amurka ta takaita bayar da biza saboda take haƙƙin bil’adama, kuma Trump ya rage ba da biza sosai gaba ɗaya, musamman ga mutane daga ƙasashe masu tasowa.

A cikin wata sanarwa, Rubio ya ce Amurka za ta taƙaita bayar da biza ga mutanen da “suka bayar da umarni, ko suka amince, ko suka tallafa sosai, ko suka shiga ko suka aiwatar da keta ’yancin addini.”

Rubio ya kira wannan mataki “mataki na yanke hukunci a matsayin martani ga cin zarafi kan Kiristoci a Najeriya da ma wajen ta.”

Wakilan Najeriya sun ziyarci Amurka

A watan Nuwamba Trump ya bai wa mutane mamaki lokacin da ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa Amurka ta shirya ɗaukar matakin soja a Najeriya don yakar abin da ya kira kisan Kiristoci.

Ba tare da musanta maganganun Trump ba, jami’an Amurka tuni suka jaddada ɗaukar wasu matakai na Amurka kan Najeriya, ciki har da haɗin gwiwar tsaro da gwamnati da kuma yiwuwar takunkumin da aka nufa.

Wata babbar tawaga daga Najeriya ta ziyarci Washington kuma sun bayyana shirin “ƙarfafa haɗin kai na tsaro” tare da Amurka.