Bankin Duniya ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da matsakaicin kashi 4.4 cikin 100 a kowace shekara har zuwa 2028, yayin da hauhawar farashi da talauci za su ragu idan gwamnati ta ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki tare da inganta ayyukan jama’a.
A cikin sabon rahotonsa na Nigeria Development Update, bankin ya ce sauye-sauyen da suka haɗa da cire tallafin man fetur da sauya tsarin musayar kuɗin waje sun ƙara yawan kuɗaɗen shiga da gwamnatocin jihohi ke samu.
Ya ce hakan ya samar da damar ƙara kashe kuɗaɗe wajen samar da ababen more rayuwa, ilimi da kiwon lafiya.
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a rabin farko na shekarar 2026, daga kashi 3.9 a shekarar 2025, sakamakon bunƙasar ɓangarorin ayyukan hidima da noma.
Ya kuma yi hasashen cewa hauhawar farashi za ta ragu zuwa kusan kashi 12 cikin 100 nan da shekarar 2028, daga kusan kashi 15 cikin 100 a halin yanzu.
Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin Nijeriya, Taiwo Oyedele, ya ce sauye-sauyen da gwamnati ta aiwatar sun taimaka wajen daidaita tattalin arzikin ƙasar tare da sanya shi a kan turbar samun ƙarin bunƙasa.
Oyedele ya ce tattalin arzikin Nijeriya na bunƙasa fiye da yawan jama’ar ƙasar, abin da ya ce zai taimaka wajen rage talauci idan aka ci gaba da wannan yanayi.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta fi mayar da hankali ne kan bunƙasar tattalin arziki da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta, musamman wadda za ta samar da ayyukan yi masu ɗorewa.
Bankin Duniya ya ce kuɗaɗen shiga na gwamnatocin jihohi sun ƙaru da kusan kashi 93 cikin 100 a zahiri tsakanin shekarar 2023 da 2025.
Sai dai bankin ya bukaci jihohin da su inganta yadda suke kashe kuɗaɗen gwamnati tare da ƙara zuba jari a fannin bunƙasa ƙwarewar al’umma, domin inganta rayuwar jama’a da rage talauci.






















