TURKIYYA
3 minti karatu
Matasa 'yan Syria sun baje ƙirƙire-ƙirƙirensu a taron fasaha na Turkiyya 'TEKNOFEST 2025'
Babban taron baje-koli na Turkiyya ‘TEKNOFEST’ ya bai wa matasa masu hazaƙa 'yan Syria damar bayyana basirarsu.
Matasa 'yan Syria sun baje ƙirƙire-ƙirƙirensu a taron fasaha na Turkiyya 'TEKNOFEST 2025'
Matasa 'yan Syria sun yi nasara taron TEKNOFEST na kirkire-kirkiren fasaha na Turkiyya / AA
19 Satumba 2025

A karon farko, ƙasar Syria ta halarci babban taron baje-kolin jiragen sama da fasaha na Turkiyya TEKNOFEST, inda jami’ai da ‘yan kasuwa suka yi amfani da damar wajen sake bayyana fasahohin Syria ga kasuwannin yankin da ma duniya baki ɗaya.

An buɗe taron TEKNOFEST karo na 13 a ranar Laraba a filin jirgin saman Ataturk na Istanbul, wanda Gidauniyar Fasaha ta Turkiyya (T3) ƙarkashin kulawar ma'aikatar masana'antu da fasaha ta ƙasar ta shirya.

Wassim Al Omar, sakataren mataimakin ministan masana’antu da tattalin arziki, ya ce Damascus na ɗaukar TEKNOFEST a matsayin taron da wuce iya baje-koli kawai.

‘‘Ƙofa ce ga masana'antun Syria don ba su damar baje-kolin abubuwan da suka ƙware a kai tare da gina haɗin gwiwa da kamfanonin Turkiyya da na ƙasashen duniya,’’ kamar yadda ya shaida wa Anadolu.

"Kasancewa a nan wani muhimmin mataki ne; Syria na cikin wani bangare na tattaunawar yankin kan fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire."

An ƙaddamar da jirgi marasa matuki wanda Syria ta ƙera

Kamfanin AvioTech na Syria wanda ke lardin Gaziantep a Turkiyya na daga cikin kamfanonin da suka yi baje-kolin.

Wanda ya kafa shi, Hussein Ali, ya gabatar da jirgin marasa matuƙi a matsayin na farko da Syria ta ƙera, wanda aka samar da shi domin amfanin gona.

‘‘Samfurin da aka nuna zai iya ɗaukar lita 35 na magungunan kashe ƙwari ko iri,’’ in ji shi.

Injiniyoyin Syria ne suka ƙera shi gaba ɗaya, kuma tuni muka soma aiki kan sabbin wasu fasashohin, tun daga fasahar kashe gobara zuwa na jigilar kaya.’’

Ali ya jaddada cewa TEKNOFEST yana ba da damarmaki masu mahimmanci wajen haɗa kai masu ƙirƙire-ƙirƙire fasahohin daban-daban kuma yana fatan wata rana Syria za ta kafa masana’antar samarwa na kanta.

Fasahar noma don ƙarfafa samar da abinci

Ɗaya daga cikin kamfanonin da suka halarci taron, Afko, ya ƙware a tsarin injin fasaha.

Wakilin kamfanin Homam Afoura ya ce injinansu na iya yin feshi a filayen noma fiye da kadada 30 kuma ana fitar da su zuwa ƙasashe sama da 60.

"Burin shi ne ce mu mayar da wannan dabarar fasaha zuwa Syria don ƙarfafa samar da abinci da kuma bunƙasa noma," in ji shi.

Yayin da ake sa ran kammala taron a ranar 21 ga watan Satumba, TEKNOFEST ya haɗa manyan gasanni 58 a cikin rukuni 137 wadanda suka haɗa da ɓangaren fasahar jiragen sama da mutum-mutumi da bunƙasa masana'antu da dai sauransu.

Kazalika taron ya haɗa tarurrukan karawa juna sani da na nishaɗantarwa.

A bara, baƙi kusan mutum miliyan 11 ne suka halarci taron.

Tun daga shekarar 2018 aka soma gudanar da taron kawo yanzu, taron baje-koli na TEKNOFEST ya zama wani dandali da matasa masu basirar ƙirƙire-ƙirƙire

ke zuwa baje-kolin ayyukansu, tun daga rokoki zuwa makamai masu linzami, tare da samun tallafi daga cibiyoyin gwamnati da abokai masu zaman kansu.