WASANNI
2 minti karatu
Kocin Liverpool Arne Slot ya ci tarar Ekitike albashin mako biyu saboda samun jan kati da garaje
An bayyana hukuncin da Arne Slot, kocin Liverpool ya yanka wa Hugo Ekitike, ciki har da hana shi albashin mako biyu, sakamakon samun jan kati da garaje a wasansu da Southampton.
Kocin Liverpool Arne Slot ya ci tarar Ekitike albashin mako biyu saboda samun jan kati da garaje
Wannan ce kakar farko da Hugo Ekitike ke buga wa Liverpool. / AP
25 Satumba 2025

Liverpool ta bayyana hukuncin da za ta yi wa Hugo Ekitike, ɗan wasanta da ya samu jan kati a wasansu da Southampton.

Rahotanni daga Liverpool na cewa za a hana Hugo Ekitike albashin mako biyu saboda samun yalon kati sau biyu, wanda ya janyo masa kora daga filin wasa.

Ekitike ya samu jan kati ne a mintinan ƙarshe na wasan bayan cire riga don murna saboda cin ƙwallon da ta ba su nasara da ci 2-1 kan Southampton a gasar Carabao Cup.

Ɗan asalin Faransa, Ekitike ya shigo wasan ne a minti na 53, inda ya canji Alexander Isak, amma sai ya samu yalon katin farko saboda nuna rashin ladabi ga alƙali.

Bayan nazarin abin da ya faru, koci Arne Slot ya ce laifin 'ba dalili kuma na shirme' ne, duk da cewa ƙwallonsa ce ta ba su nasara a wasan.

Mai shekaru 23, Ekitike ya samu yalon kati minti 8 bayan shigowarsa, saboda tamfatsar ƙwallo lokacin da alƙalin wasa Thomas Bramall ya hura usur don buga firikik.

Yalon kati biyu

A minti na 85, Ekitike ya ciyo wa Liverpool ƙwallo ta biyu inda ya cire rigarsa yayin murna a gaban masoya ƙungiyar.

Sai dai bayan haka ne sai ta tabbata cewa zai samu yalon kati na biyu, wanda zai koma jan katin sallama daga wasa.

Bayan wasan, ɗan wasan ya bayyana da-nasani inda ya ce murna ce ta ɗauke masa hankali, sannan ya ba da haƙuri ga ‘yan wasa da masoya Liverpool.

Rahotanni na cewa ladabtarwar da za a yi wa Hugo Ekitike ta ƙunshi tarar albashin mako biyu, daga albashinsa na £250,000 da yake karɓa duk mako.

Bayan nan, zai samu hukuncin haramcin wasa guda, inda zai rasa damar buga wasan Liverpool da Crystal Palace a gasar Firimiya ranar Asabar.

Liverpool ta sayo Ekitike ne kan dala miliyan $105 daga PSG ta Faransa, kuma a baya ya buga wa Eintracht Frankfurt ta Jamus.