| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Kotu ta yi watsi da buƙatar Nnamdi Kanu ta a ɗauke shi daga gidan gyaran yari na Sokoto
Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ƙi amincewa da buƙatar Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB, ta a ɗauke shi daga gidan gyaran hali na Sokoto uzwa Abuja ko kuma Jihar Nasarawa mai maƙwabtaka.
Kotu ta yi watsi da buƙatar Nnamdi Kanu ta a ɗauke shi daga gidan gyaran yari na Sokoto
An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai / Reuters
8 Disamba 2025

Mai shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya ƙi amincewa da buƙatar Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar IPOB, ta a ɗauke shi daga gidan gyaran hali na Sokoto uzwa Abuja ko kuma Jihar Nasarawa mai maƙwabtaka.

Mista Kanu, ta hannun ƙungiyar lauyoyi da ke agazawa masu ƙaramin ƙarfi (Legal Aid Council), ya shigar da buƙata yana neman kotu ta umarci Gwamnatin Tarayya ko Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya (NCoS) da su gaggauta mayar da shi zuwa Kuje a Abuja ko cibiyar gyaran hali ta Keffi a Nasarawa.

Haka kuma, ya nemi a mayar da shi zuwa kowace cibiyar gyaran hali da ke ƙarƙashin hurumin kotun, irin su Suleja ko Keffi, domin ba shi damar bin ƙarar da ya shigar yadda ya kamata.

Sai dai Mai shari’a Omotosho ya yanke hukunci cewa dole a sanar da Gwamnatin Tarayya da Hukumar Gyaran Hali ta Nijeriya NCoS waɗanda su ne aka shigar ƙara kuma a basu damar su mayar da martani yadda ya dace a madadin adalci kafin a iya amincewa da buƙatar.

Daga nan sai ya saka ranar 27 ga Janairun 2026 domin sauraron wannan buƙata.

A wani hukunci da ya gabata ranar 20 ga Nuwamba, Mai shari’a Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai, inda ya same shi da laifin dukkan tuhumar ta’addanci guda bakwai da Gwamnatin Tarayya ta shigar a kansa.

Bayan yanke wa Mista Kanu hukunci, an mayar da Mista Kanu zuwa gidan gyaran hali da ke Sokoto sakamakon dalilai na tsaro a Kuje, inda aka sha samun ɓallewar gidan fursuna a can.

A halin da ake ciki, Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yi watsi da daukaka karar da Mista Kanu ya yi, tana mai cewa ƙarar ba ta da tushe.